So faruwa yake 8&9

2.5K 132 0
                                        

[12/18/2018, 11:07 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*thank you thank you redears,, for the comments and masu son novel dinnan nagode muku hop zaku cigaba da bina har mukai qarshe thank you ma people*

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *008*

karfe 10:40

a yanxu kam har safwan ya kammala cin abincin nashi,, yana zaune kan doguwar kujerar ya miqe qafarshi har lokacin be shiga dakin ba,,
deejeh ce ta shigo da sallama ya amsa, ta qarasa ta kwashe kwanukan hakan yayi daidai da lekowar da laila tayi dan ta gaji da jira,, taga deejeh na kwashe kwanuka dadi ya isheta tasan safwan ya kusan zuwa..

ta tattara komai tana qoqarin miqewa dayake a center table din suke, taji cikin murya qasa2 yace
"ki kawomin irin milkshake din dazu"
ok sir deejeh ta fada gamida ficewa tana qara godewa Allah dayasa tayi 2 cups da yanxu setaje kitchen hada milkshake da daren nan,, ta dakko milk shake din tana jinjina tsirfa irin ta safwan,,

laila ganin deejeh ta fitane ya qara miqewa bashi da niyyar tashi yasa ta gyara zaman en iskan kayan dake jikinta ta soma taku kwas kwas,,
cike da dumbin mamaki safwan ya juyo saboda jin qarar taku,,
ai kuwa yayi ido hudu da laila wacce a lokacin har ta qaraso inda yake,, ai kuwa ba zato ta fada jikinshi, tana qanqame shi tana qoqarin lalubo bakinshi,,
da sauri safwan ya nemi tsari ta hanyar fadin 'a'uzubillah' duk ta qanqame shi,,
hakan yayi daidai da shigowar deejeh da sallama,,
se kiciniya suke yana qoqarin yakiceta daga jikinshi ita kuma se qara makalkaleshi take,,
at last ya samu ya fizgeta gamida yin wulli da ita har ta kai qasa,,
deejeh kuwa a yanxu har ta juya dan ficewa saboda abinda idanuwanta suka gane mata, ta tsinkayo muryarshi na kiranta,,
ta juyo tana amsawa da na'am sir,, yace ki ajiyemin milkshake din anan,, ya mata nuni da center table din..
laila ko damuwa da deejeh tana nan batayi ba ta soma hargagi
"haba safwan nifa er uwarka ce saboda Allah,, dan nace ka soni shine kake wulakanta ni, dubi fa kaga yadda nayi dukka wannan kwalliyar saboda kai daya amma ko dubawa bakayi ba"
se huci take kamar baqin kumurci,, qarasowar deejeh yayi daidai da damko hannun laila da safwan yayi a fusace yana jawota,,
har bakin qofa yayi wulli da ita yana mata wani kallon tara saura kwata, deejeh kuwa sum sum ta zo tabi ta wuce gabanta na faduwa jin yadda yake huci kamar baqin kumurci,,

deejeh na fita ya datse kofarshi ya saka key ranshi duk a bace..
ya zauna kan cushion din tareda dafe kanshi,, "wannan wacce irin jaraba ce, wanne zamani ne haka muke ciki,, halaka kiri2 dole se mutum ya kai zuciyarshi nesa" nan yayi addu'o'i dan neman tsari..

ni kuwa jin ya banko qofar shi yasa nayi gaba abina nabi dukka fitilun na kashe da kayan kallo, sannan na wuce dakina ina tsananin mamakin wannan abu dana gani,,
ashe har zamani ya kai haka, ni deejeh ban taba tunanin mata na kawo tallan kansu ana wulaqanta su ba,, wannan wacca irin rayuwa ce sedai muce Allah ya shiryemu bisa tafarkin addinin islama,,,  Amin

Ran laila  yakai qololuwar baci yau kam, dan bata taba tunanin safwan baze rikice mata ba a yadda ta chake dinnan,,  kodai bashida lapia ne, eh ta tambayi kanta kuma ta tabbatr wa da kanta amsar tareda yadda da cewar tabbas safwan bame lapia bane,,

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now