So faruwa yake 28, 29 &30

2.7K 106 0
                                    

[12/18/2018, 11:34 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

*this page is for u readers thanks for the comments❤💌*

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *028*

kayan hannunta ne suka b'are saboda gigicewa, ta shigo dakin da sauri, a kwance ta ganta ta qaraso da gudu, "safwan me ya samu innata, safwan ka fadamin dan Allah" seta juya gun inna a gigice, inna tashi mana wacce irin kwanciya ce wannan, ki tashi inna alhaji malam ne ya riqo deejeh "yi shiru ya isa haka" yana lallashi,
kukan deejeh ne ya jawo hankalin mutane su kaltume sukayo bakin qofar, alhaji malam ya fita dan azo ayiwa inna sutura
kuka take me tsanani har da gunji, ta saka gawar inna a gaba gabadaya ta fita a hayyacinta, safwan shima hawayen yake,

anyiwa inna wanka an shiryata tsaf cikin likkafaninta duk wannan abin da ake baban bushira baya nan.

(kuyi haquri fans nasan bakuso inna ta mutu amma ya zanyi da alqalamina, kuma haka labarin yazo🙏)😭

mutuwa kenan, Allah baya barin wani dan wani in lokaci yayi dole a tafi, kuka kuwa khadija tasha yanxu ko uffan bata iya fada saboda shock din data shiga sedai tayita bin mutane da kallo, su kaltume kuwa duniya sabuwa,,

duk maganar da safwan zeyiwa khadija bata tanka shi sedai ta tsaya kamar wata lifeless statue, anyi sadakar uku, acikin kwana ukun nan khadija ta koma wata iri, abinci se an takurata ko safwan yayi mata hirar inna da nasihun in bataci ba ya inna zataji? da kyar takeci, safwan da alhaji malam ne keta hidindimu, koda mijin inna yaji labarin ma be wani damu ba yace Allah ya jikanta kawai,

shirya kaya yake cikin jakar dama kayan khadija a jaka suke, kayan inna kuma tace seta tafi dasu dukda en tsummokara ne haka ya shirya mata su,, khadija tasan ba amfanin zamanta a gidan amma ta qudire a ranta daukawa innarta fansa kansu kaltume kunsan fishin me haquri,

mota suka hau se kano ta dabo tumbin giwa koda me kazo an fika, ba dadewa se gasu a kano, gidan alhaji malam sukaje deejeh duk a hargitse take safwan kam yaji jiki sosai gashi jibi ne checkup dinshi na qarshe a watan farko wanda dagashi kuma se sati sati ze dinga zuwa inma ba matsala se sati biyu biyu,  suna shiga safwan ya zube kan gado se bacci, khadija kuwa innarta ce kawai a ranta, "Allah ya jikanki inna, Allah ya miki rahama" se hawaye suka dan zubo mata wani sabon kukan ne yazo mata se tayi bandaki da gudu, kuka tayi sosai, har gani take biyu biyu, nan ta cire kayanta ta watsa ruwa ta sauya wasu...
zama tayi bakin gadon ta rike kanta saboda azabar ciwo, duk rayuwar ma ta fita a kanta, memories dinta tareda inna sukayita dawo mata, yanxu shikkenan babuni babu inna wannan abu na tayar mata da hankali ashe kuka take mara sauti bata sani ba, ji tayi ya janyota jikinshi sosai yana lallashi, tayi luf a jikinshi suna jin bugun zuciyar juna, bayanta yake shafawa a hankali alamar rarrashi, har bacci ya dauketa nan ya kwantr da ita shikuma ya miqe.. abinci ya samo musu, ya dawo ya tarar tana baccin dan haka ya ajiye

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now