8~Shafi na takwas

438 55 5
                                        


Wani karfe mai kamar sirinji kamar sitefula ya dauka ya tura a kasa na.
Na fasa k'ara ina kokarin mikewa ya dafeni.

"Sorry ki tsaya a hankali."
"Toh."
Ya dago kansa da mamaki karara yace.
"Unbelievable! You are virgin. Ke budurwa ne ya akayi kika samu ciki?"

Wani kololon bakin ciki ya taso min na fashe da kuka mai tsanani.

"Sorry kina jin zafi sosai ko? Yi hakuri ba zan tab'a ki ba."
Bayan yayi abinda yake ya cire karfen ya bini da kallon mamaki.

"kije wajensu gani nan zuwa zamu saye wani allura a shago."
Na mik'e da kyar na mayar da wandona na fita.
Ina shiga motar Salim,na fada a jikin Amira na fashe da kuka.
"Amira Jahid ya cuceni ya hadani da marar imani, Allah ya isar min, wayyo marata."
Na dafe marar ina jin yadda take jujjuyamun.

"Yi hakuri Mairam, in bera da sata daddawa ma da laifin warinta. Ke kika jawa kanki wannan matsalar sai dai a kiyaye gaba."

Amira ma kuka tayi min ganin yadda nake rik'e marata ina kuka.
Tsawon mintuna kafin Salim ya shigo tare da marar imanin muka fara tafiya.
Nayi kokarin cijewa na mike zaune na hadiye ciwon da nake ji.
Ai fa banga bala'i ba sai da aka zo yi min allaura a hannu, abinda na tsana tun ina karama kenan.
Na fashe da kuka na tirje naki bayar da hannuna, saida Salim ya sa baki kana na cire hannuna daga Hijabi aka yimin allurar. Na ci gaba da jero Allah ya isa da yin Allah wadaran hali irin nawa.

Anan muka ajje likitan bayan ya bayar da wani maganin yace in shanye anan take.
Na sha maganin ina mai jin bak'in cikin halin da na same kaina.

Ashe dai ba a isa a yiwa Allah wayau ba, astgafirrulah, ah to kamar shi muka so yi ni da Jahid, yanzu nafi wadda ta aikata zina zunubi mai dinb'im yawa. Ga zunubin zina ga na zubar da ciki.
Salim yana ajje mu a bayan layi muka fara tattakawa nida Amira, wasu ruwa naji suna zubo min tamkar fitsari.

"Na shiga ukku Amira fitsari yana zubo min."
"Ni dai mu tafi ko so kike sai jinin ya fara zuba akan titi ko fallasa kanki a duniya?"
Ta jani da karfi muka wuce. Muna shiga gida muka wuce dakina na cire dogon hijabin da ya jik'e jagab, na cire zanina na daura wani har a kirji.
Ruwan suka ci gaba da zubowa babu kakkautawa, ga rawar sanyi da nake yi, ko labb'ana na kasa hadewa akan rawar sanyi, kuma ba sanyin nake ji ba.
"Amir..rraa mutuwa wallahi zan yi."
Na fashe da dariya mai hade da hawaye ina durkushewa akan tulin tsumman da na tara kar na jike dakin.

"Dallah ki daina yiwa mutane zancen mutuwar nan kin san da mutuwa kika bude kafa wa Jahid?"
Na fashe da kuka ina cewa.
"Amira wai baki yarda dani bane? Baki san kaddara bane?"

"Mairam wannan kadaddara taki zababbiya ce daga gareki. Kina bani tausayi wallahi, ni nafi danganta wannan kaddarar daga mahaifinki take, yafi komai zagin diyan wasu, to yau yazo ga tashi nan tana zubar masa da jikansa."
Na sa hannuna na buge bakinta, ta fashe da dariya tana cewa.

"Ai wallahi bakin ciki kike mana ki bari muga hadadden Babynmu da zai zo duniya uwarsa na budurwa."

"Amira tashi ki tafi."
Na ce ina tura kanta.
Taci gaba da dariya da dauke min hankali har ruwan suka daina zuba, na wuce toilet na watsa ruwa na fito.
Babu abinda nake ji face marata dake murdawa kadan-kadan.
Sai ruwa da nake yawan sha.
"Nidai bari in wuce gida kinsa na rasa aji a yau sai dai monday."
Ta mike ta saba jakarta.

"Bari inzo na rakaki."

"A'a maman Baby yi zamanki."

Na dage har saida muka fita tare, ta wuce tana mai jimami ta barni cike da kewa da sabon ciwo.
Na koma gida na kasa zama na kasa tsayi na kasa kwanciyar har dare.
Ina ta jiran zubewar ciki har safe banga komai ba face dimb'in wahalhalu da nasha.

Da na sanar da Amira sai tace.

"Kila namiji ne Mairam, kuma wallahi zan baki shawara kiyi hattaara kada ki rasa rayuwarki ta wannan hanyar ki mutu a kafura. Kiji tsoron Allah ki bar cikin nan."

Naji tausayin kaina na fara kimtsa yadda za ayi na bar gidan nan da zaran cikin nan bai zube ba.
Na kira Salim na fada masa. Ban san ya suka yi da Jahid ba sai bayan la'asar da naga Jahid a gidanmu, ya baro Abujar kenan. Wannan karon yafi ko yaushe ramewa da yin bak'i, kyaunsa ya rage da kaso ashirin.

"Mairam ni nayi mamaki wallahi, gaki budurwarki kuma ace ruwan ciki sun shiga cikinki? Mu bamu yi sex ba. Wannan al'amarin da rud'ani."

Sai naji haushinsa ya kamani, to me yake nufi da hakan, meye marabar dambe da fada?

"Shirya yanzu zamu ga wani likita muji yadda za a yi."

Da kyar ya tursasani muka fita tare.
Wurin wani sabon azzalumi aka hadani dashi, shi wannan yafi wancan rashin imani dan allurar ma daka min ita yayi cike da mugunta.
Na dawo gida ina kuka da rawar sanyi.
Koda k'arfe takwas na dare yayi bana iya daga kafafuna. Ga wata jijjiga da jikina yake yi, ina cikin wannan halin naji an buga kofar dakina, dai-dai da lokacin da jini ya balle ya fara zubo min.

Nayi shiru tamkar bacci nake.

Aka ci gaba da bubbuga kofar da karfi.

Aka ci gaba da bubbuga kofar da karfi

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Mairamah.

MAIRAMAHWhere stories live. Discover now