👭👭 AMINIYA KO KISHIYA👭👭

1.2K 42 3
                                    

🔱BRILLIANT WRITTERS ASSO...🖊

Na FAUZIYYA TASI'U UMAR
®FAUZAH

Wattpad👉realfauzah

SHORT and TRUE LIFE STORY

🅿 -2

Komawa tayi ta kwanta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da suya

Sunayen Allah kawai take ambato da haka bacci ya dauketa cike da mafarkan mijinta abin alfaharinta uban yayanta.

Washe gari qarfe bakwai da rabi Dr yazo gidan mahaifinta yasamu sukayi magana akan harkar karatun yarinyar Khadijah babu wani bata lkc ya nemi makaranta me kyau yakaita kasancewar dama can kafi barowarsu gidansu tana zuwa skull din.

Kwanci tashi babu wuya a wajen me duka yau har kwanaki arba'in da mutuwar Muhammad Mijin Fauzah  akayi masa addu'a tare da sadaqar arba'in kamar yanda akeyi a al'adance ,

Lokacin yayi daidai da lkcn da suka koma hutunsu na makaranta kasancewar dama tana karatun degree dinta a B.U.K  batare da wani bata lkc ba ta koma makaranta karatunta ya kankama sosai. Shigarta cikin mutanen yana rage mata damuwa da tunanin rayuwar data tsinci kanta a ciki

Sosai karatunsu ya kankama inda kullum kwanakin takabanta suke qara raguwa hankalinta yadan kwanta da zaman gdan nasu domin komai sunayi mata daidai qarfinsu yayinda dawainiyar yaran kacokan Dr Jameel ya dauketa har mada wani bangare na nata buqatun ita kanta Amina tana ziyararsu sosai aminci da shaquwarsu yake  qara gaba koda yake dama can aminan juna ne .

Ranar wata juma'a ta kama ranar da Muhammad ya cika wata hudu da kwanaki goma da rasuwa wanda ranar ta zamana ranar da Fauzah take fita daga takabarta basuyi wata bidi'a ba kamar yanda wasu sukeyi Amina dinki kala biyar tayi mata da takalmi da jaka da mayafi dunkunan duka babu qanana ta kashe kudi lkcn data kawo mata har kuka tayi tanayi mata gdy saboda haqiqanin gaskiya Amina ta cika masoyiya ta gaske.

Rayuwa taci gaba da tafiya cike da sauye-sauye masu dadi da akasin haka yanzu har shekara guda kenan da rasuwar Mijin Fauzah babu abinda ta fasa na kwalliya da gayunta kasancewar wannan dama dabi'ar ta ce kyakkyawa ce sosai duk da kasancewar kallo daya bazaka iya gane hakanba, tanada qira da structure me kyau Fauzah ba fara bace chocolate color ce wadda fatarta take oily skin buri kuma alfaharin kowanne namiji matsakaiciya ce ta fanni tsaho domin ba doguwa bace kuma ba gajeriya bace tanada dara-daran idanu masu haske kuma shanyayyu wanda gashin idonta yake zara-zara girarta a tsare take kamar anzana ta hancinta dogone sosai bakinta dan qarami da shiryayyun haqora wanda takeda wushirya me fadi da kyau tana daya daga cikin abinda yake qara fito da sirrin kyanta tanada hips sosai da cikar qirji wanda koda kasancewar ta haihu ta shayar da yaranta amma idan baka saniba bazaka taba ganewa ba saboda a cike yake tam kuma a tsaye kamar na budurwa.

Daga wanka ta fito tana shafa mai a tattausar fatarta me kyau da santsi akayi sallama a tsakar gidan ta amsa tare da cewa “kai dan halak yaqi ambato yanzu shiryawa nakeyi zan taho gdan naki kuma sai gaki”murmushi tayi tace “bari kedai sister wlh zaman gdanne ya isheni nace da Dr ya kawo ni muyi hira ko na samu sauqin zugin zuciyata”

qarasa shafa powder tayi ta zura doguwar rigarta baqa wadda ta fito da ainihin surarta ta juyo ta dubeta ta rame sosai tayi baqi kasancewarta fara tayi ajiyar zuciya ta zauna tace “Amina kinqi cirewa ranki damuwa kinqi barin zuciyarki ta huta Sister shifa Allah baayi masa dole abinda yaga dama shi zaiyi kuma ita haihuwa lkc ne idan lkc yayi zaki haifa don Allah kiyi Colling mind dinki ”

