🔱BRILLIANT WRITTES ASSO....🖊
Na
*FAUZIYYAH TASI'U* *UMAR*
®FAUZAHWattpad 👉 realfauzah
**SHORT and TRUE* *LIFE STORY*
👌🏻🅿 *1*
*BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM*
Wannan shafi nakune yan uwana haziqan marubuta na BRILLIANT WRIT ASSO... jarumai kuma jajurtattun marubuta qara daukaka qungiyarmu me albarka ya kuma qara hade kanmu amin summa amin .
Wannan labari ba qagagge bane lbr ne daya faru a gaske da fatan zaku dakacemu sannu a hankali damin jin darasin dake cikin wannan gajeran labari muna tare daku masoyan littattafan mu na BRILLIANT kuma munayinku irin sosai dinnan😂😂
Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita a hankali taji an rungumota ta baya ta dago a nutse ganin yarinyar tata da bata shige shekara hudu ba a duniya ta janyota ta qara matseta a qirjinta cikin wata raunanniyar murya me ban tausayi ta fara mgn da sassanyar muryarta tace.
"Kuyi hqr Khadijah haka Allah yaso damu babu yanda zamuyi komai da ya faru nufinsa ne..." Shigowar dayan yaron da bazai shige shekara biyuba yasata qara fashewa da kuka cikin alamun fitar hayyaci ta kamo hanunsa shima tafara mgn kamar haka.
"Wayyoh Allah meyasa kayimin haka meyasa qaddarata tazo a haka meyasa ka kashe mijina baka kasheni ba meyasa ka mayar dani bazawara abinda nafi tsana meyasa baka dauki yarannan kabarmi mijina ba....."
Da sauri ta rufe mata baki itama cikin kuka tace meye haka Fauzah meyasa hankalinki zai gushe meyasa jarabtar rayuwa zata saki rasa imaninki haba Fauzah kin manta cewa komai kikaga yasamu bawa da sanin ubangiji don Allah karki bani kunya Fauzah pls...."😭😭😭😭.
Dagowa tayi da kanta da yake wani mugun ciwo tace" yanzu Amina shikenan su Hairan sunzama marayu yanzu shikenan narasa mijina me sona Muhammad shikenan bazan sake ganinsa ba..."
Sake rufe mata baki tayi tace kiyi hqr Fauzah Allan daya karbeshi yafiki sonsa kiyata yimasa addu'a kuma kidaina surutunnan kirinqa ambaton Innanillahi wa inna ilaihirraji'un itace kawai zatayi miki maganin matsalarki amma ba wannan surutun ba"
Innnanillahin take ta ambato amma har yanzu hawayenta yaqi tsayawa addu'a takiyiwa Mijin nata sosai wanda takijin cewa bazata qara samun miji kamarsa ba motsin shigowar mazanne yasata saurin miqewa yayyenta da wadanda suke dakin sune sukayi saurin riqe ta saida suka kaisa dakinsa sannan aka saketa aikuwa da gudu ta fita ta nufi dakin yaranma suka biyota zubewa tayi a gaban gawar tare da bude fuskarsa ta shafa sajensa tare da toshe bakinta amma ina takasa hadiye kukan.
Kwantar da kanta tayi a qirjinsa tana wani irin kuka me ban tausayi tare da jero addu'o'i na nema masa gafara da rahamar ubangiji yaran ma da basusan meke faruwa ba ganin mahaifiyarsu tana kuka ga babansu a kwance sukayi kanta suka kwantar da kansu a jikinta suma suna kuka gaba daya mutanen dake wajen zuciyarsu ta karye saboda dole komai dauriyarka saika zubarwa da wannan ahali hawaye Dr Jameel wanda take aboki na kusa ga marigayi Muhammad shine yasa hanu ya dauke Muhammad qarami wanda suke kira da Affan yayinda matarsa Amina ta dauke Khadijah wadda suke kira da Hairan.
Da qyar aka janyeta daga kan gawar Mijin nata saboda shiryashin da zaayi akaisa gdansa na gaskiya koda aka shiryasan da aka kirata tayi masa addu'a aka dagashi zaa fita dashi riqe makarar tayi tana wani irin kuka da dole kaima ka tayata kokawa yanke jiki tayi ta fadi sumammiya da haka aka fice dashi zuwa gidansa na gaskiya da fatan Allah ya jiqansa ya kyautata namu qarshen.
Bata farfadoba sai bayan kwana biyu saboda allurar da akayi mata me qarfi kasancewar yanayin da take ciki idan baayi mata hakanba qwalwarta zata Iya samun matsala.
Farkawa tayi da hailala da salatin annabi a bakinta ta dade a haka kafin komai yafara dawowa cikin kwanyarta sosai hawaye ya shiga zarya a kuncinta hakan ya ankarar da mutanen dake dakin cewa ta farka.
