10~Shafi na goma.

407 60 13
                                        

Na had'a kayana ga baki d'aya na fito a tsakiyar falon gidanmu ina rusa kuka.
Baba ya fito da waya a hannunsa ya dube ni.

"munafukar banza da wofi sai ki tashi gidan gwaggonki zaki koma da zama saura wallahi naji ance kin sa k'afa kin fito ko k'ofar gidan nan, Kiga abinda zai shiga tsakanina dake, gashi kin ja zama uwarki kwanciya asibiti sai alhakinta ya kamaki, kin cuce mu Mairama kin rusa duk tarbiyar da muka yi miki."

Wani nauyi ya k'aru a zuciyata, dama na sani muddin Mama taji wannan labarin sai ta kwanta asibiti.
Amma ba zan lamunci zama gidan gwaggo ba, ba zan sake na kusanci abinda zai sai na kara sha'awar abinda na aikata ba a baya, na tsanamta kukana na durkushe a gaban Baba ina cewa.

"Baba kayi min rai ka barni na koma Jibiya, wallahi ba zan iya zama gidan Gwaggo ba, dan girman Allah ka barni na koma Jibiya, bana jin ina da sauran kwanaki masu tsayi a duniya ka taimaka ka bar ni na nemi yafiya a wurin Mama."

Ashe harzuk'asa nayi, sai duka naji a bayana, kafin nayi wani yunk'uri ya rufeni da duka da zagi, ni kuka shi ma kukan yake yi.

"Maciya amana, mayaudariya, ki koma Jibiyan inda shegen ya samu damar mayar dake karuwarsa, wallahi ni ban haifi karuwa ba..."
Kuka yaci k'arfinsa ya durkushe a gefen kujera yana saita kanshi, na rarrafa da zummar in rungume shi, ya bangalar dani har saida na kife.
Yaya Salis ne ya shigo aguje ya tayar dani, wani irin duhu nake gani ga yawan jini da naji yana zubo min ta k'asana. Ga jini a hanci da bakina, ga aman jini da na shiga kwarowa daga inda nake tsaye rungume a jikin ya Salis.

"Baba dan Allah kayi hak'uri ka bari na kaita asibiti..."

"Asibitin ubanka? Duk wanda ya kaita asibiti ban yafe masa ba har duniya ta nad'e. Maza-maza ta gaggauta barin gidan nan kafin na tsine mata."
Nidai ban san me ya faru ba, ban san wani hali na shiga ba, ban san tsawon lokacin da aka d'auka ba kawai dai na bud'e idanu na ganki a d'akin Halima,
***
"Sannu Mairamnah..."
Muryarsa ta doki dodon kunne na, ba wai burgeni tayi ba, ba dadi ta k'ara ba, illa zallar bugawa da zuciyata tayi, na juyo a hankali na sauke jajayen idanuwa akan shi.

"Au ta farfad'o ashe?"
Na tsinci muryar Gwaggo daga bakin k'ofar d'akin.
Ya juya cike da damuwa yace.
"Eh, jinin ma ya k'are tun d'azu na cire mata."

Ta k'araso gaban gadon, fuskarta a d'aure tace.

"Sannu Mairama, in banda abinki me nayi gardama da Ubanki. Ai gashi nan kin kara ma kanki ciwo bisa ciwo."
Ta wuce bayan tayi wa Jahid maganar da ban san me tace masa ba, na daiga ya mik'e bayan ya sakar min sanyayyen murmushi ya fice.

Aka barni ni d'aya a d'akin, ina k'ok'arin tattaro tunanin da ya kamace ni.
Tsoron Jahid nake yi, kamar dodo nake ganinsa, so nake na daina jin k'auanarsa na daina jin duk wani kusanci da yake tsakanin zuciyoyinmu.

Sai bayan da akayi sallar magrib Halima fa shigo dauke da jakar Islamiyya, tayi min sannu na amsa.

Tsawon sati d'aya da nayi a gidan, tamkar gidan yari haka nake jina, gashi tun ranar da na farka ban k'ara ganin Jahid ba. Sai dai ga dukkan alamu akwai wani shagali da 'yan gidan suke yi.Naji sauk'i a zahiri, jinin da zan iya cewa na bik'i ne ya daina zuba tun kwana ukku da faruwar hakan, amma zuciyata babu lafiya, yawan damuwa da tunani sun dagargajeta.
Ko kad'an ban rame ba, sai ma wani kumburi da na k'ara yi da fari, farin ya canja daga ainahanin hasken fatata.
Ranar da na cika sati biyu a ranar Jahid ya dawo.
Da magrib, ina zaune falon Gwaggo ina kara daddak'a haddara 40Rabbana da na kusa haddarsa ga ba daya, naji sallamar Jahid a bayana.
Ban juyo ba, sai dai na amsa sallamar da yake wajibi ne.
Ya zauna kan hannun kujerar da nake zaune ya karbi littafina.

"Mairamnah."
Ya kirani cikin sanyi, ban amsa ba, haka kuma ban bude idanuwa ba.

"Kin san gobe za a d'aura aurenmu?"
Na murmusa cike da takaici, bance masa komai ba sai k'ok'arin tashi da nayi.

"Wallahi Allah gobe kamar haka kin zama matata, baki ga Gwaggo suna ta shiri ba?"
A mamakance na mayar da dubana a kanshi.

"Ba zan aureka ba Jahid. Abakar zan aura."

Na watsa masa maganar a saitin fuskarsa cike da fushi.

"Idan Abakar ya aureki ya kuma gano kin haihu ya kike tunanin zai zauna dake?"
A hasale na dawo kansa.

"Ba abinda zai gane. Ko ka manta har yanzu ni budurwa ce?"
Ga mamakina sai naga hawaye akan fuskarsa, har yanzu kuma murmushin da yake bai gushe ba.

"Mairama kada kiyi tak'ama da tantin budurci dan tuni an yaga shi, ko kin manta lokacin da likita ya k'araki da kuka je tare da Salim? To idan baki sani ba, a lokacin yayi miki allura sannan ya yaye tantin budurcinki da k'arfe da kika ga ya tura maki..."

"Tas!"
Na d'aukesa da gigitaccen marin da ban san ya akayi na iya sa ba.

"K'arya kake Jahid! Ni budurwa ce, wallahi ban haihu ba. Ni ban tab'a zina ba, ka cuce ni."
Nayi kansa naci kwalar rigarsa ina bugunsa da iya k'arfina.
Halima da Gwaggo suka rugo a guje suna neman bahasi.

"Bazan aure shi ba, Gwaggo Ku aura min Abakar..."

Na dakata jin wani dumi a hancina, na sa hannuna na goge, sai naga jini ne. Wannan shine karo na goma kenan ina ganin jini a hanci na, musamman idan nayi kuka.

Jahid na fara gani a biyu-biyu, kafin kace me na fad'a kan jikinsa a sume.

***

Muje mana...

MAIRAMAHOnde histórias criam vida. Descubra agora