.https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭
⏩4⃣
WRITTEN
AND
STORY*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Komawa yayi ya kwanta bayan yayima qofarsa key saboda a halin yanzu bayajin sha'awa ko buqatar ko wacce mace bayan Fauzah saida yayi addu'o'in neman tsari daga sharrin dare sannan yaja blanket ya rufe jikinsa kasancewar yanayin sanyi ne lkcn.
Washe gari yana tashi yayi wanka kasancewar asabar ce ya shirya cikin qananan kaya blue black din jeans da red shirt me dogon hannu ya taje sumarsa tare da gyara sajensa da dan gemun daya tsayar Wanda ya qara qawata kyakkyawar farar fuskarsa ta take alamtar da yanayin hutun da yake ciki.
Dr Jameel yana da kyau da kyan qira saboda irin mazan da wacce mace zatayi mafarki samu ce dogo ne me yana da jiki amma ba irin sosai dinnan ba kuma yana da faffadan qirji daidai buqatar ko wacce mace wanda yake shimfide da gashi luf-luf ba iya qirjinsa ba gaba daya jikinsa hannu da qafa duk gashi ne kwance gwanin sha'awa kai iya haduwa Dr Jameel ya hadu.
Abu daya yake damunsa yake cin zuciyarsa har wani lkcn yakan hanashi walwala ba komai bane face rashin haihuwarsu tsayin shekara tara kenan da auransa da Amina amma ko batan wata bata taba yiba bayan kuma yana aikinsa yanda ya kamata wannan abu yanacin zuciyarsa amma yakanyi qoqarin boyewa saboda gudun tayarwa da Aminan hankali domin yana ganin ya kamata ace tafishi damuwa duba da cewa shi namiji ne yana da damar qara auren wata matar bayan ita kuma idan yana da rabo zai samu amma yaga ita abin bai dameta ba.
Agogon hanunsa ya kallah 7:45am. Fauzah karatunta part time ne kuma lecture ta 8:30am ne ji yayi gabansa ya fadi tabbas kowa a faculty dinsu yasan mijinta ya rasu hakan yana nufin kowa zai iya kulata kenan? Da sauri ya girgiza kansa yace.
“Aa bazaima yuwu ba dole nadauki matakin dakatar da hakan” ya fada yana sakkowa daga step din benan dake parlourn inda bedroom dinsa yake oppstar din.
A parlour ya tarar da Aminan da Affan tana shirya break fast a dinning area ta bayanta ya zagaya ya rungumota yayi kissing wuyanta ya juya ya dauki Affan din ya shiga juyawa dashi a parlourn yanata dariya dire shi yayi ya kalleta yana zama akan kujerun da sukayiwa dinning din qawanya ya zauna yana jan cup ya hada tea ya sha ya miqe ya dauki key din motarsa da wayoyinsa ya juya zai fita katseshi tayi da cewa.
“Dr ina zakane kaketa sauri haka? yau fa asabar ce ” gabansa ne ya fadi yayi saurin aro nutsuwa yasawa kansa yace “am wani aikine ya tasomin urgent a hospital so shine zanje na dawo” yana kaiwa nan ya juya ya fita binsa tayi da addu'ar samun nasara.
Kai tsaye dagaUnguwar da yake yankaba unguwar Hotoro yayi cike da faduwar gaba amma haka yarinqa sawa kansa juriya saboda ya quduri niyyar mallakarta ko ta wanne hali saboda yanzu a duniya bashi da burin daya shige auran Fauzah burinsa mafarkin daya shekara biyar yanayi akanta ya tabbata, ya zaiji idan ya mallaketa wanne irin farin ciki zaiyi ranar da ya kwana tare da ita?
Tambayoyin da yakewa kansa kenan yana ta murmushi shi kadai kamar zautacce ,motar yayima matsuguni a wani fili dake gyefen gdansu kadan daidai lkcn da take fitowa daga gdan sanye da doguwar riga maroon tayi rolling din kanta da baqin mayafi jaka da takalminta da agogon dake daure a tsintsiyar hanunta duk baqaqene sai maroon din janbaki da tasaka ta yi kyau sosai abinka da kyakkyawar dama duk da ba fara bace ita wata kalar fata ce da ita wanda kallo daya bazaka gane ita din ba fara mace kasancewar sheqin fatarta yana daukan ido sosai anihin fata me kyau kenan wato oily skin.