https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*
*🅱RILLIANT* *WRITERS* *ASSO* 🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭
⏩1⃣2⃣
WRITTEN
AND
STORY*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**Wattpad* 👉🏻realfauzah
*TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Dagowa yayi ya dubi Dr Jameel da yalwataccen murmushi a fuskarsa yace “congratulation my friend wlh ni dama nasan da akwai abinda Allah ya boye tsakaninku tabbas gsky ta fara halinta yau gashi Fauzah dauke da cikinka a jikinta shakka babu Fauzah ciki ne da ita tsayin wata guda da sati daya ”
Tsananin mamakin abinda Dr Mercavely yake fada masa ya hanashi motsawa farin cikinsa ya kasa boyuwa zubewa yayi a qasa yayi doguwar sujjadar gdy ga mahaliccinsa daya azurtashi da samun qaruwa a lkcn da baiyi zato ba kuma bai tsammata ba.
Mercavely ne ya dagoshi ga mamakin sa hawaye ya gani a fuskar abokin nasa, tissue din dake hanunsa yasa yana goge masa yana girgiza masa kai tare da tambayarsa dalilin hawayen nasa dagowa yayi ya dubi abokin nasa yace
“Dole nayi kuka Dr Usman na rasa da bakin dazan godewa Allah narasa irin godiyar da zanyi masa ashe dama Dr zanga dan kaina ashe dama inada rabon haihuwa a duniya ashe rabon Fauzah zata haifa min yayane ya kashemin amini na lallai Allah buwayi ne gagara misali...”
Ya qarasa mgnr muryarsa na rawa cikin alamun tausayawa Mercavelly ya kada kai yace “shi Allah babu yanda bai iyaba kuma komai kaga yayi ikonsa ne Dr babu abinda zan fada maka game da matsalolin masu ciki saboda haka sai a kula sosai wajen ganin tanacin abinci sosai saboda na fahimci kamar bayan matsalar laulayin dake damunta akwai rashin cin abinci wanda hakan zai iya shafar abinda ke cikinta”
Gyada kai yayi yace “insha Allahu zan kula sosai Friend” miqewa yayi ya rataya jakar tarkacansa yayi murmushi yace “abinka da farin shiga so wlh kake dagawa yar mutane qafa nasanka da jaraba akan Fauzah kamar bunsuru haka kake.."duka yakai masa suna dariya dukansu yace
“ aikuwa kaga baa haifamin ragon da ba domin bincike ya nuna yaran da iyayensu suke yawaita kusantar junansu lkcn rainon cikinsu sunfi kuzari da lfy fiye da wadanda basa heaving sex sosai” gyada kai yayi yace“ hakane amma adai kula kar aje garin neman qiba a samo rama”
Ajiyar numfashi yayi yace “to Dr insha Allahu zan qoqarta kasan ita jarabar halitta ce ” rakashi yayi yaja motarsa sukayi sallama ya tafi
Shikuma ya nufi apartment din Amina tana zaune a parlour tana kallo ya zauna dubansa tayi a nutse tana nazarin farin cikin data gani shinfide a fuskarsa kafin tayi mgn ya katseta da janyota jikinsa yace “I'm very happy wifey ki tayani farin ciki munkusa samun qaruwa a gdan nan pure heart cikina ke gareta ohhh god bless you ya rabbih”.
Duk da sanyi da jikinta yayi amma be hanata nuna farin cikinta ba domin tasan cewa tsarin ubangiji ne hakan tasan cewa shine ya shiryawa rayuwarsu hakan, a fili tace “alhamdulillah ranar da muka dade muna jira takusa zuwar mana gdannan muma munkusa samun namu na kanmu gsky nayi farin ciki Allah ya amfanashi ya kuma qara musu lfy”