SO FARUWA YAKE 001

6.7K 237 3
                                    


💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
🎀🎀🎀
🎀🎀
💝💝
💝 *love just happens*👌🏻

🐄 *Real hausa fulani writer's forum*

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

بسم الله الرحمان الرحيم اللهم صل وسلم وبارك على سيدنا محمداً وآله

الحمد لله dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, daya bani ikon fara wannan littafi ina rokon ubangiji ya bani ikon kammalawa,, kamar yadda na fara

ina godiya ga eruwa, dats sister from another mother, my mentor, my dearest nd deepest friend my my my,, my din sunada yawa but all i can say is *thank you my deejehlurv*
Actually dis novel is her idea but she gives it all to me nd tell me not to mention her name but i hav to,,
thanks once again
the novel is all urs not mine😉
i ❤ u dear

ina neman afuwar ku masoya na, jina shiru da kukayi na part 2 din *soyayyar Asmad* da *Aklaaqin nafs* dukka ban manta ba
*kece sila* ma na dan dakatar dashi in nayi nisa a wannan se na fara turo shi
ku dai ku tayani da addu'a Allah ya amfanar damu abinda ke ciki y yafe kurakuren da nayi da wanda zanyi walau na sani ko ban saniba

*001*

*********
*Makarantar secondary ta mata dake qauyen Garki a jigawa*

kamar yadda kowanne dalibi dan aji shida na secondary wato ss3 yake shiri haka nima nake nawa shirin dan yin bankwana da kawaye duk kuwa da ba qawayen gareni ba,,
fuskata kadai mutum ze kalla ya gane irin tsantsar farincikin da nake ciki, bakomai ke sakani farinciki ba se idan na tuna inna ta yau zanje na ganta,,

kauyen *danladi* wanda ke cikin garin jigawa
kauye ne dan qarami wanda babu nisa da garin gumel cikin jihar jigawa,,gidajen kasa ne a kauyen dukda akwai ginin bulo amma befi gida hudu ba kwata kwata a kauyen,, kuma gidajen bulo na masu hali ne,ko na wadanda suke birni..

yamma ce likis yawanci a wannan lokacin masu gashin_nama sun fito da masu sana'o'i, haka manya wadanda suke zaman banza zaman kashe wando sunfi fitowa a wannan lokaci dan zaman majalisa

a hankali na nufi cikin gidan namu wanda shima yake cikin sahun ginin qasa,,,
gidanmu irin gidan qauyene babba
babu siminti kuma akwai kewayen dabbobi, kamar dai yadda gidajen kauye suke.

da sallama na shiga cikin dan karamin soron gidan wanda ya sadani da babban tsakar gidan namu banko kalli ko ina ba nayi hannun dama wanda ya sadani da kewayen mu,,
innata na hango a zaune a bakin rijiyar tana wanke kwanuka,, na dire kayan hannuna da hanzari tare da qarasawa gunta da sauri na fada jikinta,,
itama riqeni tayi dan ta gane nidin ce
tana fadin,"oyoyo deejeh," kana ganin yadda muke kasan munyi kewar juna,,
sakina tayi tana fadin, jeki kai kayan naki daki,, ba musu na dagata nima tareda qarasawa gun kayan nawa, na wuce cikin wani dakin kasar wanda seda na rankwafa sannan na shiga,
naja kayana ciki,, tsaf na samu dakin wanda duk hutu dama in zan dawo haka nake samunshi, saboda yadda innata take kula da duk wasu abubuwa nawa
na kai kayana ciki tareda fitowa na taya innata ayyukan da bata qarasa,,tana hanani amma naqiya

karfe 8 na dare
dukka en mata da samari suna dandali banda ni da nake jikin innata muna hirar yaushe rabo,, a hankali na dago, nace
"inna wai ya naji gidan shiru ne tunda na dawo ko bakowa ne, ina su baba kaltume?"
er kwafa inna tayi
"yo ai kaltume da yaranta harda babanku sun tafi gumel wai cin kasuwa"
da sauri na dan dago
"gumel kuma inna?, cin kasuwa fa kikace inna"
eh nidai cemin sukayi yau zasu dawo shiyasa ma ban dora girki ba gudun kar a zo ran kowa ya baci tunda ba girki na bane"
wannan wacce irin rayuwa ce, yanxu suka tafi suka bar inna ba ko abinda zataci saboda rashin galihu da rashin sanin darajarta, kuma basu bar mata komai ba ita kaltume ta kwashe yaranta dukka sun tafi ita kuma inna ko oho kenan
ya Allah ka azurtani ko nida innata ma dena ganin wannan wulaqanci da fifiko
sauke numfashi nayi sanda na kai nan a addua ta nace ameen ni kadai a raina a fili kuma nace

