https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭
⏩7⃣
WRITTEN
AND
STORY*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Cikin matsanancin tashin hankali Fauzah ta dubi Amina tace “me kikeson kicemin Amina me kikeson fadamin kina nufin rashin kunyar Dr har takai ya kalle yace miki yana sona? Shine kekuma kika dauko jiki kikazo ki titsiyeni akan saina aureshi?
Hmn to wlh tun lkc be qure muku ba gara Ku nemi wadda zaku rainawa hankali amma badai niba me zanyi da Dr me yake dashi da zai bani wlh Amina bana sonsa bakuma zan aureshi ba na tsanesh....”
Bakinta ta rufe mata tana girgiza mata kai tace “qarya kike Fauzah kinason Dr kuma zaki aureshi wlh Fauzah sai kin auri Dr saboda ke yakeso yana sonki kuma zai rayu da ke saboda kece burinsa ki rubuta ki ajiye Dr mijinki ne...”
Dakatar da ita Ummah tayi tace “haba Amina wannan wacce irin mgn ce kema kinsan abune da bazai taba yuwuwa ba do Allah kubar mgnr nan karma ta fita waje kuja mana zagin jama'ar duniya” “Ummah zai yuwu tunda yana sonta kuma itama tana sonsa Ummah nasani ni kuke kalloh kuma ni na lamuncewa Fauzah tazo mu zauna tare nasani tunda Dr yayi niyar aure ko bai auri Fauzah ba zai auri wata tunda kuwa har nasan da hakan mezai sa naqi bashi dama ya auri zabin ransa wlh ummah bana baqin ciki indai Fauzah ce a matsayin kishiyata tasan komai nawa tasan matsalata nasan komai nata nasan matsalarta zamu fahimci juna kuma zamu zauna lfy Ummah don girman Allah karkuce aa addu'arku kawai muke buqata”
Jinjina kai Ummah tayi tana qara jinjina al'amarin abin da kamar yuwa amma dai baa tara sani da Allah shigowar baba ce ta sasu dagowa suka zuba masa ido bayansa Dr Jameel ne sai macarvely dake biye dashi shima.
Daya bayan daya take kallonsu kafin ta sauke rinannun idanunta a cikin nasa ya rame sosai yayi baqi amma har yanzu kwarjininsa yananan, wata muguwar harara ta zabga masa dake alamtar da irin haushinsa din da takeji.
Dauke idonsa yayi saboda bazai iya jure kallon qasqancin da take jifansa dashi ba gashi qiri-qiri yake hango qiyayyarsa a cikin qwayar idonta, suna gama shigowa baba ya kirata cikin sanyin jiki ta shiga parlourn inda suke zaune ta tsuguna gabansa tace “gani baba”
Gyaran murya yayi ya kira Ummah da Aminan suma suka shigo suka zauna sake gyara zamansa yayi yace.
“Fauzahtuljannah wannan zaman naki ne dan haka nakeso ki bani hankalinki aro ku saurareni Wannan bawan Allah Jamilu batun yau ba tun wata guda da suka wucce ya sameni da mgnr Neman izinin neman auranki, to a gsky a lkcn banyi naam da mgnrsa ba duba da yanda tsakaninki da matarsa yake nayi iyakar qoqarina na ganar dashi kuskuran dake cikin hakan da kuma abinda hakan zai janyo amma yakasa ganewa.
To yau ina zaune a kasuwa suka je suka sameni suka qara tasomin da mgnr gsky naso sake yi musu musu amma hujjojin da suka kawomin sune suka kashemin jiki har naji zuciyata ta kwanta da lamarin,duk da haka ban yanke hukunci ba saboda damar takice ba tawa ba Fauziyya kece kike da ikon zabawa kanki miji baniba saboda haka nakeson jin raayinki game da hakan”
Tunda Baba ya fara mgnr take hawaye har yakai aya shiru tayi tana ajiyar zuciya ba tare da tace komai ba, saida ya sakeyi mata mgn sannan ta dago kanta tace.
