So faruwa yake 10,11&12

2.9K 121 1
                                    

[12/18/2018, 11:07 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *010*

kamar yadda gwaggo ta fada hakan nagani dan kuwa arfa ba qaramar karbuwa ta samu gun alhaji malam ba,, sedai ita batayin shigar banza kamar sauran yara, kusan kayanta dukka doguwar rigane.
Arfa yarinya ce me haske amma bata da kyau sosai,,tanada dan tsayi daidai gwargwado amma bata da structure kwata kwata,,

tare sukaci abincin dukkansu,, suka koma falour sunata hirar yaushe rabo, kuma harda alhaji malam acikin hirar.. sedai abinda safwan ya lura se wani shisshige mai take amma se be kawo komai ba,

yau kwanan arfa biyu a gidan,, suna zaune a falour itada safwan, a lokacin dare yayi dan har 10 ta kusa, ummi da Alhaji malam suna sama,,
wani film suke kalla suna hira sama sama.. arfa ta dawo kujerar da safwan yake,,  "wai ni dan uwa se yaushe zamu aurar da kaine ko se ka zama tuzuru"
a lokacin tana sanye da wasu kayan bacci ne amma ba shara shara ba irin masu santsin nan kuma ta dan yafa gyale
be juyo ba yana kallan tv din, yace
"se sanda kika shirya"
"to aini na shirya fa tun tuni dama kaine bakaso tun sanda Alhaji malam ke maka maganar se kayita dodging" to nima yanxu na shirya
ya fada still hankalinshi na kan tv din,,
arfa tayi dan murmushi "yeeee to se ka fadawa su Alhaji malam,
to shikkenan,,,
se kuma ta qara matso shi sosai har yanajin numfashinta itama tanajin nashi,, shidai har lokacin be juyoba dan hankalinshi nakan tv din,,
se kuma arfa ta soma shafar jikinshi,,, da mamaki safwan ya dauke idonshi daga kan tv din yana kallonta, ta kashe mai ido daya tareda fadawa jikinshi...
ta soma yi mai wasu salo,, nan fa safwan ya gane inda ta dosa,, se ya dan dagota
"mene haka er uwa?" ya fada voice dinshi na dan cracking saboda yadda take so ta rikita shi
arfa tace
"wannan ai normal ne aure fa zamuyi" ai safwan na jin haka se ya yakiceta daga jikinshi ya miqe
"wacce irin rayuwa kika saka kanki haka arfa nasan da ba haka kike ba wats wrong with u? to ki sani ni bana auren mace mara class,"
yana kaiwa nan yayi gaba da azama arfa ta bishi,, pls safwan ka gane mana ya kamata ka waye mene a ciki?,,
yana kaiwa qofar dakinshi yayi banging tareda saka key,,

yabar arfa a waje tana mamaki,, ko kadan bata taba zaton ustazancin safwan ya kai haka ba,, gosh ta fada tana rike goshinta
komawa nata dakin tayi
ta zauna jiki a sanyaye "yanxu ya zanyi,, dan nasan safwan cewa zeyi baze aureni ba anymore.. ohh noo"

tun daga wannan ranar safwan ya dena sakin jiki da arfa dan yaga kirikiri so take ta jefashi halaka, yau kwana biyu kenan da faruwar abin
safwan na zaune a falourn shi arfa ta shigo da sallama,,
ya amsa mata saboda darajar sallama da kuma sanin wajibi ne amsawar,, ta matso kan kujerar da yake zaune itakuma ta zauna a qasa,
"kayi haquri dan uwa sharrin shaidan ne bazan qara ba wlhy na maka alqawari" safwan ya daure fuska nan ta shiga mai dadin baki daga karshe ya haqura dan sun shaqu da arfah
se hira kuma ta barke yayi ta mata nasihu kan abinda take ba daidai bane ko kadan a musulunce..
kamar mutuniyar kirki ta dinga narkewa tana mai shagwaba tayi kamar ta ji wa'azin dayake mata..
har suna hirar zuwa gobe ze fadawa Alhaji malam kan maganar aurensu,, nan fa suka yi hirarsu irin ta masoya me cike da tsafta dan safwan akwai addini,,
bayan dan lokaci sukayi sallama ya soma shiri dan akwai inda zeje. itama ta koma dakinta dan ko breakfast batayi ba,, qarfe 1:15 kowa yana nashi sallar azahar din haka Arfa ma tayi nata yayinda ita kuma deejeh take fashin sallah,,

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now