So faruwa yake 6&7

2.7K 132 0
                                    

[12/18/2018, 11:07 AM]: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *006*

tun wajen 11 na kammala ayyukana ummi se yabona take kan ayyukan da nayi, na koma daki kafin zuwa rana haka inda ummi zata fadamin me za'a dora se naje na fadawa ma'aikatan,, yau kam nayi missing restaurant musamman kitchen,, shaf na manta da maganar mukarram,,
qarfe 12 ummi ta shigo dakin, na miqe nan ta sanar dani abinda zance a dafa na amsa mata gamida miqewa na zura hijab dina,
baya na zagaya inda masu aikin girki suke,, wata er datrijuwa na gani wacce naji ana cemata gwaggo,  na qarasa muka gaisa na fada mata saqon ummi dan ummi bata girki se alhaji na gari,,
gwaggo irin mutanen nan ce me surutu,, ni kuma dama na gaji da zaman ciki ni daya yasa na zauna gunsu gwaggo har a gama girkin,,
dukda yanxu na dan san wasu girkunan,, ina nan ina taya gwaggo aiki
se ga wata daga cikin masu tayata aiki nan ta shigo,, ta kalli tukunyar dake kan murhu,, ta kalli gwaggo
"ap gwaggo an kuma", dukka muka tsaya muna kallonta, meya faru? gwaggo ta tambayeta
"kinsan ai tunda Alhaji malam (baban safwan) baya gari dole muna da en talla dan kuwa yanxu laila ta shigo gidan nan, kuma nasan kwana zatayi  gashi kuma kun dora sanwa kadan"
gwaggo ta fahimceta se ta kalleni tace deejeh jeki tambayeta me takeso a dafa mata,, banyi musu ba na miqe na tafi
a main falourn na sameta tayi dai dai itada ummi suna hira, laila yarinya ce er shekaru 24 haka taci ado kamar me shirin zuwa gasar kyau, batada tsayi sosai kuma batada haske dan ko deejeh ta fita haske
bayan nayi sallama ummi kadai ta amsamin tareda fadin ya akayi khadijatu
nace "gwaggo ce tace nazo na tmbyeta me za'a dafa mata"
ummi ta kalli laila tace
"laila kinji wai me zakici?" yanxu dai meatpie nakeso anjima kuma zanci spring rolls da jollof rice" ummi ta kalleni "khadijatu dakko mata meatpie a fridge da drinks se ki sanar a dora abinda tace "nace to,,
naje fridge na dakko meatpie tareda drinks da cup na dora a tray na kawo mata,, daga haka na fice zuwa gunsu gwaggo
nan na sanarwa gwaggo,, gwaggo kuwa tace bata iya wani spring roll ba dama dai meatpie dinne,, nikam na koya sanda nake aiki a restaurant dan haka nace musu na iya,,
tare mucigaba da aikin, muna cikin aikin gwaggo ta kalleni tace
"amma Allah wadaran wasu matan masu tallan kansu," cike da rashin fahimtar ta na kalleta nace gwaggo meya faru"? tace
"ai tunda Alhaji malam baya gidan nan zakiga en mata masu talla sunzo gun safwan,, hakan yasa shi ma safwan din yake barin gidan da zaran Alhaji malam baya nan"
tabdi na fada a raina a fili kuma nace
"amma gwaggo me yasa se Alhaji malam bayanan suke zuwa?"
kama baki gwaggo tayi alamar mamaki
"tab ai Alhaji malam mutum ne mai tsauri, baya barin shigar banza a gidanshi, inde yananan takura musu yake,, babu wacce ke ko qwaqqaran motsi ko muma muna shakkar shi,, hatta iyalanshi ma, dan mutum ne me magana daya, ga addini amma yanada haquri sosai da sanin yakamata, akwai dattako, sannan yanada fara'a inde kikaga fadanshi to akan addini ne akayi ba daidai ba"

na gyada kai alamar gamsuwa dan tsarin Alhaji malam kam abin burgewa ne, haka ya kamata ace kowanne magidanci yake da kula a cikin gidanshi,

mun kammala komai,, nayi springrolls din da d'an yawa, bayan komai ya kammala ne na debi na cikin gida na dan shirya table,,
spring rolls din na dibi yadda zata isa sauran kuma na zuba a fridge,

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now