https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*
*🅱RILLIANT* *WRITERS* *ASSO* 🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭
⏩1⃣4⃣
WRITTEN
AND
STORY*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**Wattpad* 👉🏻realfauzah
*TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Janyota yayi zai rungumeta saboda a yanzu babu abinda yake buqata sama da yajishi a jikinta janyewa tayi da sauri ta miqe tana girgiza masa kai shima tasowa yayi ya qaraso gabanta sake matsawa tayi ta zube a qasa da sauri ya riqota cikin kidima ya daka mata tsawa yace “ meye haka kikeyi ne zaki je ki illata kanki kina shirmenki ”
Dagowa tayi ta dubeshi a qasqance tace “dole ne dama kace ina shirme mana Dr tunda buqatar ka ta biya ka samu abinda kakeso Dr me Amina zatayi maka a rayuwa da zakake qaurace mata me zatayi maka da bazaka iya fitowa ka fada mata ba domin ta qyara kai fa da bakinka kake fadamin matsalar matanka takace matsalarka ta matanka ce ashe kenan furucinka iyakar bakinka ya tsaya ashe son ranka ne kake fada meyasa Dr meyasa wlh bantaba zaton hakan daga gareka ba”
Rufe mata baki yayi da hanunsa yace “sheet up pls Fauzah me nayi ne wai me tace miki nayi mata?” ture hanunsa tayi tace “kana nufin bama kasan akanme nake mgn ba kazo ka takuramin ka qwarzabeni ka hanani hutawa ka mayar dani sex machine naka amma ga matarka can matar rufin asirinka tana buqatarka kana guje mata why Dr why” ajiyar numfashi yayi ya matseta a qirjinsa yana tura hancinsa cikin sumarta yace “shikenan baby Angel insha Allahu zaa gyara” janyewa tayi a jikinsa ta koma ta kwanta taja bargo ta rufe jikinta tace “ni don Allah ka tafi canma na yafe kwanan yau banaso" murmushi yayi ya hayo gadon shima ya shige cikin blanket din yace nikuma ban karba ba banason wannan kyautar yana qoqarin shigewa jikinta ta juya masa baya tace “Oh my god Dr wlh nifa na gaji bazan iya yi maka komai ba pls don Allah yau dai daya ka kyaleni na huta”
Hugging dinta yayi ta baya yana shafa cikinta zuwa qasan mararta hanunsa ta janye ya dora kansa a kafadarta yace “ karmu fara haka dake my Angel zaki azabtar dani in kikayimin haka pls” saqo ya shiga aika mata tana qunquni rufe mata baki yayi da nasa.
Washe gari da wuri ya fita kasancewar yanada aikin safe itama kwanciya tayi bata farka ba sai 11:30am sannan ta tashi ta nemi abinda zata ci ranar yini tayi tana baqi saboda haka bata samu wani cikakken time ba sai dare abinda yabata mamaki yinin ranar sur bataji duriyar Amina ba bayan tayi sallar la'asar ta shirya ta fita zuwa apartment din nata ga mamakin ta qofar a kulle take ta kwankwasa sosai amma shiru juyawa tayi cike da mamaki ta koma sashinta ta shiga kitchen.
Youghut ta dauko da chinchin ta zauna taci ta kwanta tana kallo qarfe shidda daidai taji tsayuwar motarsa ya shigo tana zaune tayi masa sannu da zuwa babu wata walwala a fuskarsa ya amsa tare da tambayarta lfyrta amsa masa tayi ya wucce dakinsa yadan dauki lkc sannan ya kirata miqewa tayi ta shiga yana tsaye ya dubeta tare da kashe mata ido yace wanka nakeson kiyimin zama tayi tace “kayi hqr kayiwa kanka Allah na gaji yau baqi na yini inayi aunty Hadiza ma tace tana gaisheka ” “Okay yayi kyau shine baki kirani nazo mun gaisa ba ko?” ajiyar zuciya tayi tace “yi wankanka tukunna” wankan ya shiga ba jimawa ya fito da kanta ta shafa masa mai sannan ya saka kayansa janyota yayi yace “my Angel mijinki yana jin yunwa fah ” dagowa tayi tana kallonsa tace “ nasan yanzu matarka ta gama maka girki muje na rakaka” tsuke fuskarsa yayi yace “Okay matata ko to kekuma mece ce tawa?”