Ku kwantar da hankalinku my wattpadians, wannan short story ne ba zai daukemu dogon lokaci ba, kuma ba zan dauke shi ba ko cireshi na mayar dashi wani gun ba. Hasali ma sadaukarwace a gareku.
Kai tsaye gidansu Ameera na wuce, tayi mamakin ganina a yammacin, muka zauna muna hira da tattaunawa tsakaninmu har akayi kiran magrib, bayan nasha ruwa a gidansu muka yi sallama da sunan gida zan tafi.
Ameera bata barni ba har saida na hau abin hawa ta biya shi kudin da zai kaini unguwarmu, muna fara tafiya na sanar dashi ba unguwar nayi ba low cost zai kaini.Bai yi musu ba ya kai ni har k'ofar gidan Abakar ya ajje ni.
Duk yadda naji gabana yana faduwa hakan bai hanani shiga gidan ba bakina d'auke da addu'a.
Mu ka gaisa da matarsa cikin mutunci, ni har mamaki nake yadda bata kishina ko kad'an. Abakar ya shigo muka gaisa ya jani ya nunamin bangaren da yake gyaramin da sunan gidana. Rayuwata tayi tas har ina tarairayo irin soyayyar da zamu shimfida acikin gidan.
Muka yi hirarmu ta masoya ya bani abinda zai bani, ya goyani akan mashin d'insa ya saukeni a bayan layinmu.
***
"Gidan Ubanwa kika fito?"
Numfashina ya d'auke na tsawon dak'ik'u kafin ya dawo.
Zuciyata taci gaba da bugawa da karfi nayi saurin boye ledar dake a hannuna acikin hijabina.
"Baba? Yaushe ya dawo?""Mairama nace daga ina kike?"
Ya k'ara maimaitamin tambayar, cikin kid'ima nace."Gidansu Aunty naje, kuma Mama ta aikeni."
"Mu tafi gaban uwar taki, sannan ki bani abinda yake hannunki."
Na fara mutsinya, ganin ya tsareni da ido ya sa na fidda leda na bashi.
Ya shiga gaba, ina bin sa abaya.
Tuni jikina ya fara kakkarwa, ina jin zafi a zuciyata ina duba makomata muddin Mama ta karyatani."Ina kike?"
Ya fara kwala mata kira.
Itama a tsoracen ta dawo dan bata yi tsammanim dawowarsa ba.
"Ina yarinyar nan ta dawo? Sannan ubanwa ya bata wad'annan kayan?"
Yayi watsi da doguwar rigar atamfa, kwalin yawa da takalmi dake cikin ledar."Haba Alhaji sak'o fa nace ta karb'o min gidan Hajiyarmu."
Allah sarki, uwa uwa ce wallahi."Ni zaku mayar mahaukaci? Karfe goman dare zata karbo miki sako? Ke ki fada min gaskiya wallahi ko nayi miki mugun dukan tsiya."
Na fashe da kuka na durkushe agabansa. Tuni na yanke hukunci sanar dashi gaskiya."Baba Abakar ya bani..."
Kafin na iyar ya d'aukeni da mahaukacin mari. Ya shiga falo ya dauko wayar wuta ya shiga jibgata ta ko 'ina, na daure nak'i yin kuka face neman guduwa da nayi.
Tuni wani irin duhu ya mamaye ganina da kyar na iya lallab'awa izuwa d'akina ma fada kan gado ina kakkarwa. Har lokacin Baba bai daina banbamin fad'ansa ba, sai dai dukkan laifin ya d'ora shi akan k'awayena. Yana ta ik'irarin su suke lalata tarbiyar da yayi min.Zazzab'i mai zafi ya rufeni har safe jikina bai saki ba, fuskata ta kumbura sosai.
Har akayi Sallar azumi aka sallace ina cikin wannnan halin.
Bayan sati biyu da salla jarabawarmu ta fito cikin rashin sa'a na fad'i a physics kuma ya zama wajibi sai ina dashi.
Curwata kala-kala suka addabeni, na rame nayi bak'i sosai.
Yau tun safe nake kelaya amai, tun ina na ruwa har ya kai babu komai a cikina sai yunk'uri da nake yi. Cikin hakan na daure na shirya dan zuwa Islamiyya sai dai ina fitowa bakin k'ofar gidanmu na tarar da Baba.
Gaishesa nayi yak'i amsawa wanda hakan ya jazamini muzanta a bainar k'annena da yayyuna da suke zaune a k'ofar gidan.
Koda yake ni naso hakan tun da ya riga ya yafe gaisuwar tawa."Ke ki koma gida."
Babu musu na juya jiki a mace na koma gida, ko hijab ban cire ba naji yana kwalawa Mamanmu kira, jiki na rawa ta amsa kiransa."Kina ji ko? Wallahi wallahi idan yarinyar can ta k'ara saka k'afa ta fita sai na sab'a miki, ko ina kar ta sake zuwa har Islamiyyar na hana mata. Da jarabawarsu ta fito zata bar garin nan."
Fuuu ya ja babbar rigarsa ya fice.Na manta ban sanar daku na d'ad'e ina fama da ciwon Ulcer ba, dan haka yana cikin abinda yake wahalar dani ko azumi bana yi sai dai a fitar min da hatsi kullum.
Yanzu abin yayi k'amari daga amai har ya koma aman jini. Cikina yana halbamin sosai ga zuciyata da tayi nauyi. Ni duk a tunani na ulcer ce.
Ina bakin k'ofar d'aki, jinin dake fita a bakina duk ya lalata min jiki gashi ba ni da k'arfi kiran Mama bale ta kawo min d'auki. Baba ya shigo da sallama yaci karo da halin da nake ciki. Hankalinsa a tashe yayo kaina yana kwalama Mama kira."Hajiya yanzu kina cikin gidannan kin bar Mairam tana kusan mutuwa ko? To meye amfanin zamanki a gidan? Mairam sannu, tashi muje asibiti."
Mama da jikinta yaci gaba da rawa ta kamani zuwa motar Baba, ta koma ta dauko Hijabinta da nawa har zata shiga Baba ya tsayar da ita.
"Ina zaki? Ki koma ciki da Salis zamu je."
Nan ya kira babban yayanmu yaja motar muka nufi babbar asibitin dake garin Jibia.***
Likita ya gyara zaman madubinsayace.
"Alhaji kaga abinda Gwaje-gwajen suka bayar."
Cike da kid'emewa Baba ya cire hular kansa yana maimaita.
"Innalillahi wa'inna alaihirraji'una...Mairam? Mairam ya kike so nayi?"

BINABASA MO ANG
MAIRAMAH
General FictionMummumar k'addarar da ta datse rayuwata. rayuwata ta wujijjiga, ta zama abar k'yama da Allah wadai.