Mairamah
Kamala_Minna
Zo ka bani drum daya.@Mum Ama😥😥😥this is for M.B wallahi cin hanci ne na bayar.
Bayan kowa ya watse sai k'awayena Sadiya da Halima gwaggo, sai uwar gayya Amira dake ta hidiman gyaramin gida.
Amira ta kama hannuna lokacin da muka dukufa dasu Sadiya muna hiran makaranta da dare-dare tace.
"Mairamah."
Na mayar da hankali na akanta na amsa."Me kike boyewa a k'asan zuciyarki ne? Wannan annurin da kike yi, wannan walwalar da murna tsoro suke bani."
Ta shafa gefen fuskata, bance komai face nima tsoron da naji ya d'arsu a zuciyata, har ga Allah na daina jin bacin rai, duk wani kunci da nake dashi safiyar yau ya wanke."Mairama, ga Jahid nan ya shigo shi kad'ai, sai da safe, ki kula da kanki. Kiyi addu'a sosai kinji. Ina sonki fisabilillah."
Ta manna min kiss a kunce, nayi murmushi na fara goge hawayen da suka zubo min."Amira ki kwana nan kada ki tafi tsoro nake ji."
Na rik'e hannunta.
Ta juyo da sauran karfin guiwarta ta girgiza min kai."Yawwa yanzu na san Mairam ce da naga kinyi hawaye, hum kunji wai in kwana anan..."
Ta fashe da dariya tana dunguremin kai."Saida safe."
Ta mik'e, har ta kai k'ofa nace."Dan zo dan Allah."
Tana zuwa nayi mata rankwashi na haye can karshen gado ina dariya."Tabdi! Zan kyaleki yau amma wolla sai na rama gobe."
Dai-dai lokacin Jahid ya shigo, suka gaisa kana ta same su Halima a falo suka wuce sashensu Gwaggo.
Jahid ya shigo da sallamarsa mai sanyi, haka kawai sai naji tausayinsa ya dirarmin a zuciya. Ya karaso kan gadon ya zauna bayan ya ajje ledar dake hannunsa.
Ban rufe fuskata ba, haka kawai nake jina kamar ba amarya ba."Amaryata."
Ya riko hannayena ya hada da nashi masu dumi sosai.
Na d'ago idanuna da suka fara kankancewa na zuba a fuskarsa.
Ban san ya akayi ba na sakar masa murmushi mai sanyi, shima murmushin ya sakar min kana ya sanyani acikin rik'onsa, nutsuwa ta saukar min har a k'asan ruhina.
Ya bubbuga bayana, yana sanyaya min."Zo kici abinci, kinji."
Banyi musu ba, na sauko bayan ya gabatar min da madara mai sanyi da naman kaza, cikin nishadi tamkar ba Mairam da Jahid ba muka ci naman sosai, ni rabona da naci abinci irin haka har na manta.
Na shiga bayi na rage marata na fito bayan nayi arwala.
"Yaya Jahid bari in salla.""Jira ni mana."
Ya mik'e bayan ya rage manyan kayansa zuwa jallabiya.
Mun jima akan sallaya har sai da naji bacci yana daukata. Na dauko sabon kur'anin da Mama ta bani na karanta shafi goma na farkon suratul bak'ara."Yaya bacci yazo, kayi min izni in kwanta?"
Ga dukkan alamu yana mamakin sauyina, da sanyin da nayi. Ya riko hannayena ya fara cewa."Mairama, yanzu ba kamar da bane, ni mijinki ne mijin sunna, yankin ibadarki, Mairama ina so ki dauke duk wani rud'ani da wani rashin fahimta na can baya, kizo mu gina rayuwarmu a tsalkake, Mairama ina sonki son da ba zan taba iya barin ki ba. Son da ba zan so kiyi nesa dani ba. Dan Allah Mairama ki zauna dani na tsawon rayuwata, Ki aminta na inganta rayuwarki."
Nayi wani irin murmushin da ya bayyana fararen hak'orana.
"Yaya zan zauna da kai har lokacin da ruhina zai rabu da gangar jikina. Har zuwa lokacin da zan kwanta dama, bayan nan zan yi addu'a gobe a lahira mu hadu a aljana inuwa d'aya."
Na fashe da kuka mai hade da dariya, shima kukan yake yi, dukanmu muna tuna yadda rayuwa ta wujijjigamu acikin kwanaki k'alilan. Muka yiwa juna alkawurra da dama a lokacin, muka yi aniyar goge ciwon tab'o da rayuwa tayi mana, tabon kawai muke bukata dan ya zame mana darasi anan gaba.

VOUS LISEZ
MAIRAMAH
Fiction généraleMummumar k'addarar da ta datse rayuwata. rayuwata ta wujijjiga, ta zama abar k'yama da Allah wadai.