So faruwa yake 17&18

2.1K 99 0
                                    

[12/18/2018, 11:24 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

realhausafulaniwriters@gmail.com

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *017*

baya yayi itama ta dan ja baya tana tasbihi,, se suka gaisa cikin mutunci amma ya karanto damuwa a fuskarta ya wuce itakuma ta fice, tana gunsu gwaggo suna hira sama2 taji an kirata,, ta qarasa falourn nan ta tadda mukarram da safwan,
"qaraso mana amaryar" mukarram ya fada cikin sigar zolaya,
"alhaji malam yace ki bani takardun account din dayace kiyi filling ba musu na mike na wuce daki na dade ina nema saboda suna cikin kaya,, na dakko na fito na tarar har mukarram ya miqe ze wuce
na qaraso inda yake nace
"sedai fa kuma ban saka phone number ba dan banida waya da kuma wasu en abubuwa da ba'a rasa ba" ba matsala ya karba yayi waje dan naga kamar sauri yake..
waje nayi ban kalleshi ba shima din be waiwaye ni ba,

dare yayi har qarfe 10 nayi ta maza na wuce bangaren dan bacci nikeji, na shiga da sallama, ganin baya falour yasa nayi hamdala,, dakin na shiga naga baya nan ma, babu bata lokaci nayi shower na shirya cikin kayan bacci na dora hijab akai na nemi guri nayi kwanciyata,, har bacci ya daukeni bai shigo ba, ashe yana can gun ummi suna tattaunawa kan wasu businesses dinshi da yake so mukarram ya rika mai, yana neman shawararta,

da asuba na farka na tarar yana alwala,, ya fice nima nayi sallah nayi en lazimi na har ya dawo ina kan dadduma,, seda gari ya soma haske bacci ya daukeni danni banma so komawa baccin ba,,

yau da yamma mukarram ya kawomin waya wai inji alhaji malam, nayi godiya sosai na bude naga message na accounts dina
alhaji malam ya zubamin kudade a ciki, kawai jira nke ya dawo nayi mai godiyar abinda yakemin

sai yamma likis alhaji malam ya dawo naje nayimai godiya sosai yace bkomai,, nan yake sanar dani goben se wajen magrib zamu dauki hanya,

ina zaune ina tunanin innata inda hali inaso naje naganta, amma yanxu innaje me zance mata? nasan akwai tambayoyi da yawa da zatamin gameda wannan auren nawa wanda ni kaina ban gamsu ba balle nayi wa wani bayani,, watakila kuma idan naje ma na qara mata kan damuwar da take ciki,,
tunanina ya katse jin shigowarshi, hannunshi rike da cikinshi ya shigo falourn idonshi ya sauya launi fuskarshi tayi ja da alama yana jin jiki,, da sauri na qarasa dan tsananin tausayi na rikoshi, ina jera mai sannu kan doguwar kujerar ya zauna na dakko mai magungunan shi ya sha,, ya hada uban gumi dukda A.C dake dakin hawaye ya silalo min dan tabbas dukkan alamu sun nuna yana cikin jin zafin ciwon,, hannuna na cikin nashi se qara matse hannun nawa yake saboda azaba,,
se da yayi kusan 30 mins sannan ya lafa, wani wahalallan bacci ya daukeshi, a hankali na saka hannu na danyi baya da gashinshi daya hargitse har ya kwanto mai kan fuska,
"meyasa kake wahalar da kanka,, ka tafi kaki shan magungunan ka"
ita kadai take maganganunta, dama dare yayi ganin yayi bacci yasa na samo blanket na lullubeshi ni kuma na kwanta kasan kujerarshi, bacci ya kasa dauka ta ina ta tunane tunane
"dole na ringa kula da safwan da kaina, dan da alama ba lapiarshi yakeso ba,
wani bangaren zuciyata ya tambayeni, toke mene naki na damuwa tunda shi be damu ba,
"for the sake of humanity ai bazeyu dan mutum yayi maka ba daidai ba kaima ka saka mai da ba daidai ba, yanada kyau mu dinga koyi da kyawawan halayen fiyayyen halitta a matsayinmu na musulmi, in mutum yayi maka ba daidai ba kai kuma se ka saka mai da alkhairi wanda indai yanada hankali ze san be kyauta da kanshi ze zargi kanshi,, na bawa kaina amsa,
"bazeyu ba wanda kuke taredashi dukda ba zaman wani arziki muke ba baida lpia kuma na wofantar dashi, ko darajar alhaji malam ma ai zeci..
still wani bangaren zuciyata ya kuma tambaya ta
wai shin deejeh me safwan ya miki har haka da kika rikeshi kika qi sakin jiki dashi kamar yadda ya fada miki, alhalin cikin koyarwa irin ta addinin islama yayi hani da riko, da gaba forget nd forgive shine hali nagari..
(cikin wata qissa: sahabbai suna zaune tareda fiyayyen halitta kullum wani mutum zezo wucewa se fiyayyen halitta tsira da aminci su tabbata a gareshi yace "ga dan aljanna nan" hakan yaja hankalin sahabban, kullum haka, se daya daga cikinsu yaje ya zauna dashi yaga dai har shi yafishi yin wasu ibadun ma, seya tambayeshi yace wai shin wanne aiki kake aikatawa ne haka da Annabi (SAW) yake cema dan aljanna,? se mutumin yace shidai yasan kullum in ze kwanta bacci zece ya yafewa kowa kuma har zuciyarshi, baya ta6a kwana da wani a ranshi,, Allah yasa muyi koyi da wannan kyakkyawar dabi'ar ameen)

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now