Murmushi tayi tace “ bazaki ganeba Fauzah muje ku gaisa da Dr din yace sauri yakeyi ” “af wlh na manta tare kuke fah muje ”

Suka juya suka fita bayan tayi rolling da mayafin doguwar rigar  a qofar gdan suka sameshi yana jingine a jikin motarsa sanye yake da qananan kaya blue jeens da jar shirt da suka karbi kyakkyawar fatarsa data gaji da hutu tazama kamar glass saboda sheqi da haske gent's handsome guys kenan da shekarunsa bazasu haura 35 ba sosai Jameel dan hutune saboda hutun har fitowa yayi a jikinsa ga tarin dukiya da Allah yayi masa amma abu daya da yake damunsu shine rashin haihuwa.

Tunda suka fito ya kafeta da shanyayyun idanunsa yanajin abinda ya dade yanaji game da ita yanayi masa yawo a jikinsa.

Dagowa yayi da sauri yana qoqarin saita nutsuwarsa tare da sauke ajiyar zuciya yace “ranki ya dade ya karatu ya zawarawanki don nasan yanzu sunanan buhu 2 ” murmushi tayi tace “habadai Dr saikace wata me jiran kadan aini bana kula kowa duk ma wanda yazo gurina cemasa nakeyi ni ba aure zanyi yanzu ba ” wata qaqqarfar ajiyar zuciya ya sauke wadda tasa dukkansu suka dago suka dubeshi karaf idonta ya fada cikin nasa tayi saurin yin qasa da kanta ,
                  Waskewa yayi yace“ kai amma fah bakya kyautawa wlh to meyene amfanin zaman Fauzah ai kawai ki fitar mana da miji musha biki mu miqaki gdanki kawai shine kwanciyar hankalinmu baki daya ”
Ajiyar numfashi tayi tace“ to Allah dai yayi mana zabi na alkhairi kawai yanzun ma akwai wani lecturen mu da yake ta yimin nacin na bashi dama yazo gdanmu amma naqi”

Kicin 2 yayi da fuska ya zaro kudi a aljihunsa da wani kwalin chocolate ya miqa mata yace “gashi a bama yarana ni zan tafi ”.

Qin karbar kudin tayi da farko amma ganin yanda ya bata fuska yasa tasa hanu ta karba ta juya tayi masa sallama ta koma gda.

Saida suka gama sannan Aminan ta shigo nan suka shantake sunata hira kasancewar ita din ba ma'abociyar yawan mgn bace yasa saidai tayi murmushi wanda zataba da amsarma a gajarce take bayarwa sai dare sosai yazo daukan Amina da kansa ya miqa mata leda yace“ ga turaruka kema kake fesawa zawarawanki” tsuke fuska tayi tace “Allah Dr ka bari banaso nifa natsani Kalmar nan ko a wani ba niba wlh ” yanda tayi mgnr tayi bala'in burgeshi yace “to kiyi hqr zaa kiyaye insha Allah ” murmushi tayi ta juya tare dayi masa gdy  sukayi sallama da Amina tare da yimata alqawarin itama zatazo nan kusa gdan nata .

Tana shiga dakin nata ta zazzage ledar cike da zaquwa saboda Allah yayita ma'abociyar son turare amma abin mamaki kwalin wata tsaleliyar waya ne ya fado daga cikin ledar sannan turarukan guda uku masu kyau da tsada sai set din man shafawa da powder zubawa kayan ido tayi cike da fargaba haka kawai gabanta yake faduwa  tsam ta miqe ta fita tsakar gdan ta fadawa ummah abinda yake faruwa duban kayan ummah tayi tace “toh ikon  Allah Fauzah cemasa kikayi bakida waya?” kada kai tayi tace “wlh aa ummah ” shiru umman tayi tare da girgiza kai can tace “to  Allah ya saka masa da alkhairi amma kedai ki kula da kanki don Allah kada wani abu na tur ya fito daga gareki Fauzah Amina mutum ce Ku riqe amanar junanku ”

Gyada kai tayi da sanyi jiki tace “insha Allahu ummah ”

UMMUH HAIRAN CE...📝

True Life StoryWhere stories live. Discover now