Labarin Mairamah.
True life story.
Labarin gaske ne da ya faru akan wata baiwar Allah. Akwai tarin al'ajabi da van mamaki a tattare da labarin. Karfin ikon ubangiji yafi gaban misali.Akwai tsananin ban tausayi da rashin adalci aciki.
Na yarda zan rubuta wannan labarin ne dan naga akwai tarin darasi aciki. Ba dogon abu zan k'ara ba sai dai zan yiwa labarin kwalliya ta yadda alk'alamina zai ji dadin fito da ainahin abinda ake so a karanta.
Zan canja sunaye, jamhuriya da kuka muhalli. Kamar yadda labarin ya buk'ata.An gina labarin rayuwata cike da rud'ani da al'ajabi. Duk da kasancewar farkon ginin ya kasance nagartacce, cike da farin ciki da k'aunar ci gaba da numfasawa a doron k'asa, ban sani cewa ba, ita kaddara ba a goshi ake rubutata ba, ba tana duba ga nagarta ko kasantuwar mutum a kyakkyawan mazauni ne ba.
Na k'ara yarda da cewa abu biyu ne mutum yake sani a rayuwarsa.
Farkon rayuwarsa, watau haihuwarsa, sai kuma k'arshensa wanda ya kasance mutuwarsa.Ku biyoni dan kuji yadda tawa salon kaddarar mai ban mamaki take.
Sunana Maryam Malik sai dai tun ina k'ank'anuwa aka mayar da furucin Maryam izuwa Mairam, yanayin yadda k'anena Salim yake kira na kenan alokacin da gabb'an bakinsa basu sami cikakken 'yanci ba.
A lokacin da nake aji ukku na sakandare, rayuwata ta inganta ta yadda Abbana yake k'ok'arin ginata.
Ina cikin jin dad'i kasancewar ina gudanar da rayuwata kamar yadda adini ya shar'anta.
Burin Abbana nayi karatu na zama wata abar da za'ayi alfahari da ita, nima inada wannan burin sai dai shigowar Uncle Abakar a rayuwata ta karkata. Malamin makarantarmu ne tun ina aji d'aya na sakandare yake k'aunata sai dai dokar makaranta bata halatta masa ni ba har sai da na shiga aji shidda.
Sai muka gina soyayya mai k'arfi a tsakaninmu tare da alk'awarij aure.
Wata ukku kafin mu fara jarabawar kare makarantarmu ya iso gidanmu dan ya gabatar da kansa ga iyayena tare da neman iznin aurena.Bayan doguwar tattaunawa da yayi da mahaifina suka tabbatar masa da basu da burin nayi aure a yanzu.
Abba ya kirani a falonsa ransa a b'ace.
Na shiga da sallama na durkusa a gaban Gwaggo Sara, ita ce yayarsa.
Mace mai son abin duniya da nuna ita hamshak'iya ce. Ba laifi mijinta shahararren mai kud'i ne a garin Katsina."Maryamah haka kika mayar da rayuwarki? Ki rasa wanda zaki turo ya nemi aurenki sai Abubakar din? Da matarsa da 'ya d'aya? Malamin sakandire? Kin yi wayon banza wallahi. Har dambe yake yi da matarsa fa."
Mahaifina dai baice uffan ba ya bar yayarsa taci gaba da balbalinta.
Abakar baya dukan mata a sanina, ita matarsa da ya doka laifinta ne kwalarsa taci akan yace ba zata fita ba, ya mareta ta rama shine dukan da aka bice gari ana yad'a cewa yayi mata. Itace ta sanar dani hakan da yake akwai kyakkyawar alak'a tsakaninmu da ita, dari bisa dari ta amince na shigo gidanta duk da cewar da yawa daga cikin makusantana sukan ce dani "Baraki take miki wallahi."
Amma ban d'auka ba na rik'eta matsayin 'yar uwa.Gwaggo Saratu taci gaba da fad'anta daga k'arshe ta shaida min da na kare karatu gidanta zan koma. Dan gwara nayi aure a birni inda ba zan sha hayak'in itace ba.
