Uzuri ya giftawa Suwaiba Makwabciyarmu hakan bai bamu damar zuwa asibiti ba, da dare Babanmu ya dawo ya tambayeni ko munje, na sanar dashi bamu je ba.
Ga mamakina sai ya mik'o min k'aramar wayar Nokia, harda sim na mtn a ciki.
"Ki rik'e idan na fita zan kira ki.""Tohm nagode Baba."
Na karbi wayar jiki na rawa na kunna.
Da misalin karfi takwas Baba ya kirani, ya sadani da wani malamin Islamic nayi masa bayanin abinda ke faruwa.Wasu maganguna yayi min bayanin su, nayi godiya na karba na wuce daki.
Kamar wasa duk na sha maganin da Baba ya kawo sai na yini ina ciwon mara, hakan ya k'ara tsoratani zuciyata ta fara yimini waswasi.
Yau muna kan hanyar dawowa daga makaranta na tsayar da Yaya Salis a wani kemis."Yaya maganin kurajen nan zan sayo dazu da safe baba ya bani kudi."
"Toh kiyi sauri dan Allah."
Naci sa'a baice na kawo ya karb'omin ba, na shiga ciki na mik'a naira d'ari aka bani p.t.strp, abin awon fitsari. Na tura a jakata na fito.Muna komawa dama fitsari ya matsa min na shiga bayi da 'yar kwalba nayi fitsarin. Bayan nan nabi hanyoyin awo da aka rubuta bayan takardar abin na auna fitsarin na shanya akan windon dakina.
'Positive'
Na rud'e na kasa tantance banbancin dake tsakanin positive da nagetive.
"Me haka yake nufi?"
Yawan rudewar da nayi yasaka ni kiran Amira da gaggauwa."Amira ciki gareni, wallahi har awon fitsari nayi ya bani positive ya zanyi?"
Amira taja tsaki daga inda take kana tace.
"Cikin ubanwa? Bayan kin ce baku taba yin sex ba ya za ayi ciki ya shiga? Ki dai kara gwada pts din kuma ai Dr Salima tace idan infection yayi yawa har positive zai iya nunawa ko kuma idan wancan tsohon naki zai barki ki fito muje asibiti kawai."
"Amira kizo gobe mu tafi asibitin amma wallahi bani da ko sisi kuma hankalina ya kasa kwanciya."
"Karki damu, baki da komai fa. Ki shirya gobe zan kiraki muje."
Nayi mata godiya ta kashe wayar.
Hankalina ya kasa kwanciya har sai da na kara gwada fitsarina a karo na biyu, inda aka tuma nan aka fado positive dai.Wallahi ban runtsa ba daren ranar, nayi sa'a bama zuwa makaranta dan haka na zauna jiran Amira. Shiru har azhar bata zo ba wayarta kuma kashe, hakan ya sa na kara shiga damuwa fuskata ta kumbura sosai.
Wata dabara ta fado min, na debi fitsarina na fita bayan layin gidanmu na kai a wani kemis."Malam dan Allah Mamana tace ka auna mata fitsarin nan."
Ya karb'a yace in zauna waje in jirasa.
Bayan mintuna talatin yace in shigo in karba.
"Ki kawo naira dari, ciki gareta hakan ya nuna."
Kut! Na had'a wasu mugayen yawo da suka yi barazanar huda makwarbazo na.
Na cire naira dari na basa na karbi sakamakon da ya bani da sauran fitsarin.
Ikon Allah kadai ya isar dani gida. Zuciyata naji ta koma gefe d'aya tana bugawa da sauri ga wani irin ciwo da nake ji a cikinta. Ba ni da wani zab'i da wa wuce na kira Yaya Jahid."What? Ciki? Ina bazai tab'a faruwa ba, wallahi ban tab'a shigarki ba ban tab'a sex dake ba Mairama. Amma kada ki tashi hankalinki gobe zan aiko Salim ya daukeki kuje inda wani likita ya duba ki."
Na goge hawayen da suka zobo min na kokarta nace.
"Tou shikenan, gobe sai ya tsaya ta bayan layin mu, bari in kira Amira sai muje tare."Daga haka muka yi sallama tuni zuciyata ta tsinke.
Amira tace zata zo da karfe goma kafin ta wuce makaranta, naji sanyi a raina Amira kawar arziki ce ba zata juya min baya ba.