Mahaifiyarta ce ta fara zuwa kanta ta dagota jikinta ta shafa kanta tace
"sannu Fauziyya kiyi hqr komai kikaga ya same ki a rayuwa dama can Allah ya tsaro miki hakan ki rungumi qaddararki insha Allahu zakiji dadi kuma zakiyi dariya a gaba Fauzah nasan kinason Muhammad amma yazamuyi haka Allah ya qaddaro muku bazakuyi doguwar rayuwa ba shi Allah yafi kowa sanin dalilin dayasa yayi hakan fatana dai a kowanne hali kuma a kowanne yanayi karki manta dayi masa addu'a saboda ita ce kadai soyayyar da tayi saura da zaki nuna masa..."
Shiru tayi saboda kukan dayake Neman kwace mata wanda batason yinsa saboda zai zamo kamar tunzura yartata zatayi.
Bude qofar akayi aka shigo tare da sallama sai yanzu ta bude idonta ta saukeshi cikin na Aminan murmushi tayi mata dayake nuni da qarfafa gwiwa ta qaraso ta riqe hanunta tace sannu sister Allah ya baki lfy rufe idonta tayi ta bude lkcn da Dr Jameel suke shigowa da likitan hanunsa riqe da Hairan da Affan ya zauna a kujerar dake gefe suka gaisa da Ummah tare da tambayar ta "ya me jikin?"ta amsa da cewa " da sauki Jameelu mun gode sosai da dawainiya Allah yabar zuminci yasa ya dore tsakaninka da marigayi har a gdan aljannan"
Ya amsa da amin juyawa yayi ya dubeta yace "Mrs Moh ya jikin?" A sanyaye ta amsa masa dakin yayi shiru na wani lkc kafin yaran su katse shirun inda Hairan ta matso jikin Maman tata ta dafata tace "momy na tambayi Uncle ina dady na yace yayi tafiya zuwa aljanna bazai dawoba saimun girma kuma wai dadyna ya barmasa amanarmu dan haka daga yau shine dadynmu nida junior Affan wai hakane momy "
Kukan dataketa qoqarin tarewa shine ya qwace mata ta dago a hankali ta kalleshi shima ita din yake kallo da idanunsa da suka kada dukayi jawur ya fahimci me kallon nata yake nufi tana Neman izininsa ne wajan bama yarinyar amsa saboda haka ya kada mata kai alamar tace mata eh don haka ta janyota tace
"hakane Khadijah shine dadynku daga yau kinji?" gyada kai yarinyar tayi alamun gamsuwa tace "to momy meyasa kike kuka haka jiyama naga uncle yana kuka kudaina kuka kanku zaiyi ciwo kuma kinsan dadyna bayason kukanmu dukkan mu ko tam tunda kinayi babu ruwana nidai kuma zan fada masa"
Miqewa wayi ya fice dauke da Affan din inda sukuma suka shiga hada kayansu domin barin asibitin kai tsaye gdanta suka nufa gdan taya zame mata baqi a yanzu hasken dake cikinsa gaba daya ya gushe babu komai a cikinsa sai tarin duhu da qunci haka suka shiga kasancewar gdan a cike yake da dangi yar karbar gaisuwa.
Dakinta ta shiga ta fada saman gadon ta kwanta kukanta yasake dawowa sabo saboda gaba daya rayuwarta da mijinta ce take dawo mata sabuwa sosai suka rinqa rarrashinta tare da bata labarai kwatan kwacin irin wanda take ciki a yanzu hardai tadan saki jiki ta rage damuwa amma fah har yanzu bata iyacin komai sai tea shima sai bisa takurawar Amina .
Haka suka rinqa shidewa gashi har yau anyi addu'ar bakwai inda iyayenta suka shirya tafiya da ita gda kodan saboda rage mata damuwa komai da Aminan akayi sukayi sallama da maqota tana kuka suna kuka haka suka rabu kasancewar Fauzah mace ce meson mutane ba ruwanta da talaka dame kudi kowa natane shiyasa barinta unguwar yayima kowa ciwo to amma babu yanda zasuyi haka Allah ya tsara.
Daki guda aka ware mata a gdan Nash aka gyara mata duk da kasancewar iyayenta bawasu masu dukiya bane amma sunada zuciya da kuma rufin asiri saida daddare Dr yazo daukan Amina sukayi sallam ta fita bata jima ba ta dawo hanunta dauke da ledoji guda uku da kudi ta ajiye ledojin ta miqa mata tace gashi yace akawowa yaransa sannan wannan ki riqe a hanunki saboda koda zaki buqaci wani abu qin karbar kudin tayi takuwa ta ajiye mata ta fice dolenta ta dauka tace "to na gods sister kiyi masa gdy Allah ya qara budi "
Ta fita ta koma ta kwanta da tunani barkatai a zuciyarta sai wajan goma na dare ta bude taga naman kajine da youghut da tarkacan sweet da chocolate na yara dayan ledar kuma sabulai ne da omo manya da turaruka murmushi tayi tace .
"Uhmn Dr kenan kome zai hada tunkiya da breaxia dazai siyo min turaruka nida ko sabulu me qamshi bana wanka dashi"
UMMU HAIRAN CE...