Babi na 3

869 80 0
                                    

Wata sabuwar duniya ce domin kogon nan zagaye yake da wani dutse wanda tsakiyar Wannan dutse ya kai girman rabin masarautar Kalahari gashi kuma jeji ne sosai mai yawan duhuwa ,kayan itatuwa kuwa babu kalar da babu ga ruwa yana gudana daga saman dutse tsuntsaye sai shawagi suke a gurin ,🕊🕊 , ‘kara da yaji ta wani 6angaren ya tabbatar masa akwai namun daji ciki kuma masu cike da had’ari
        ya ja dokin sa har inda ruwan yake hannun shi d’aya kuma rik’e da Jaseena. Ruwa ne mai kyaun gaske ,yanda yake gudana ma abin kallo ne a nan ya dauraye jikin Jaseena dokin shi ma ya sha..nan ne fa Hameed ya fara sabuwar rayuwa daga shi sai dokin shi Zabil da kuma Jaseena wanda mahaifin ta ya maida ruwan kwakwa abincin ta, shi kuma yakan kama kifi ya busar don ya samu abin ci ,ko kuma y’ay’an itatuwa..haka suka yi ta rayuwa a jejin………..
     

 bayan shekaru goma sha shida(16 yrs ltr)

    Zaune yake a fadar sa, su waziri sai zuba fadanci ake , wasu maza wad’anda da ka gansu kasan cewa magidanta ne sanye cikin kayan da basu fi a k’ira su  da tsumma ba suka shigo fada gami da zube wa ‘kasa suna kwasar gaisuwa duk jikin su sai 6ari yake yi d’aya daga cikin su yace ” Allah ya baka nasara sarki !!! Mun kawo k’arar Yerima !! Ya takurawa y’ay’an mu ko diban ruwa basa iya fita saboda da ya gansu sai ya fasa tulun,shine  muk………….kafin ya k’arasa yaji sauk’ar mari Tas!!!! Hakan yasa ya mik’e a firgice yaji an sake kwarfe shi ta k’afa take ya zube ‘kasa warwas !! Sarki ya ja tsaki Mtsew!! Yace ” ni zaku dubi tsabar idona Ku zo min da zancen banza Wai kun kawo karar Yerima? Toh baku isa bah !! Wato har an fara sa mishi ido kenan ? Ina so ku sani ,Rizwan Jini ne na sarauta yana da ikon taka duk wanda ya so kuma babu mai tanka masa ” ya dubi sarkin yak’i yace ” me kuke jira ne Amjad?!!! Aje a rufe min su a kurkuku da kuma horo mai tsananani!! Da sauri sarkin yak’i Amjad ya kama hannayen su ta baya ya tisa ‘keyar su suka bar fada yayinda Jalalud-deen ya koma kan kujerar sa yana maida numfashi kamar wani damisa
           Sarkin yak’i Amjad yana fita da su yayi hanyar kurkuku dasu ,murya ‘kasa- ‘kasa yace sai dai ku yi hakuri da irin Wannan zalunci da ake muku ni na tabbatar cewa akwai ranar da zata zo idon Jalalud-deen sai ya raina fata kuma sai ya zama wulak’antace a idon jama’a!! Yayi d’an murmushin takaici dai dai lokacin sun iso mashigar kurkukun ya wuce chan ciki da su ,sun dad’e suna tafiya kafin su iso d’akin da za’a sa su ,ganin masu gadin na kallon sa ya sa ya hakad’a su ciki a fusace ,gami da rufo k’ofar ya juya idonsa cike da k’walla ya fice Daga kurkukun…..
 

       Gudu take a kan dokin sanye da bak’in dogon wando mai fad’in gaske ta sama , ta ‘kasa kuma a tsuke,rigar jikinta na cikin dogon hannu ne da shi kuma sak’awa akayi da auduga na saman kuma da fata akayi shi bak’in mayafi ne rataye a kanta wanda har ya zagaye fuskar kamar wanda tasa nik’ab baka ganin komai sai girar ta ,idon ta da kuma saman zirin karan hancinta , takalmin k’afarta ma na fata ne ,ta rataya wata y’ar jaka a jikinta sai wani dan biri da ke zaune a kafad’ar ta

     ”  Hyaaaa!!!” Ta fada gami da bugan dokin ta baya ,yayin da shi kuma ya kara gudu. Sun dad’e suna tafiya kafin su isa mashigar garin tana isa ta sauk’a daga saman dokin ta kama linzamin suka ci gaba da tafiya basu zame ko ina ba sai kasuwar garin nan ta wuce gun wani mai saida ganyeyaki na magani ta mik’a masa jakar , ya karba ya Ciro kad’an daga ciki ya shinshina sannan yayi murmushi ,yace ” yayi kyau Jaseena !! Wannan na’a  na’a mai kyau ne !! Ya sa hannu cikin aljihun shi ya Ciro sulalla ya muk’a mata ta kar6a ta juya abunta ba tare da ta ce k’ala ba ……..
        Cikin kasuwar ta sake kutsa kai tana ganin yanda Kowa ke gudanar da alamuran sa cikin kwanciyar hankali ,kai tsaye ta nufi gun mai shinkafa ,ya auna mata ta kar6a kawai ta jiyo hayaniya bata ankara ba ta hango dawakai kusan biyar sun dumfaro inda suke ,da wasu matasa a kai sai 6arna suke ,guda daya daga cikin su ya sha ado da kaya irin na alfarma shi ya fi Kowa ma ta’adi a cikin su suna ta buge mutane ,suna zubar musu da kayayyaki ,ta gefen Jaseena suka wuce gami da banke wata mata mai juna  ta fad’i ‘kasa kayan marmari da ta siyo ma duk suka zube ,a fusace Jaseena ta dubi mai shinkafan tace “Wannan kuma su  waye haka kamar mahaukata ??!!! Mai shinkafa ya zaro ido yace ki rufa ma kanki asiri baiwar Allah!! Wannan shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !! Ta juya ta sake kallon hanyar da suka wuce tana wani irin murmushi na k’eta ” a ranta tace lallai yau kakarta ta yanke sak’a!!! Mai shinkafa ya ce ” amma baiwar Allah kina garin nan kice baki san Yerima Rizwan ba? Murmushi kawai tayi ta d’auki shinkafan ta sa a Jakarta ta juya ba tare da ta kalle shi ba balle ma ta bashi amsa ,ta nufi gun matar da ta fad’i kasa wanda duk an zagaye ta ana kallo kuma babu wanda ya ma je kusa da ita  don ya taimake ta……………

JASEENA Donde viven las historias. Descúbrelo ahora