13~Shafi na sha ukku.

751 90 54
                                    

K'arshe!

A garkar gidansu Mairama aka shimfid'a tabarmi da yawa, dama akwai masallaci kusa da gidansu, nan take cikin mintuna k'alilan unguwar ta tumbatsa da jama'a.
"Jiya aka d'aura auren, ance bata son mijin Abubakar din malam Sidi take so. Zuciyarta ce ta kumbure har jijiyoyi suka tsinke, ga rashin jini, sosai jininta yayi k'asa wannan ne yayi sanadiyar ajalinta na dare d'aya."
Wannan ne jita-jitar da ake ta yad'awa tare da jajantawa juna.
Bayan duk wani mai hakki da gawar Mairama ya gana da ita aka fitar da ita da waje.
Aka sallaceta aka yi aniyar sadata da gidanta na gaskiya, gidan da kowa yake fatar ya kyautata.
Abu kamar wasa, Baba ya kasa yarda Mairama ta rasu har saida ya ga an rufeta ruf acikin k'asa. Ya duba gabas da yamma yaga duka matacci ne. Yayi tsaye akan kabarinta yana k'ok'arin fahimtar al'amarin da yake faruwa.
Baba bello ne ya ahama da abinda yake faruwa dan haka ya rik'o hannunsa suka jiyo, yana da tabbacin a yanzu Mairama tana jin takun tafiyarsu, yana mai fatan bata bak'in ciki da barinta da suka yi a wurin, yana fatan haske ya yawaita gareta, yana fatan mala'ikun rahama ne a tare da ita, yana fatar Mairama ta huta a kabarinta, Mairama ta samu 'yanci.
Zuciyarsa taci gaba da k'onuwa har suka iso gida ana kabbara.
A lokacin ne Amira ta rugo a guje ta fad'i a gabansu.
"Baba dan Allah kun bar Mairama ita kad'ai? Acikin k'asa ? Baba tsoro nake ji, Baba Mairama ta bar ni..."
Mahaifin Amira da yayanta suka yo kanta a guje aka kwasheta.

Har yanzu dai Baba bai runtsa ba, bai kuma yi koda kwalla bane, shi dai yana jin wani nauyi a zuciyarsa, yana jin kamar almara abinda ke faruwa.
Duk wanda yazo makokin sai ya koka ko kuma ya girgiza da kalar mutuwar Mairama.
A cikin gida ma haka al'amarin yake.
Jiya kamar warhaka gidan nan ana cike da murna, Mairama na zaune a barandar can ana taya juna murna, gashi yanzu kwata-kwata babu ita, babu kuma wanda ya isa ya dawo da ita a doron k'asa. Wannan al'amarin ya raunata zuciyoyi da yawa.

Jahid yana nan daki an rufe shi, shi kansa yana buk'atar kad'aici, yana bukatar ya tabbatar wa kansa cewa ya rasa mai kusantarsa.
Haka aka ci gaba da zaman makoki har dare yayi aka watse.

Amira tuni an mayar da ita gida, Abakar yana asibiti sosai jininsa ya hau.
Tsawon sati ba a daina zuwa zaman makoki ba, Mairama tayi mutane wanda har ana zargi akwai mutan boye acikin masu zuwa.
Ranar da ta cika sati d'aya ne Jahid ya nemi da a nuna masa kabarin Mairama.
Da shi da Yaya Salis suka je wajen. Ya durkusa akan tarin k'asar dake a wajen ya sumbaceta.

"Kin tafi ko? Kin ji d'adi Mairama, da alamar kina cikin rahamar Ubangiji ko? Yanzu me kike yi Mairama? Na tabbata kina hira ne da kyakkyawar aikinki."
Ya murmusa tare da tattaro kasar ya zana fuskarsa da hawaye akai.

"Ki kalli yadda kika barni ni daya a wannan duniyar da babu abinda ta tara sai firgici da rud'ani. Mairam ki yafe min, Mairama ki yafe mun, Mairamah..."
Sai ya raunata, ya durkushe akan wajen yana kuka mai tab'a zuciya, wata iska mai sanyi yaji ta kad'a, a wajen, har saida zanen da yayi ya goge.
Ya murmusa har a k'asan zuciyarsa yace.

"To na daina kukan tun da ba kya so."

"YaJahid mana..."
Ya tunano sautin muryarta, shagwabarta, sanyinta da kuma yarinta da takan sanya acikin kalamanta.
Ya mik'e akan k'afafunsa, ya zuba hannayensa biyu acikin aljihunsa, ya karanto mata adu'o'i masu tarin yawa har sai da Salis ya nemi da su tafi.

Mama kam sai godiya domin kuwa Ubangiji ya bata dauriya sosai, Burinta d'aya, Mairama ta samu rahamar Ubangiji. Allah ya sada su a aljanna.
Jahid ya fito fili ya sanar da iyayensu ainahin abinda ya faru tsakaninsa da Mairama, ya dorawa kansa laifin tilastawa da yayi mata sanadiyar tana k'aunarsa. Aka jajanta lamarin, soyayyar Mairama ta k'ara ninkuwa a zukatansu, suka bita da addu'o'i.

Baba ya shiga hali maras fassaruwa, har yau ya kasa tsayar da zuciyarsa a wuri d'aya.

***
Tana tsaye akan doguwar bishiyar da ta yawaita da furrani da korayen sansami, dogayen fararen kayanta suka k'ara haskaka goshinta da kuma fuskarta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 27, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAIRAMAHWhere stories live. Discover now