*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA KO* *KISHIYA* 👭
⏩3⃣
WRITTING
AND
STORY
*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Miqewa yayi a kasalance yace “munga amarya Moha Allah ya sanya alkhairi yasa mu dawo barka”murmushi yayi yace “amin ya Allah muna gdy da ziyararka yallabai”
Murmushi yayi kawai ya zura hanunsa a aljihu ya zaro rafas ta dari bibbiyu ya ajiye a saman fridge yace“ gashi a baiwa amarya ”
Gdy yayi masa suka fita ya rakasu suka hau mota suka tafi wannan karon shida Farciwely ne a motar shi kuma marcavely da Journalist tunda suka taho ya daga kansa sama yana kallon saman motar zuciyarsa na kaikawo tsakanin qirjinsa da gdan prof Moha saurin zabura yayi yana karanto addu'o'in tsari daga sharrin shaidan da zuciya da suke neman jefasa cikin bala'i.
A haka suka qarasa inda ya ajiye motarsa ya dauka ya nufi gda inda ya tarar da matarsa Amina da basu shige shekara uku da aure ba tayi kwalliya tana jiran dawowarsa murmushi ya sakar mata wanda iyakar bakinsa ya tsaya saboda a zahirance batayi masa kyau ba bata burgesa kamar yanda Fauzan Moha ta burgesa ba.
Ko da dare yayi haka zuciyarsa ta rinqa zafi da kaisa inda bai kamata yajeba wani irin so da qaunar matar abokinsa na neman hanasa bacci karo na farko a rayuwarsa da soyayyar wata ya mace ta hanasa runtsawa kuma soyayyar ma ta matar aure matar abokinsa tashi yayi ya shiga zagaya dakin zuciyarsa cinkushe da tunani kala-kala tare da addu'ar neman sauqi gurin me duka,
Shi da kansa yake tambayar kansa wannan wacce irin jarabta ce wanne irin abin kunya zuciyarsa take shirin sashi yayi mayasa zuciyarsa zataso matar amininsa. Ganin tana shirin tashi yasashi saurin shigewa toilet ya dauro alwala ya tayar da sallah tare da fadawa Allah damuwarsa da nufin ya kawo masa mafita.
Tun daga wannan rana ya kamu da matsananciyar qaunar matar Amininsa har takai ya mayar da gdansu gdan zuwansa ko yaushe yakanje ko shi kadai ko shida abokansu ko kuma shida matarsa.
Hankali nutsuwa da tarbiyyarta yasa kullum farashin qaunarta yake hauhawa a zuciyarsa, a dalilin mazajensu aminta mai qarfi ta shiga tsakanin Fauzah da Amina wata hudu da auran Fauzah da Moha Allah ya azurtasu da samun ciki nanfa kulawa da tarairaya ta qaru sosai Moha yake kula da matarsa shikuwa Dr Jameel komai ya jagule masa son Fauzah kullum qaruwa yake azuciyarsa yayi yayi iyakar yinsa wajen yakice abin a ransa amma ya kasa haka dai yaci gaba da addu'a ta neman yayewar ubangiji amma ina kamarma qara masa akeyi takai ta kawo ko yaushe ya ganta sai yakejin wani matsanancin feeling dinta yana bijiro masa dole badan yaso ba ya fara janye jikinsa daga gdansu saboda gudun rinjayen zuciya da rudin shaidan.
Watan cikinta tara cikin ikon Allah akayi mata Cs aka ciro mata yarta mace akayi hidimar suna yarinya taci sunanta Khadijah shekararta daya da wata biyu tasami wani cikin shima Cs din akayi mata wannan karon namiji ne shikuma sunan mahaifinsa yaci wato Muhammad bayan tayi arba'in tadan fara samun qwarin jikinta Moha ya nema mata admission a B.U.K ta fara karatunta inda take karantar Islamic studies.
Tun daga lkcn yasami dama yakan hau adaidaita sahu yake makarantar ya tsaya a bayan inda Moha yake parking don kawai ya ganta idan kuwa yaga dan sahu ya kawota wani irin kishinta yakeji sai yaji kamar ya sai mota ya bata amma bashi da damar hakan, dabara ce ta so masa inda qarshen shekarar 2015 ya sayi sababbin motoci yan yayi qirar focus guda biyu fara da maroon ya bawa Moha maroon din yace gift dinsa ne na birthday kasancewar ranar ashirin da uku ga watan December ne birthday dinsa shikuma yabawa Amina farar ganin hakan yasa shima Moha yabawa Fauzah maroon din.
![](https://img.wattpad.com/cover/166989233-288-k765844.jpg)