So faruwa yake 34,35 &36

2.4K 105 0
                                    

[12/18/2018, 11:38 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *034*

sabon babin shagwa6a khadija ta budewa safwan tunda taga tanada cikin nan,, gashi kuma yana sakata kasala, har makaranta tare suke zuwa yanxu se yaga ta shiga class sannan zai kyaleta,
sanda safwan ya sanarwa su alhaji malam, karkaso kaga murna a tattare da alhaji malam, ba karamin dadi yaji ba, abin yayi mai dadi sosai, ummi kuwa tafi kowa bakincikin wannan abu ita wai kamar ita ta hada zuri'a da er aiki, wannan abu yafi komai 6ata mata rai, duk yadda takeji da safwan dinta yadda en mata ke sonshi da hauka a kanshi, har yanxu ummi ta kasa gano kyawawan halayen khadija wanda yaja ra'ayin safwan,

shirye shiryen dawowa nija sukeyi dansu khadija sun sami hutu kuma yaje checkup dinshi na wannan watan, kullum safwan na manne da khadijanshi tun bataso har ta rabu dashi seyace shi gun babynshi yazo, sedai akwai abinda ke damun safwan saboda yadda suke da khadija yanxu yanaso yaji cewar ta amshi soyayyarshi, dan gaskiya yana bukatar matarshi yanxu, shi abinma har mamaki yake bashi yadda yake hidimtawa wata mace bayan shine en mata kebi, yau shi mace ke wulaqantawa tana ja mai aji, ko iya wannan ma ya isa ya nuna mai bambancin khadija da sauran mata irin su arfa dukda itama arfan yanxune ta zama haka...

a bangaren su umma kuwa su oga sun dawo dan har sun bincika mata inda khadija take kuma sun tabbatr mata tana india amma sun kusan dawowa nija, dan oga ba karamin shu'umi bane yana hulda da mutane daban daban duk inda kake a fadin duniya seya nemoka danshi a gurinshi ba qaramin aikinshi bane, a takaice ma yasan cewar khadija tanada ciki amma be sanarwa su umma ba danshi a ganinshi ba abune da suka tambaya ba kuma beda muhimmanci tunda baya cikin aikinshi,, yanxu su umma jira kawai suke khadija ta dawo,

khadija kuma a nata bangaren tunani yana addabarta, gashi ita ba uwa ba, batada kowa da zataje ya bata shawara, zuciyarta tana fadamata tana qaunar safwan sedai ta kasa amsa hakan kome yasa?  oho mata,,, tunda zancen cikin nan ya fara, yadda suke da safwan yake sakata qara sonshi sosai amma hankalinta yaqi kwanciya data amince mai, wannan tunani kan dagula mata lissafi (nikuwa a ganina ba abune mai wahala ba sedai kuma me karatu in ya duba ta fuskar khadija da yadda take bata da wani experience kan zamantakewa tunda ta taso ne a qauye kuma batada qawaye so zata dinga gani kamar safwan ze cutar da ita ne saboda abubuwan da suka dinga faruwa, wanda yaci ace ta gane daze cutar da ita da tuni yayi,,)

sun shirya tsaf sun fito, safwan dama yayi sallama da dr. wajen 12 na rana suka iso garin kano, duk zuwan da khadija zatayi kano setaji dadi sedai wannan karan ta kasa gane meyasa takejin wani bakon lamari a tattare da ita kamar bata farincikin sauka,,  driver ne yazo daukarsu dan alhaji malam baya qasar ma, amma yayiwa driver bayanin komai, gidan ummi straight suka wuce, a falour suka tarad da ita ta dora kafa daya kan daya tana karkada qafa, tasha adonta cikin brown less me kyau tana kallon tv din, sallamarsu tasa ta dan juya tana kallon qofar da suke shigowa, ko kallon arziki basu samu ba dan ita har safwan dinma haushi yake bata ko kanme ze wani yi ma khadija ciki, duk haushinshi takeji,, yanayin yadda sukaga ummi yasa kowa yasha jinin jikinshi ba kamar khadija ma,, zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa, da kyar ta amsa da lpia sannan ta miqe, "kazo ka sameni a sama"  ta fada ta wuce abinta, kallon juna sukayi shida khadija, seda khadija tace ka tashi ka tafi mana, kmar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya miqe jiki a sanyaye yana fargabar abinda zeje ya tarar, khadija ma ta tsorata, ta samu guri ta zauna kan kujerar tayi shiru, kawai se wayarta ta soma qara dayake ta saka layin nija dinta, number hafsat tayi appearing kan screen din da murna ta dauka dan tama manta ta,,
sallama sukayiwa juna suka amsa
"kin manta dani khadija ina kika shiga ne haka daga zuwa india an nemeki an rasa" dan murmusawa khadija tayi "haba kawata ya zakice haka kinga yau dinne ko 1 hr bamuyi da sauka ba" "ayya toya gari ya jin dadi"
"Alhamdulillah" khadija ta fada, se suka fara hirar school inda khadija ke sanar mata ai harta fara wata a india ma, daga karshe suka rufe hirar da in hafsat ta samu lokaci zatazo..

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now