3~Shafi na ukku.

512 59 1
                                        


Hankalina ya dugunzuma, na rasa ainahin amsar da zan bawa Baba, to taya ma zan bashi amsa bayan bai sanar dani abinda sakamakon gwajin ya sanar ba.
"Ba...ba!"

"Mairamah ciwon zuciya a cikin shekarunki na sha takwas? Ciwon zuciyar ma ba mai sauk'i ba duk akan Abubakar d'in?"

Na dafe kaina, tare da goge wasu hawaye masu zafi da suka ziraromin, sai yaushe Baba zai daina d'ora laifin 'ya'yansa akan wasu? Ni shine abinda yafi min ciwo fiye da ciwon da ya tabbata a zuciyata.

"Am Alhaji ka kwantar da hankalinka, wannan ba abun d'aga hankali bane muddin aka kiyaye k'a'idojin samuwar lafiyarta. Yanzu anjima bayan mintuna hamsin zaka iya dawowa dan yanzu akwai aikin gaggawar da zanyi."
Likitan ya tashi yana sauri ya zari farar rigarsa da wasu kayan aikinsa ya barmu a office din.
Banda kuka babu abinda nake yi kuma Baba bai lallasheni ba, kamar ma haushina yake ji.
Haka muka koma gida bayan mun tsaya an saye magungunan da aka rubuto min.
Sosai Mama ta tashi hankalinta, tayi min nasiha mai kashe zuciya da sanyaya jiki.
Bayan wasu dak'ik'u Baba ya koma asibiti suka gana da likitan duk da cewar ban san me suka tattauna ba.

Na dawo gida naci gaba da jinya, wannan karon Baba yana sassauta min har ya kan ce naje mak'ota nasha iska ko kuma ya d'aukeni a motarsa ya kaini gidan 'yan uwanmu.
Nayi kewar Amira sosai kasancewar ta koma birnin Katsina inda ta fara karatu a jami'ar UMYUK. Sadiya ma tana garin Sakkwato a jami'ar UDUS. Ni kad'ai ce ban samu jami'ar ba. Allah kenan!
Yanzu muna magana da Abakar ta hannun wayar makwabciyarmu, har haduwa muke dashi a bayan layi.
Kwasam! Baba ya kira agaggauce na shirya kayana ga baki d'aya ya samo mini Admission a Alqalam Uni. Nayi farin ciki sosai duk da har yanzu wani bangare na zuciyata yana matuk'ar son auren Abakar a gaggauce.

Dama na gaji da zama a Jibiya, dan haka a ranar na had'a komai nawa nayi sallama da Mamanmu, Yayanmu yazo d'aukata muka wuce ina mai cike da kewa.

Dawowata Katsina!
Daga nan ne zananniyar bak'ar k'adarar dake bibiyata ta fara bayyanuwa.
Yaya Jahid. K'anen mijin Gwaggo Saratu ne, Anan gidan yayansa yake zaune dan service da yake a garin Katsina da yake a Abuja yake zama. Tun ina J.s.s yake k'aunata, nima ina sonsa sai dai alokacin ban dauki cewar soyayya wata a bace mai daraja ba. Har saida soyayyar Abakar tayi tasiri a raina hakan yasa na manta da shafin Jahid a rayuwata, na d'auka cewa Abakar shi kad'ai ne Namijin da nake so kuma zan ci gaba da so, sai dai na k'aryata kaina lokacin da na d'auki soyayyar YayaJahid na dasa a zuciyata, da yake bayan so akwai shak'uwa da sabo a tsakaninmu, hakan yasa na fad'a tarkonsa a lokaci k'ank'ane.
Ina zaune a gidan Babanmu dake anan Katsina tare da matarsa d'aya, sai sauran yayyena maza da suke karatu a katsina duk suna gidan. Duk weekend idan Baba ya koma Jibiya na kanje gidan Gwaggo Saratu na zauna tare da yaranta su Kubra da Halima. Anan ne muke samun damar cin karen mu babu babbaka tare da Ya Jahid.
Na mato a sonshi. Irin son nan da yake mantar da soyayyar duk wani d'a namiji a ruhin 'ya mace. Matsala d'aya da muke samu wayewarsa tayi yawa, ya tab'a mace ba komai bane a wurinsa a cewar sa mu 'yan uwa ne wai, ah to wai kam! In banda abinsa me zai hada kifi da kaska?
Har wannan lokacin da yawa sun zo neman aurena Baba ya hana, 'yarsa boko zata yi. Hmm! Kuma ko sau d'aya bai tab'a neman jin ra'ayina ba akan wannan d'anyan hukuncin da yake yankewa.
Bayan mun yi hutu naje Jibiya, Abakar ya tashi hankalinsa sosai da yaga na canja masa, dama wayar da ya bani lokacin da zanje Katsina tuni na canja sabon layin da Jahid ne kad'ai zai kira ni. Wannan karon naji tausayin Abakar na bashi number da zai sameni bayan na jibga masa k'aryar cewa wayar aka sace. Bai barni ba har saida ya bani kud'in wata wayar wai idan naje katsina na saye kuma kudin dubu biyar ne, sai naji ya bani haushi na raina kud'in sosai.
Na bawa Mama dubu ukku aciki na sayawa Jahid agogon dubu biyu da na koma hutu na bashi.
Ba laifi muna waya da Abakar kullum yana k'ok'ari wajen ganin na gamsu da k'aunarsa.

Wata ranar asabar naje gidan Gwaggo zan yi kwana biyu.
Ranar lahadi da safe duka gidan aka tashi da jimamin rasuwar wani abokin mijin Gwaggo, dan haka suka shirya ga baki d'aya zasu tafi dama Halima bata nan tana gidan Babbar yayarsu sai maraice zata dawo. Ni kuma nace ba zan bisu ba kwana zanyi.
Na rufe ko ina a gidan na shige d'akin Halima nayi baccina, sai sha d'aya da rabi na tashi. Nayi wanka na fito d'aure da k'aramin towel sanin cewa babu kowa a gidan. Na sanya hijab dina a sama na wuce kitchen na debo abinci na dawo falo na zauna ina ci.
Sanyayyiyar sallamarsa ta doki kunne na yana tsaye abakin k'ofa rik'e da wasu takardu.
Na murmusa na gaidashi ina ta k'okarin rufe jikina, ya dawo kan kujerar da nake ya zauna.

"Iyye yarinyar nan kinga wani shek'i da kike yi kuwa?"
Nayi dariya tare da jefa masa harar wasa. Na ture filet din abincin nasha ruwa tare da mikewa a muzance nace.

"Ya Jahid bari inzo."
Ya rik'o hannuna yace.
"Ina zaki? Dan Allah ki zauna muyi hira."

"Ai zan dawo kaya zan saka yanzu nayi wanka."
Har kamar zai sake hannuna sai kuma yayi kokarin daga hijab dina yana dariya, nayi saurin rike hijab din ina hade fuska.
"Zo nan my love."
Ya jawo ni da k'arfi na fad'a jikinsa. Da azama nayi k'okarin mik'ewa amma sai naji towel d'in jikina ya subule zuwa k'asa. Da sauri na jawo towel din ina k'ok'arin daurawa.
Hanzarina ya katse lokacin da naji hannun ya Jahid akan k'irjina wai zai d'auramin towel d'in.

"Nidai ya ka bari kada Gwaggo su dawo dan Allah..."
A firgice na dago jin salam...

Ku d'an jirani zan zo...

MAIRAMAHOnde histórias criam vida. Descubra agora