“Wlh Baba bana sonsa bakuma zan aureshi ba In har auren kukeso nayi ku bari zan kawo miji da kaina amma bazan taba auran Dr ba Baba na tsaneshi saboda halinsa bazan taba auren cin amana ba baba bazan aureshi ba bana sonsa pls”
Tana rufe bakinta Amina ta cafe da cewa “Wlh baba Fauzah tanason Dr taqi bari ta gane hakanne da kanta saboda wani qudiri nata na daban kuma bata da Mijin daya dace da ita kamar Dr saboda shine zai jibanci lamarinta don Allah Baba karku biye mata wlh banida matsala da Fauzah"
Miqewa tayi da sauri zata fice daga dakin saboda ta gaji da jin kalaman nasu ji takeyi kamar suna watsa mata tafasasshen ruwa a zuciyarta, tana fita ya biyo ta zata wucce ya riqo hanunta da qarfi ya fizgeta ya cillata motarsa ya ja a guje yabar unguwar kuka sosai takeyi saboda bata qaunar abinda zai hadata dashi ta tsaneshi fiye da mutuwarta parking yayi ta murda murfin zata fita ya riqota tare da kulle motar matsowa yayi kusa da ita sosai qamshinsa tare da hucinsa na bugarta yanayi mata tafiyar tsutsa a hanunta bude saukar wani abu taji me dumi a hanunta wanda yasata dagowa ta watsa idonta cikin nasa hawaye ta gani kwance akan fuskarsa sauri dauke kanta tayi saboda bata iya jure kallonsa.
Qara matse hanunta yayi yace “Fauzah meyasa baqya sona meyasa kike qina meyasa kikaqi fahimtar manufa ta meyasa kikaqi gane halin da nake ciki wlh Fauzah da inada ikon cire sonki a zuciyata da tun ba yanzu ba na dade da cirewa pls ki fahimceni banida niyyar cutar daku dukkanku abinda nakesonyi bai sabawa shari'a ba kuma ba kanmu aka faraba Fauzah meyasa Amina zata fahimceni ke kikasa fahimtata???”
Janye hanunta tayi daga nasa tace “ bazan taba fahimtarka ba Dr saboda bakazo da abinda zan fahimce kan ba banasonka Dr banason aurenka wlh da na aureka gara na mutu babu aure” saurin rintse idonsa yayi ya toshe kunnansa tare da bude mata qofa ta fice da sauri har tana tuntube.
Venue dinsu na exam ta nufah har an raba booklet anfara exam itama ta karba ta zauna bata iya tsinana abin arziqi ba saboda tarin tension din dake zuciyarta haka tayi something ta fita ganinsa tayi har lkcn yana tsaye da sauri ta juya ta samu wani dan sahu ta haye suka wucce ta gaban shi
Murmushin takaici yayi ya shiga motar yaja ya fita shima daga mkrntar.
Dama yau din itace exam dinsu ta qarshe dan haka tana zuwa gida ta hada kayanta a trolley saboda gaba daya Kano tayi mata zafi so take ta nisanta kanta daga garesu ko tasamu sauqi taji dadin hutun season din da suka tafi a daidai wannan lkcn.
Daga ummah har baba babu wanda ya qara taso mata da mgnr Dr hakan ba qaramin dadi yayi mata ba amma da taje kwanciya kasa bacci tayi saboda tunanin baqon al'amarin da ya shigo rayuwarta sama ta kai kwana biyu tsakani kuwa zakara ya bata Sa'a tabi motar Kano line zuwa jihar Adamawa gdan qanwar Ummanta dake zaune acan da mijinta wanda yake baffah a gurinta kasancewarsa qani a gurin babanta shima.
Sunyi farin cikin ziyarar bazata data kawo musu nan suka baje a parlour da aunty Rafi'ah sunata hirar yaushe gamo cikin hirar me take basu lbrn abinda yasa tayo balaguro zuwa Adamawar sosai aunty ta jinjina lmrn dagowa tayi ta dubeta tace.
“Amma Fauzah ke bakya tunanin akwai wani abu da Allah ya boye tsakaninki da abokin mijinki kuma Mijin aminiyarki?” dagowa tayi tayi murmushi tace “kema dai aunty wlh da wata mgn kike ni babu abinda Allah ya boye tsakanina da Dr Jameel kawai tsagwaron cin amana ne kuma koma menene banaso bakuma zan aureshi ba”
Jinjina kai aunty Rafi'ah tayi tare da cewa to Allah ya zaba abinda yafi alkhairi amma ni na hango wani abu dake baki hangoshi ba duba da tun lkcn da ya fara sonki da qaunarki ke Fauzah kiyi addu'ar zabin alkhairi kawai amma irin wannan auren yin Allah ne bayin mutum ba”....
Pls Share
*UMMUH HAIRAN* *CE* ...✍🏻