4~Shafi na hudu.

514 55 1
                                    

Salamammen hannunsa akan k'irjina wanda ya saka ni jin wani irin abu, tamkar gizo-gizo na yawo akan fatar jikina.

"Haba Yaya Dan Allah ka daina..."
Ban k'arasa ba ya had'e bakunanmu a wuri d'aya, ya fara wani irin salo wanda ban taba jin irin wannnan yanayin tun kafuwata a duniya ba. Yaci nasarar luguiguita duk wani sashe na jikina.
Tuni ya cire dan towel dinda nake kuri dashi, ga mamakina, zuciya bata so amma gangar jiki ya gagara k'in karb'a.

"Come on Baby, please Kiss me."
Ya fad'a cikin narkakkiyar muryarsa da yasa na rufe idanuna na tsawon dak'ik'u kana na bud'e su a hankali. Na k'ok'arta turesa dan na mik'e cikin rashin sa'a hakan ya bashi wata damar d'ora bakinsa akan na fulanina.
"Zuz! Zuz! Zuz!"
Kamar wannan kalamar na yawo a jikina fa.
Jahid bai barni ba, haka kuma ban samu k'arfin guiwar hanashi ba har sai da naji hannunsa dake kan cinyata yana k'ok'arin mik'e hanya. Nayi saurin rik'e hannunsa a zabure na mik'e naja hijab d'ina. Na ruga a guje izuwa d'akin Halima na datse k'ofar d'akin.
Gabana sai falfalniya yake yana fad'uwa, tsoro mai tsanani ya d'arsu a zuciyata. Ashe haka yake? Wannan ce manufar soyayyarsa a gare ni?
Raina ya bak'anta,yayi d'aci. Sai dai na samu nutsuwar bugawar zuciya kana na wuce bayi. Wani farin abu mai kama da majina na gani a k'asana. Ko da bani da tabbaci nasan alamun motsuwar sha'awa ce.
Na kimtsa kaina na fito na shirya cikin kayana na hada jakata da na zo da ita.
Ina jin dawowarsu Gwaggo naje na gaisheta na sanar da ita zan wuce gida.

"Assha! Gashi driver ya fita amma kamar naga motar Jahid jeki ce yazo ya kai ki."

Akan me? Salon ya k'ara murk'ushe ni a motar?

"Gwaggo bari in hau adaidaita bacci ya Jahid yake."

Ta janyo jakarta tace.
"To shikenan karb'i ki hau mashin, ina gaida uwarku."
Na karb'i d'ari biyar a hannunta nayi godiya na fice.
Bini-bini wannan tunanin yak'i barina sakat a yau, duk na zauna abinda ya faru tsakaninmu nake gani sai naji tsigar jikina ta tashi.
Babanmu bai dawo ba sai da safe dan haka na shige d'aki na kunna wayata na kira Abakar. Ina jin tausayinsa da yasan abinda na aikata a yau da ko harbeni zai iya.

***
Yau kusan sati hud'u kenan ban lek'a gidansu Kubra ba, kuma bana d'aukar kiran Jahid duk yadda ya nace. Karshe ma na kashe wayar idan bani zan kira ba ba kunnawa nake ba.
Yau kam na tashi da murna jin cewar Sadiya da Amira zasu kawo min ziyara. Ita Sadiya ta shigo Jibiya ne tace ba zata koma ba har sai ta zo wajenmu. Tun jiya tazo ta kwana gidansu Amira.

Ban girka musu komai ba kasancewar bani da ko kwabo, Baba banda kudin cin abinci a makaranta ko naira baya bamu, gashi ko amakarantar bani da 'yanci dan ajinmu d'aya da Yayana wanda nake biyewa ma. Ko sallama bata had'ani da kowa.
Yaya Salis na rok'a ya bani d'ari ukku. Ina shirin fita na siyo koda Indomie ne sai gasu sun yi dirar mikiya.
Nayi tsalle na fad'a jikin Sadiya ina murnar wata sabon gani. Yaushe rabo?

"Ni baki yi kewata ba ko? To wallahi zan tafi."
Amira ta fad'a tana hararata.
Nayi saurin rungumeta ina dariya.
"Ai wallahi kin san nafi sonki ko?"
Tayi dariya itama, naja su muka wuce d'akina bayan sun gaishe da matar babanmu.