"toni inna ai yunwa nakeji yanxu"
ban qarasa rufe bakina ba mukaji sallamar wani yaro a soro, wai ana sallama da deejeh
miqewa nayi tareda fadada murmushin fuskata dan nasan mutum daya ne zeyi sallama dani,
na gyara fuskata da er qodaddiyar atamfar dake jikina dukda kayana sun kode amma ba kazanta ko kadan na dakko hijabina har qasa na sanya nayiwa inna sallama na fito.
a qwar gida na sameshi,, ya sakarmin murmushi nima na maida mai
na tsugunna har qasa na gaida shi,,
"deejeh na kin dawo lpia?" ya fada cikin farinciki,,
nan muka soma hirar yaushe rabo, tareda hirar turo manyanshi da zeyi kamar yadda muka tsara tunda na gama karatuna,,
mun kammala hirar zan wuce ya miqomin ledar, cike da kunya na miqa hannu dan na amsa duk da banso na karba sedai hamza ya wuce haka a gurina,
ya riqe nima na miqa hannu zan amsa,, mukaji murya a tsakar kanmu da hayaniya
"eh lallai karuwanci da amsar abin samari har a qofar gidana,daga dawowarki?... kodayake ai gara ki nunawa duniya kin dawo, shikkenan bakina ze soma ciwo"
muryar abbah na ya cikamin dodon kunne tare da baba kaltume da yaranta kusan su biyar dukkansu tsaye,
ji nayi hawaye na ambaliya a fuskata, banko tsaya karba ba na maida hannuna tareda yin cikin gida dan qunar da raina kemin
da gudu na wuce kewayen mu na fada jikin inna ina kuka me tsuma rai,, nan ta shiga bubbuga bayana a hankali cikin sigar lallashi,, tana murzamin hannu alamun nayi haquri
ajiyar zuciya na fara saukewa dan duk bakincikin da nike ciki haka inna kemin nan da nan se naji zuciyata tamin sanyi, ko ba komai kwanaki kadan suka ragemin nima cikin gidan, zan tafi na rabu da shan wannan wulaqanci. nasan hamza ze turo magabatanshi ne nima nayi aure na huta

muryar abbah ta katse ni wanda ko sallama beba ya shigo se bambami yake, ji nayi yana fadin to kice ya turo dan kowa ma ya huta nima na gaji,,
na danji dadi,,
a tsakar gida suka shimfida qatuwar tabarma, suka baje su kilishi, fura da nono kasancewar gumel ana samun fura da nono masu kyau,, haka suka baje ita da yaranta
muna hangosu a dan tsakar gidan dake kewayen mu, saboda katangar data kewayemu ta fadi se saura kadan hakan yasa duk abinda akeyi a tsakar gida muna hangowa suma suna hango abinda mukeyi a namu dan qaramin kewayen da aka waremu...

seda suka cinye tas sannan baba kaltume ta daga murya yadda tasan sarai zamuji tace
"laaa me gida kaga mun cinye komai,, gashi kuma bamu tsakurarwa su deejeh ba,,"
budar bakin abbah se cewa yayi
"yo haka kwa akayi,, to miqa musu wannan sauran furar"
bako kunya kaltume tace
"bishira ungo kaiwa su deejeh"
wacce aka cewa bishira wacce bazata wuce shekaruna ba wato 18 ta taso se karairaya take tazo ta dire gayan fura kwalli biyu cikin wani murfin kwanon sha,,
ba um ba umm umm tayi gaba
nida inna muka bita da ido
wannan furar kwalli biyu mukaci naci daya inna taci daya,
muka sha ruwa,,
bayan mun gabatar da shafa'i da wutirinmu ne muka kwanta,,

yau da farinciki na tashi domin kuwa girkin innar mu ne,,
tunda safe inna ta tashi muka gyara bagaren namu tsaf, aka dora sanwar abincin safe,
haka aka kammala komai cikin farinciki dan har yaran gidanma suna murna idan girkin inna ta ne dukda basonta suke ba amma sunsan tafi kaltume iya girki

muna zaune kan abin kaba muna shan hantsi, mukaji sallama
inna ta amsa cike da farinciki dan ta gane muryarta,,
salamatu ta shigo inna na lale marhaban
na gaida baba salamatu daganan na shige daki,,
nan fa sukayi ta hira kasancewar salamatu bata fiya zama a d'anladi ba,, a kano tafi zama
cike da tausayawa ta kalli inna tace
"haba asabe, dubi yarinyar nan dan Allah ji kayan dake jikinta se kace mara galihu,, ita kadai a gidan nan ta fita zakka daga sauran yaran dukkansu suturunsu masu kyau banda nata"
"haba salamatu kema ai kinsan halin da muke ciki,, itama an kusa bikinta kinga duk se mu huta"
"amma ke kinada kudin da zakiyi mata kayan daki ne?"
"Allah ze kawo salamatu"
"to nazo miki da shawara"
salamatu ta fada
"meze hana ki bani ita na kaita birni ta dinga yin aikatau kafin lokacin bikin nata kinga se ta samu sosai,"
tun bata kai karshen zacen ba
inna ta katse ta
"ya isa salamatu, wannan ma ba magana bace, gaskiya babu inda zan kai diyata, kedai kawai ki kyale"
ganin inna ta dau zafi yasa salamatu sakkowa
"yi haquri asabe"
jin haka yasa inna ita ma sakkowa tace
"kiyi haquri salamatu, bawai dan ban yarda dake bane, kema kin san duk garin nan kece kadai wacce muke mutunci da ita, wlhy na yarda dake, amma ki sani ni mahaifiya ce bazan iya bada dije ba har zuwa birni inda batasan kowa ba kuma tana aiki, na sani Allah ne mai karewa amma shima yace tashi na temake ka, ni yanxu auren dije ne a gabana, nima hankalina zefi kwanciya na aurar da ita kuma itama ai bazataji dadi ba taji ni da kaina na dauketa na kaita birni saboda bidar kudi, kiyi haquri mu bar wannan maganar kawai"
"shikkenan asabe wlhy bakomai, na fuskance ki"
dukka wannan hirar da su inna sukeyi ina jinsu,
naji dadi sosai yadda inna ta bawa salamatu amsa, na sani inna bazata taba bari nayi nisa da ita ba, nima kuma baso nake ba

sallamr wani yaro ta katseni yana fadin, abani daddawa,
na miqe na kaimai daddawar tareda amsar kudin....

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now