👭AMINIYA KO KISHIYA👭

872 37 3
                                    

https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*

*🅱RILLIANT* *WRITERS* *ASSO* 🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭


⏩8⃣


WRITTEN
           AND
             STORY

*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH*

*TRUE LIFE STORY*

*SHORT STORY*


Mikewa tayi tana murmushi ta shige dakin da aka bata a matsayin masaukinta wanka tayi sannan ta gabatar da sallar isha da shafa'i da wuturi ta kwanta tare da bude data ta fara chart da qawayenta sai goma sannan ta kwanta.

Rayuwa mai dadi takeyi a Adamawa bata da damuwar komai sai ta yaranta data barosu a Kano saboda mkrnta amma suna ranta kuma kullum sai sunyi waya da Ummah da Baba Amina ma sunyi waya da ita sau biyu shidinma Aminan ce ta kirata saboda ita yanzu dukkansu haushinsu takeji.

Yauma kamar kullum suna parlour ita da aunty Rafi'ah suna hira Baffah Mukhtar ne ya shigo fuskarsa dauke da fara'ah Aunty Rafi'ah ya kira suka shiga daki itama mikewa tayi ta shiqe nata dakin agogo ta duba 4:37pm, guda taji aunty Rafi'ah ta saki a parlour gabanta ne yayi wata muguwar faduwa daidai lkcn da ta turo dakin ta shigo.

Bayanta Amina ce  zuba masu ido tayi cike da mamaki aunty ce ta nunawa Amina gurin zama ta zauna itama zama tayi tana kallon Aminan, kawar da shirun Amina tayi tace “wannan kalloh haka Fauzah kamar na canza miki ”

Ajiyar zuciya tayi tace “mamaki ne yake neman sheqeni Amina ya akayi kika zaqulo gdannan?” murmushi tayi tace “ba wannan zaki tambayeni ba tambaya ta zakiyi meye yake tafe dani yanzu tunda kin baro Kano saboda mun dameki mun hanaki zaman Kano to kiyi hqr yanzu mun biyoki ne domin mu daukeki mu tafi dake”

Dubanta tayi tace“ku tafi dani kuma ke da wa zaku tafi dani?” kafin amina takai ga bata amsa aunty ta shigo tace “Fauzah kizo inji baffanki yana parlourn sa ” miqewa tayi gabanta na ci gaba da faduwa ta zari hijjab dinta ta saka ta fita.

Shiga tayi bakinta dauke da sallama idonta cikin nasa yana zabga mata wani qawatacce murmushi saurin dauke kanta tayi tare da zama nesa dashi kadan ta sunkuyar da kanta tace “Baffah gani aunty tace kanason ganina"

Gyaran murya yayi yace “fauzah bakiga baqonki bane?” sake qasa tayi da kanta tace “naganshi ina yini” a nutse ya amsa mata tare da tambayarta lfyrta, a gajarce ta bashi amsa shiru ta dan ratsa kafin baffah ya kawar da shirun da cewa “alhamdulillahi Fauziyya ga Dr Jameel yazo tafiya dake wanda yake a matsayin mijinki a yanzu saboda Allah cikin ikonsa sati guda daya gabata aka daura aurenki dashi bisa sahalewar mahaifinki....”

Zabura tayi ta miqe jikinta na wata irin rawa mgn take sonyi amma takasa saboda tsabar dukan da zancen na Baffah Mukhtar yayi mata jin yanda bakinta ya harde yasata saurin zubewa a qasa ta dora hanunta a kanta ta saki kuka me sauti wanda ya janyo hankalin Amina da aunty Rafi'ah suka nufo dakin da sauri.

Tarar da ita sukayi ta hada kai da gwiwa jikinta yana wani irin tsima da gudu aunty ta qaraso ta riqo ta tureta tayi tace “ki qyaleni aunty qyaleni na mutu aunty na shiga uku meyasa rayuwata banida sa'a meyasa komai yake zuwa min a baibai meyasa Baba zaiyimin haka meyasa zai auraddani ga Jameel na shiga ukuna mutuwata kizo Allah dama kasheni kayi da ganin wannan baqar ranar ni Fauzah na auri mijin aminiyata Innanillahi wa innah ilaihirraji'un.....” ta qarashe mgnr muryarta na shaking.

True Life StoryWhere stories live. Discover now