https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭
⏩6⃣
WRITTEN
AND
STORY*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH**TRUE LIFE STORY*
*SHORT STORY*
Tana tashi da safe ta shirya a gurguje ta fita daga gdan dan sahu ta dauka ya kaita har mkrnta ta biyashi ta shiga cikin department dinsu lkcn babu kowa tunanin abinda ya faru jiyan ya tsaye mata a rai bata samu sauqinsa ba sai da sauran daluban suka hadu aka fara lecture.
12:30pm suka samu Interval ita da wata qawarta abokiyar karatunta suka tafi capteria suna hanya suna hira har suka qarasa inda sukayi order na abinda suke buqata.
matuqar mamakinta ya kasa boyuwa qamewa tayi a inda take cikin muguwar razana da kidima wanda hakan yayi sanadin sullubewar robar Mirinda din dake hanunta.
Ba wani abu ta gani ba illah Dr Jameel zaune ya dora qafa daya kan daya da kwalin lemon exectic a hanunsa ya kafeta da sihirtattun idanunsa .
Lumshe idanunsa yayi ya budesu a kanta lkcn da take qoqarin tashi ta gudu daga wajen da azama ya miqe ya cafko hanunta ta fada qirjinsa hanu yasa ya matseta sosai ta fara kiciniyar qwacewa amma yaqi bata dama sunkuyowa yayi da kansa daidai kunnanta yace.
“Zuwa nayi ki maimata min abinda kika fadamin jiya ya hanani bacci” qarfinta ta hade waje guda ta qwace tana haki juyawa tayi zata fita ya qara kamota wannan karon bata bari ya hada ta da qirjinsa ba qasa ta zame tayi zaman yan bori hanunta ta dora a kanta ta kwallah qara gabadaya hankalin mutanen dake cikin restaurant din ya dawo kansu.
Shima zama yayi ya tanqwashe qafafunsa tare da tallafe kansa da hannunsa daya dayan kuma yana cikin nata be damu da kallon da ake musu ba yace.
“Wallahil azeem Fauzah bazan bar gurinnan ba sai kin maimaita min abinda kika fadamin jiya da daddare. kin dauka nidin matsoraci ko kuma ragon namiji ne da wannan hargagin naki zai sa na janye qudiri na a kanki? Hmn Fauzah kenan bakisan waye Jameel ba to wlh inma kina tunanin hakan ki daina domin babu abinda zai hanani mallakarki Fauzah ban damu da ki soni ko ki qini ba inasonki kuma zan rayu dake a kowanne hali”
Miqewa yayi ya gyara kwalar rigarsa yace “bismillah Fauzah yanzu aka fara wasan amma inason tabbatar miki bana loosing a rayuwata tun farko rabon Hairan da Affan shine ya hanani saninki sai bayan kin kasance matar abokina sannan kika bayyana gareni qaddarar data kashe Moha ba wata bace face qaddarar aurena dake Fauzah idan zan rabu da kowa zan rasa komai dana mallaka indai ina numfashi bazan fasa auranki ba, ki rubuta ki ajiye Jameel mijinki ne ”
Juyawa yayi zai fita ta riqo hanunsa da sauri tana girgiza masa kai bude baki tayi tace “don Allah Dr kayi hqr wlh bana sonka bazan iya auranka ba Dr kar son zuciyarka yasa muyi abin kunya abinda duniya zata tsine mana wlh bazan iya aurenka ba ya zanyi da kunyar matarka ya zanyi da kunya Amina da wanne ido zan kalleta, pls na roqeka karka bari tasani Dr idan kai babu ruwa a idonka ni nawa akwai bazan iya wannan abin kunyar ba......” ta qarashe mgnr kukanta yana qara qarfi hanunsa ya dora a lips dinta yace.
“Ni ba abin kunya zanyi ba sunnah zan raya kece kika toshe tunaninki kika zubar da iliminki kike kallonsa a matsayin abin kunya” yana kaiwa nan ya fice da sauri ya shiga morarsa ya bar mkrntar da gudun tsiya.