So faruwa yake 40, 41 & 42

2.6K 99 1
                                    

[12/18/2018, 11:43 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *040*

safwan na zaune a bakin gadon, Abban khadija yana kwance kamar koyaushe idanuwanshi a bude yana kallon safwan, safwan ya bude littafin yana kallon abban khadija yau zan karanto maka wannan yadda ze debe maka kewa kaji dadi nima dama inaso na karanta naji,,
seya bude littafin shidai Abbah yana kallonshi ne kawai, daga inda suka tsaya ya cigaba

Mahaifinki shahararren dan kasuwa ne, me harkokin gold sunanshi Alhaji muhammad muhammad fari, yanada enuwa guda biyu sedai ba uwa daya uba daya suke ba, shi mahaifinki mamanshi daban suma mamansu daban, (da kawu da umma kenan), mahaifinki mutum ne mai son zumunci, hakan yasa ya gina katon gida na gabadaya shida en uwanshi lokacin ma iyayenshi suna raye suma duk anan suke zaune, munyi auren soyayya da mahaifinki, sedai Allah be bamu haihuwa ba kusan shekaru biyar da auren, mahaifinki be damu ba yace haihuwa ta Allah ce nina fishi damuwa, dan mutum ne mai kawaici, da fawwalawa Allah lamuranshi, saida muka shekara 8 da aure sannan na samu cikinki, alokacin ma har na fidda rai, sanda muka gane munyi murna sosai, kashegarin ranar ne mahaifinki yayi hatsari akace ko gawarshi ma bazata ganu ba, nasha kuka na gode Allah, daganan kuma se enuwa suka fara maganar rabon gado ni banma sani ba, se kawai cemin akayi ana nemana a court, a nan nake sanar dasu aini inada ciki fa, a yadda na lura maganata tayi musu d'aci dole aka daga rabon gadon har zuwa sanda zan haihu, tun daga wannan ranar aka fara farautar rayuwata data jaririna, sedai akwai tsaro sosai da nake dashi, musamman danake likita wacce qasa ke ji da ita, hakan yasa ake tsarona sosai, sedai na saka a raina idan na haihu zan tafi qasata tunda banida enuwa a wato Niger,,,

shigowar dr. ya katsewa safwan karatun dayakeyi wanda kadanne ma ya rage ya qarasa karanta abinda ke littafin, wanda duk deejeh akaso ta karanta, duddubashi dr. yayi sannan yayi hamdala saboda ganin yadda ake samu progress sosai a jikin nashi.

After 3 month,

Abba yanxu yana magana sedai be cika surutu ba, yana jin dadin yadda safwan ke debe mai kewa, har yanxu ba'a saki su umma ba, dan alhaji malam yace har sai abbah ya yarda tukunna, abbah yanxu da sanda yake tafiya, jiki fa yayi kam gaskiya sosai,,
jira kawai ake ya ware sosai,

diyar khadija tana wata na shida kenan, itakuma khadija tana kan karatunta na nursing har yanxu batayi regaining memory dinta ba,, dr. ya kawowa khadija me kula mata da suhaimat in zataje school tunda karatun nasu babu wata tsawwalawa ba irin na nija ba, kuma mostly se dare take karatunta,

yau khadija ta gama shirinta cikin wasu en kanti ta yafa gyalenta ta mai sallama driver ya jata, tana class a zaune malamin da alama bazezo ba duk jiranshi da sukayi, dan tsaki tayi, da batayi tashin wuri ba, miqewa tayi zata fita, se taji wata na waya "hlo kubrah" se khadija taji kanta ya wani juya, kubrah ta fadi sunan tana maimaitawa kamar lokacin ta faraji, akwai wani abu gameda sunan datakeson tunawa, kubrah ta qara maimaitawa har ta fice tanason tuno wani abu amma ta kasa sedai jikinta yana bata koma mene to ya shafi rayuwarta ta baya,,

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now