"Mairama ina Abakar? Kin ji matarsa ta haihu ko?"

Ameera ta tambayeni, nayi murmushi nace
"Yana nan yanzu ma ma sanar masa zaku zo duk yana gaisheku."

Kafin waninsu ya k'ara cewa wani abu muka ji sallama a bakin k'ofar d'akina.
Muka juya a tare dan tuni ni na san ko waye.

"Ina wuninku."
Ya fad'a acikin halin gajiyawa.

"Lafiya kalau."
Sadiya da Amira suka karb'a.
Nayi saurin kawar da kaina daga dubansa. Ya rame sosai ,kamar yana cikin damuwa.
Bai k'ara cewa komai ba daga hakan ya juya ya bar bakin k'ofar.

"Mairama wannan fa? Wallahi ya had'u wai kin ga sajensa? Innalillahi."
Sadiya ta dade da ganin idi zindir.
Na harareta kafin nace.
"Ya Jahid ne fa da kika sani."
Ta kwalo ido waje kana ta rufe baki tace.
"Kam! Amma yaron nan ya k'aro walak'anci wallahi ya mugun k'ara kyau, kodai bleaching yake naga ya k'ara fari?"
Mu kyalkyale da dariya.
Amira ce ta tab'e baki tace.

"Amma dai da ganinsa akwai walak'anci, kin ga wani yauk'i kamar yazo gaban jakkai."

Ita dama haka take, tak'i jinin walak'anci ko a nuna ita bare ce.

"Hum amma dai fad'a kuka yi ko? Naga kwayar idanuwanku tana neman yafiye."
Amira ta fad'a tana kama hannayena.
Masaniyace akan halayya musammam ta zamantakewa na jima da sanin hakan. Ita kad'ai ce ta isa ta gano ina cikin damuwa ko idan nayi karya ta sanar dani karya ce nayi.
Na murmusa nace.
"Eh."
Nan na sanar dasu dalili.

"Kai amma ke jaka ce wallahi, dan ubanki idan baki bashi ya tab'a ba wa zaki baiwa? Naga dai ai har gidan nan an san yana sonki kuma aure zaku yi. Ni wallahi baki ga yadda muke da Sadiq ba, muna shan minti sosai kuma wallahi bai tab'a shigata ba."

Kafin ta rufe baki Amira ta watsa mata harara.
"Ke kam Sadiya zaki mutu da burin auren Sadiq dan wallahi ba aurenki zai yi ba. Kuma ke Mairama je ki yi abinda tace idan ya halakaki ya gujeki zaki gane."
Sadiya ta kaiwa Amira duka tace.
"Wallahi ba wani halakawa. Ke Amira ba kya jin feelings ne?
Ai budurcinki ba zai zube ba. Kina nan virgin din ki. Wallahi ki sake masa kuci soyayya amma dai karki kuskure gigita ta saka ki, ki barshi ya shigeki."

Amira bata k'ara cewa komai ba face tsaki da taja.
Ta mik'e tare da jan jakarta tace.
"Ku dai acciki. Ni banda wannan lokacin na izgilanci."
Ta fice daga d'akin yayin da Sadiya ta saka dariya.
Mu ka bita a baya, koda muka fito har ta hau adai-daita.

"Amira ba zaki sauko ba? Ki zo zan nuna miki wani abu."

"Mairam na wuce, Mama na jirana."

Sadiya ta d'aga mata hannu tana cewa.
"Shegiya nagode. Kema zaki dawo a hannu ai."
Sadiya ta kara cewa.
"Ki ga kud'in da ta bani."

Nace.
"Kin gode, Amira nada kirki."

"Ke! Waccece anan? Mairam me na fad'a maki? Bana ce kada na k'ara ganin wannan 'yar iskar a gidana ba? Shine ta biyoki har anan ta bata ki?"

"Baba..."
"Yi min shiru! Ke kuma wallahi idan kika kara zuwa gidan nan sai na bata miki, lalatacciya."
Ya watsawa Sadiya wani mugun kallo.
A hasale ta haye mashin da ta tara ba tare da tace komai ba suka wuce.
"Wuce mu tafi ke kuma."
Na koma cikin gida ina rusa kuka kamar raina zai fita.

Ina zuwa...

MAIRAMAHWhere stories live. Discover now