So faruwa yake 13&14

2.2K 106 3
                                    

[12/18/2018, 11:12 AM] Sis Zee mtn: 💝💝 *SO FARUWA YAKE* 💝💝
                       🎀🎀🎀
                         🎀🎀
💝💝
   💝   *love just happens*👌🏻

By,, *Aysha b (Aeshab)*💌

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
           ☆We the best ☆

Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

realhausafulaniwriters@gmail.com

بسم الله الرحمان الرحيم

                        *013*

A zahirin gaskiya alhaji malam be san gidan safwan arfa ta taho ba, kawai dai ta musu sallama dan sanda tabar gidanma alhaji malam bayanan,,
cikin dakin ta kai kayanta, ni kuwa na zuba abincina na dauka banko sauraresu ba, daki na nakoma naci abinci,, seda nayi sallar isha'i sannan na dakko kwanon na fito, banga kowa ba kuma dama naji motsinsu daga dukkan alamu dai sun fita ne, na daga kafada alamun su ta shafa na dauke warmer din na maida kitchen na wanke kwanukan, dan iya cikina kawai nayi girkin..

suna zaune a motar, arfa ce ke driving, dan cewa tayi yazo su fita ya dan sha iska,, daidai wani babban restaurant suka tsaya wanda beda tazara sosai da gidansu sadwan da deejeh,,
sun bada order arfa se hira take mai shidai baifi yace um ko um-um ba,
sanda aka kawo musu suka faraci duk se sukayi shiru, se can arfa tayi mai kallon tsanaki,,
"dan uwa wai me kake tanadi ne gameda wannan aure naka,?"
kamar ta sani abinda yakeso kenan ta sosa mai inda kemai qaiqayi
"wlhy er uwa ni kam bani da wani shiri, bansan mene manufar wannan aure ba"
"tabdi ai kuwa ya kamata ka sani, kawai ka zauna da ita, ka sanar mata kaifa zaka saketa..."
tun bata ida zancen ba yace
"ai babu ma saki in kuma ba so kike Alhaji malam ya tsine min ba"
arfa ta tabe baki ta cigaba da cin abincin,,
mintina kadan kuma se ta dago
"ina da shawara dan uwa,"
"meze hana ka samo mata miji sannan seka saketa kaga alhaji malam bazega laifinka ba, indai ka aurar da ita"
tunani safwan ya tsunduma kusan 30 seconds sannan yace
"eh kinyi gaskiya er uwa tunda itama nasan ba sona take ba dan haka zance ta fidda miji kawai na aura mata shi wanda takeso"
arfa tayi wani murmushin mugunta, yawwa dan uwa, amma dama ai bazeyu kuyi ta zama haka nan ba"
haka safwan ya gamsu da maganar er uwar tashi har ya dan soma walwala,, se wajen 10 suka dawo gidan, lokacin deejeh tana kan dadduma ta idar da shafa'i...

arfa ta wuce dakinta shikuma ya shigo na deejeh da sallama,, ta amsa ciki ciki indai ba kusa daf da ita kake ba bazaka sani ba..

a gefen gadon ya zauna ko kallo be isheta ba,
"amm khadija dama na yanke shawarar raba auren nan namu, tunda kamar an shiga haqqinki, dan ke baki cancanci mutum irina ba kwata kwata, shiyasa na baki dama ki samo miji in yaso se na aurar dake dan alhaji malam baze yarda ba na sakeki"
harara deejeh ta zabga mai wacce besan tanayi ba,
sun dau tsayin lokaci babu wanda yace da wani kala, dan haka se ya miqe yana fadin
"na baki lokaci zaki iya tunaninki son ranki," daga haka ya fice
sanda ya koma daki arfa tayita yi mai wasu abubuwa da be gane ba, ganin haka yasa yace shi bacci zeyi, ta tayar da bori ita a dakin zata kwana,, sunsha fada ya koreta, ai kuwa dataga yayi bacci ta salalla6o ta dawo ta kwanta a jikinshi,, se asuba suka farka,

kwanaki se tafiya suke zama kam babu dadi tsakanin deejeh da safwan, arfa kuwa tana nan taqi barin gidan, yau deejeh zata fara zuwa university dan duk abinda ya kamata uba yayiwa diyarshi, alhaji malam yayiwa deejeh,,
dan an kawo lefen nata akwatuna 8, a haka ma dan a gaggauce ne,, kuma dukka kayan a dinke suke, daga kan atampa, less, material, shadda,,, kayan kwalliya dadai duk tarkacen mata,, komai a wadace har sunyi yawa ma,
anty salimat tayiwa deejeh nasihu sosai, kan ta riqe mijinta, ta tunasar da ita haqqin aure da kuma amfanin haquri, 

SO FARUWA YAKE CompleteWhere stories live. Discover now