"Na rantse da girman Allah sai Mairam ta auri yaron nan, idan ba haka ba, ke Saratu dake Jamila ku zama shaida zan cireta daga cikin 'ya'yana."
Hayaniyarsa, yawan d'aga muryarsa tun daga falon Gwaggo ya tashe ni da nannauyan baccin da nake.
Na mik'e da kyar na lek'a falon, su shida ne, wannan karon harda Mamata a zaune wurin, giyar kewarta ta jani na ruga aguje na fad'a jikinta ina kuka.
"Mama ashe ba zan mutu ba har sai na ganki, Mama dan Allah ki yafe mun duk abunda nayi maki na tuba ba zan sake ba, na tuba ba zan kara aikata irin haka ba."
"Ke!"
Baba Bello ya daka min tsawa daga inda yake zaune a kusa da Baba."Wai ba zaki fad'a mana shegen da lalata rayuwarki ba?"
Nayi shiru ina dana sanin zuwa wajen.
Babanmu ya kalle ni da kallon tsana yace."Barta Bello, bama buk'atar ji dan mun san ko waye, amma abinda nake so dake shine ki sani cewa aurenki da Jahid babu makawa."
"Baba wallahi bana son Jahid, baba ba zan iya auren shi ba. Baba kayi min rai kar ku had'ani da Jahid."
Mamanmu kad'ai ke zubar da hawaye a wajen, nidaj wannan ne zab'i na ba zan iya auren Jahid ba."Mairamah, ban tab'a tunanin yi miki auren dole ba tun ta sowarki, amma zan baki zab'i a yanzu. Ki aure Jahid zan yafe maki laifinki kuma na sanya miki albarka, na kuma rokar miki Ubangiji, ko kuma ki aure Abubakar, na cireki daga cikin jerin 'ya'yan da na haifa a duniya, na barki da duniyar ko zata koya maki hankali."
Duk wasu jiyojina suka k'ulle, wani tsoro ya k'ara damfare k'irjina,ban kai ga yin zabi ba naji Mama na cewa."Haba Alhaji! Wannan hukuncin yayi tsauri mana, ai duk halin da yarinyar ta shiga kai ka jawo mata..."
"Dallah ki rufawa mutane baki. Har ke isa muna yanke hukunci ki sako bakinki?"
Gwaggo Saratu da katsewa Mama hanzari, naji ciwo da katsewar izgili da tayi mata, har akwai wanda ya kamata ya saka baki a al'amarina kamar uwar da tayi nak'udata? Me yasa ba za a yi mata adalci ba, waya san tsawon daren da ketare bata runtsa ba duk akaina? Sai yau za a kwatseta akaina."Mama kiyi hak'uri, Baba indai zaka yafe min, indai rayuwata zata dawo kamar ada, zan aure Jahid, zan yi maka biyayya. Baba ka yafe mun."
Na fashe da kuka mai tsanani na rungume Mama da itama kukan take yi.
Daga nan aka hadu kaf mutanen gidan muka dauki hanyar Jibiya, ashe shagali sosai suka shirya har walima ake a ranar juma'ar ni ban sani ba.Amira na Jibiya, wajen k'arfe bakwai na maraice tazo ta daukenj da motar yayanta muka fita, da iznin Mama."Mairam kin ga wata k'iba da kika yi? Baki da lafiya Mairama kuje asibiti wallahi."
Nayi murmushi mai ciwo, wanda ni kad'ai na san meye manufarsa."Amira wane asibiti zanje? Ki duba tun ranar da na shiga matsalar nan Baba bai tab'a barin naje asibiti ba, basu damu da lafiyata ba su dai mutuncinsu, Amira kin aman jinin da nake yi kuwa? Amira kullum sai jini ya dinga fitowa ta hancina fa."
Cike da damuwa Amira tace.
"Subhanallah! Ai bai kamata kiyi shiru ba, bari zan kira Jahid din gwara kuje kiga likita wallahi."
"Hum kawai dai ni wasiyya zan bar miki, lokacin da babu ni a doron k'asa ki rubuta labarina, koda Allah zai sa a samu canji daga masu hali irin nawa, masu hali irin na mahaifina da masu hali irin na Jahid."
"Mtss! Kema ai zaki iya rubutawa kafin ki mutun."
Ta kai min duka a kafada, na kyalkyace da dariya ina tsokananta.Haka muka ci gaba da jajantawa juna har muka iso gidan Abakar. Tun da yaji zancen aurena da safe ya yanke jiki ya fad'i.
Yana kwance a kan katifar da aka shimfid'a masa a sashen da muke kira nawa.
Yana jin sallamarmu ya mik'e zaune."Mairama? Dan Allah aure zaki yi ki zauna da wani ba ni ba? Mairama kada ki barni kinji? Kizo wallahi komai na bukatunki zan sauke miki."
Na fashe da matsanacin kuka, ina jin tausayinsa, ina jin tausayin kaina.
Na mik'e a wahalace, nace."Abakar, ba wanda nake da sauran lokacin zama dashi a duniyar nan. Dan Allah nidai..."
Na jinkirta tare da durkusawa agabansa.
"Nidai Mairamah ka yafeni, ka yafe ni Abubakar koda za a tambayi hakkinka akaina."Na mik'e a guje na fice daga wajen. Ban san me suka zanta tsakaninsa da Amira ba, na dai ga ta fito hannunta rik'e da kudi muka wuce.
"Karb'i."
Ta mik'o min kudin dake hannunta."Dubu goma ne ya baki, gudummuwarsa, yace ya yafe maki har a gaban Allah, kuma kiyiwa mijinki biyayya. Ni wallahi Mairama kina kashe min jiki, kina sakani yawan fad'uwar gaba. Dan Allah ki nutsu ki cire komai a ranki, Jahid fa kina son shi meye aibin zama dashi?"
Ba zaki gane ba Amira, amma dai da sannu zaki gane.
Bance komai ba sai dariya mai sanyi da nayi, kuma har a raina naji dariyar, hararata Amira tayi tace.
"Nidai sai da safe, dan Allah kada ki bari nazo na ganki cikin damuwa."
"Insha Allah, zan yi yadda kike so Amira."
Muka yi sallama na lababa na shiga gida.
Da dare, na duk'ufa wajen kai kukana a fadar Ubangiji, nayi sujjuda mai tsawo ina neman gafararsa da neman mafita. Sai karfe ukku da rabi na mik'e akan k'afafuna, na koma kan gado na kwanta.
'Yan uwa da abokan arziki suka shaida daurin auren Mairama Kabeer da Jahid Salim.
Ni kaina ban san inda na samu farin ciki da walwalar da ke kan fuskata ba, kowa sai mamaki na yake yi, da la'asar Amira da gayyar k'awayena suka kunna kid'a da sifikun dakin yayanmu da suka dauko ban yi sanya ba nace nima fa sai nayi rawa. A filin gidanmu na fito na dan taka.
Aka dau ihu ana dariya, kowa murna yake musamman Amira da take mamaki na.
Da magrib aka shirya ni cikin atamfa fara da dogon mayafi muka dauki hanyar Katsina, anan gidan Gwaggonmu part din baya aka gyarawa Jahid kafin mu koma Abuja, kamar yadda suka ce.

ESTÁS LEYENDO
MAIRAMAH
Ficción GeneralMummumar k'addarar da ta datse rayuwata. rayuwata ta wujijjiga, ta zama abar k'yama da Allah wadai.