Ga ciwon ulcer da ya rufeni tun jiya da dare, ga zuciyata da ke ciwo ga rashin nutsuwa bale bacci haka na fita tsakar gidanmu tun da asuba nayi wanke-wanke, nayi wanka na shirya zaman jiran Amira.
Ina cike da jimami har karfe tara."Mairam gani kofar gidanku."
Na katse wayar aguje na fita. Tana tsaye tana sallamar dan mashin.
Rungumeta nayi na fashe da kuka.
"Haba Mairam meye haka muje ciki mana."
Ta jani har dakina muka zauna kan katifata da yau kusan sati daya kenan bata ga kimtsi ba, ko sharar dakin na daina."Amira wallahi ciki gareni kalli yadda cikina yayi girma."
Na bude mata shafaffen cikina da ko alama baiyi kama dana masu ciki ba. Ta shafa cikin kana ta buge kafadata."Shegiya dama nasan haukarki ce, ina ciki yake anan?"
"Amira ba zaki gane ba, sau ukku fa ana aunawa ciki yana bayyana, kuma kiga maganin da Baba ya bani idan nasha sai naji marata tayi karfi ta fara ciwo. Wallahi akwai al'ajabi da rudani acikin wannan lamarin Amira."
"Issok ki daina kukan mana, ba kince shi Jahid din yace kuje asibiti ba? Ki bari kuje sai muji amma ni na tabbatar da duk sharrin ciwon sanyi ne."
Nan taci gaba da kwantar min da hankali har Salim ya iso, na shaida mata muje ta rakani, bata yi gardama ba muka tafi tare.
Ita ta hakik'ance babu ciki ajikina, yayinda ni kuma zuciyata ta bani akwai ciki ajikina.Wata muguwar unguwa Salim ya shiga damu, mafi yawansu duk iyamurraine har muka iso kofar wani gidan haya mai dauke da dakuna goma aciki. Daga ciki muka shiga cikin wani daki da Salim yayi mana iso.
Wani inyamurine ko baccin safe bai tashi ba, shigarmu ta sanya shi mikewa ya zura rigarsa, suka yi magana da Salim kafin yace ya fita ya bamu wuri."Ki zo ki kwanta anan."
Na mike tsaye a tsorace na isa gare shi, ya nunamin shimfid'arsa da ya tashi, naki kwantawa amma Amira tace in kwanta.
"Ki bude cikinki."
Kafin ma nayi masa gardama yasa hannu ya dage rigata, ya sassauta zanena izuwa kasa. Ya dora wata nakura bayan ya daddana marata ya fara latsa nakurar.
Kamar minti daya yace in mike."Cikin ya kai four months, dan haka ba zamu iya ciresa nan ba."
Amira ta zaro ido a tsorace tace.
"Ciki? 4months kuma cirewa Mairam?"
Na kama hannayenta na rik'e ina cewa."Amira dama na gaya miki, kuma dole aciresa idan ba so kike yi Baba ya koreni ba. Wallahi da ya san ina da ciki gwara na mutu."
Amira hankalinta ya tashi sosai, ta juya ta kalli likita tace.
"Dr. Yanzu dole sai an cire? To kuma ya za ayi?"
"Da cikin bai shiga wata hudu ba da zamu iya ciresa yanzu a wurin nan, amma tun da ya cika wata hudu dole saidai muyi miki abinda zai zube daga nan zuwa gobe da safe, hope gidanku babu kowa?"
Amira ta share zufar dake tsefomata tace."Ba zaman kanmu muke ba, muna da iyaye. Yanzu babu wata hanya?"
Kai tsaye yace mata babu."Ki bamu wuri zamu fara aikin ko?"
Amira ta mike a sanyaye ta fice daga dakin.
Ya kalleni cikin wani irin yanayi yace."Zo ki kwanta anan, ki cire wandonki."
Ya mik'e ya kulle k'ofa.Na daure na kawar da abinda zuciyata take raya min, na cire tsoro na dangana na cire wando na kwanta. Ya zo ya ware min k'afafu.
Ku zo mu je...

ANDA SEDANG MEMBACA
MAIRAMAH
Fiksyen UmumMummumar k'addarar da ta datse rayuwata. rayuwata ta wujijjiga, ta zama abar k'yama da Allah wadai.