6~Shafi na Shida.

457 69 8
                                    

Wannan rayuwar muka ci gaba da gabatarwa acikin sati biyu da suka shud'e na zamana a gidan.
Ranar da zan koma gida,nayi wanka na cikin doguwar riga ina ta murna zan tafi gida, na same ya Jahid a d'akinsa yana bacci, na haye kan katifarsa ina tashinsa ta hanyar bubbuga k'afarsa.

"Yaya wake up, Gwaggo tace kazo ka kaini."
Ya juyo ba tare da ya bud'e idanunsa ba ya murmusa tare da jawoni na fad'a ajikinsa.

"Yanzu tafiya zaki yi ki barni? Dan Allah kiyi zaman ki nan gidan mana."
Nayi k'ok'arin turesa nace.
"Gida zan tafi, nidai sake ni dan Allah."

Yayi k'ok'arin had'e gab'ob'inmu amma nak'i bayar da had'in kai.

"Ashe har yanzu bakya sona? Shikenan ki tashi na kaiki."
Ya had'e ransa tamkar an sanar dashi mutuwa.
Ya mik'e da zummar shiga bayi, ashe ko guntun wando babu ajikinsa.
Wannan giyar ce ta jani har rungumesa ta baya ina hawaye.

"Dan Allah ka daina cewa hakan, walla ni ina matukar k'aunarka Jahid amma kai kana amfani da tsananin son da nake maka kana cutar da rayuwata, ka barni na kusanci Ubangijina Jahid, ka barni na daina aikata zunubi, ka barni koda ubangiji na zai daina fushi dani."
Na fashe da matsanacin kuka ina jin ciwon ayyukan da muka dulmuya muna aikatawa.
Ya juyo ya sanya ni acikin rik'onsa.

"Haba Baby wallahi bamu taba aikata Zina ba. Kuma nayi miki alk'awarin ba zamu tab'a yin haka ba."

"Duk Kansu zunubbaine masu cinye lada tamkar yadda wuta take cin kara. Dan Allah muyi hakuri mu same baba yayi mana aure kawai."

Ya gogemin hawayena kana ya zaunar dani akan gadon yana cewa.

"Shikenan, nayi miki alk'awari gobe zan yiwa Yaya magana sai ya same Babanku. Kuma daga wannan ba zan koma ko rika hannunki ba har sai an d'aura aurenmu."

Sai naji raina yayi sanyi kad'an, ni kaina ina son kasancewa dashi amma bata wannan hanyar ba.
Nan na bayar da kai bori ya hau. Muka yi tamkar yadda muka saba har ila yau bamu aikata zina ba.
Dama ance, Shi zunubin da ya danganci zina. Lokacin da ake yinsa zaka samu nishad'i da nutsuwar gabb'an jiki. Bayan kammala, sai wad'an can abubuwa biyu su gagareka. Hakan ya ke kasancewa dani aduk sa'ada muka kammala ta'asar mu. Na kanji duniya tayi min zafi har sai nayi alk'awarin rashin sakewa sannan nake samun salama a k'asan ruhina.

Bayan komawa gida naci gaba da mayar da hankalina akan karatu.
Duk lokacin da Jahid yazo gidanmu na tambayesa maganar aurenmu, ya kance mu jira lokaci tamkar yadda Babanmu ya sanar dashi.

Jahid ya kwanta ciwo na tsawon sati biyu, kana ya mik'e akan k'afafunsa duk da cewar ya matuk'ar galabaita, yaci gaba da ramewa ba tare da dalili kwakkwara ba har na tsawon lokaci, aduk sa'adda na tambayesa sai dai ya kawar da kai yace.
"Mairama Aure nake so. Aure nake so amma babu hali."
Wad'ancan kalaman sukan narkar dani su dulmuyar dani irin duniyarsa na lokaci. Nima auren nake so.
Jahid yayi tafiya Abuja. Ya rage zama a Katsina sosai idan yazo ba zai fi kwana biyu ba yake komawa. Ni na sani akwai wani abu da yake damuwarsa bayan wancan.

Wata d'aya, wata biyu, wata ukku, banga jinin al'ada ba.
Ana wata ga wata. Sai na bi na damu kaina, zuciyata tana ci gaba da tsinkewa. Na rame kwarai kullum cikin ciwo nake. Da yake ance ba a sanin murnar karen da bashi da wutsiya, a gidan babu wanda ya fahimci hakan.
Ranar da abin yafi k'arfina na kira Amira na ce tazo gidanmu.

"Kai haba Mairama kema wallahi kin bani kunya, to yanzu meye marabarki da Sadiya? Duk sunanku d'aya masu bawa maza jikunkunansu sabida soyayya ta rufe idanunku... Kuna tsoron fushinsu amma bakwa tsoron na ubangiji ko? Ki dubi yadda kika dawo kamar ba Mairama nutsatstsiya ba."
Hawaye suka zubo min, na aminta da zantukan Amira, na fice daga cikin jerin nutsatstsi.

"Amira, shin ya zamu yi wallahi tun April ban sake ganin period d'ina ba, har yanzu."

Amira tayi shiru gabanin tace.

"Bari in kira wata Sis d'ina muji."

Nan Amira ta kira wata likita yar uwarta tayi mata bayani, muka tabbatar wa da likitar ban tab'a aure ba kuma ni budurwa ce.

"Yanzu sai muje a saye maganin infection d'in ko muje asibiti a dubaki tun da ita bata gari bale muje asibitinsu."

Sam! Hankalina bai kwanta da hakan ba, amma dole zan aminta da Infection din ne yayi mugun kamu tamkar yadda tace.

Na fito da sunan muje asibiti Baba ya hanani fita, hakan yasa ran Amira ya b'ace ta wucewarta ba tare da ta kara bi ta kaina ba.

Tsawon sati ina neman hanyar magana da Amira ban samu ba, naci gaba da zama cikin jimami da bugun zuciya, ciwukana suka raunata.
Da na rasa hanya dole na je inda makwabciyarmu na tuntub'eta.

"Mairama ai wannan dole babanki yaji, bari in ya shigo gidanku na same shi sai a kaiki asibiti."
Nayi mata godiya na koma gida.
Haka ko akayi ta sanar da babanmu ya amince muje asibiti da safe.

Jiya kun jini shiru ko? Nayi celebrating birthday dina shi yasa hidima tayi min yawa ban samu yi muku update.
Ina zuwa ku jira ni...

,

MAIRAMAHWhere stories live. Discover now