Wannan maganar ta k'ona raina.
Na dubi mahaifiyata da take a madafa tana hura wutar itacen da tak'i kamawa na fashe da kuka, Mama ita kad'ai ce take goyon bayan soyayyata da Abubakar duk da bata bani damar sab'awa umurnin mahaifina ba.Ranar monday jiki babu dad'i na shiga makaranta, tun abakin get na hango babbar k'awata Ameera tana taron yan makara. Ina isowa ta bani hannu muka gaisa kafin ta karbi jakata ta bawa d'aya daga cikin 'yan makaram da ta kai ajinmu.
"Amira sallami 'yan makaran nan akwai maganar da zamuyi."
Babu b'ata lokaci ta sallamesu, mu kuma muka nufi bayan ajujuwa."Amira sam basa son Abakar,ni kuma wallahi ina son aurensa ba shi da wani mugun hali face talauci da suke masa ikirari a matsayinsa na malamin makaranta. Ya kike ganin zamu yi?"
Amira tace.
"Babu shakka kina cikin jarabawa amma kiyi hak'uri ki d'auki maganar danginki, karki zo ki dage ayi miki aure baki ya kamaki kwana biyu ku samu matsala abu yazo yayi muni, shi aure lokaci gareshi babu makawa idan an rubuta sai kin aureshi, amma ni wallahi shi yafi bani tausayi dan yana tsananin sonki."
Maganar Amira ta kwanatar min da hankali, ita mai azancin magana ce duk da itace k'arama acikin kawayena biyu da nake ji dasu a duk fadin makarantar, ta biyun itace Sadiya, itama da muka kora mata bayani sai ta goyi bayan Amira suka ci gaba da kwantar min da hankali akan nabi iyayena."Mairama Abbanki yace sai dai na jiraki har shekaru shidda idan kin kammala karatunki, zai tambayeki a lokacin idan kin amincewa aurena. Mairamah zan jiranki amma dan Allah kada ki butulcemin."
Maganar Abakar a gareni lokacin da muka gama zana jarabawa muna cike da murna wani b'angaren kuma muna kewar juna.
Na tabbatar masa da babu matsala ni tashi ce har Abada.Cikin watannin da muka yi na jiran sakamako Abba yayi nasarar rabani da k'awata Sadiya, tun ranar da ta hadu da saurayinta a k'ofar gidanmu.
Daga lokacin ya kara canja min yake tsananin takura min, ya sanar dani kar na sake ya k'ara cin karo da k'awayena a gidan. Ya zagesu ya tabbatar min idan na biyesu zasu b'ata rayuwata, ba ko yaushe yake gida ba dan a Birnin Katsina yake aiki inda muke a Jibia. Matarsa daya ce acan da sukan yi canji da Mamanmu daga Baya Mamanmu tace tafi son zama gida ga baki d'aya.Sadiya ba ta cika kamun kai ba, tana da yawan samari da yawo, sab'anin Amira da kan yi fiye da wata ukku bata zo gidanmu ba. Nima ba zuwa nake ba ko nan da can musamman idan Baba yana nan. Islamiyya kad'ai nake zuwa a yanzu kasancewar nayi nisa sosai a karatun. Na jima da sauke alk'ur'ani ina kan haddarsa. Nayi littafai da dama na Musulumci.
Daga ranar da kaddarata ta fara itace.
Abakar yana ta k'ok'arin mu had'u amma abu ya garara mussaman yanzu da Babanmu yake hutu a gida lokacin azumi na kwana ashirin da biyu, wata k'ila hidimar salla yake son ya bani shi yasa na aminta da mu had'u a gidansa. Inda matarsa nake nufi...Ina zuwa...
YOU ARE READING
MAIRAMAH
General FictionMummumar k'addarar da ta datse rayuwata. rayuwata ta wujijjiga, ta zama abar k'yama da Allah wadai.