Babi na 9

706 76 4
                                    

Suna tafiya tana mata hira har suka isa wani babban gida ,ginin mai tsayi ne sosai ga kyau kuma tare suka shiga kai tsaye hanyar d’akin girke -girke suka nufa yarinyar ta ajiye kwandon kwai din ,a d’ayan 6angaren kitchen din kuma wayannan yan matan nan ne da suka mata dariya tare da Jauda suna tsaye sun zuba musu ido ,d’ayar tace ” ke!! Benaxir fa ta dawo !!! Kika shigo da Wannan bakya tunanin zata iya 6ata miki rai in ta ganta ko??!” Murmushi Jauda tayi sannan tace ” babu komai Aisha ai zamu fita ta baya in Mun gama aiki !!” Aisha de bata sake tanka mata ba ,Jaseena tace ” Wacece Benaxir har kuke tsoron ta haka ? D’ayar da tun farko bata tanka mata ba tace ” Wannan bai shafe ki ba !!:roll:” a tare Jauda da Aisha suka daka mata tsawa gami da k’iran sunan ta Meenah!!! Wai ke me yasa bakya son mutane ne kin cika bak’in hali !!? ” Aisha ce ta k’arasa maganar……
Jaseena tayi murmushi tace ” ni zan koma ,nagode da kyautata wa da kuka yi min ” Aisha tace don Allah ki tsaya mana yanzu zamu gama aiki mu tafi fada ,yau akwai tseren doki a fada kuma Kowa zai halarci gurin domin fidda gwani a wajen sarrafa doki ,kuma fa har akwai fad’a da zaki ,kowacce shekara yarima Haidar ke gaba a duk fannin.!! Kinsan yarima Haidar da son mutane ! Ai shine ma sadaukin Wannan masarauta Kowa yana karrama shi ,ba kamar mahaifin shi sarki Hasheem ba ,bai d’auke shi a kan komai ba ,Kinsan Haidar abokin mu ne tun muna k’anana tare muka taso har yanzun nan da kika gani ,ko lokacin da muka miki dariya a hanya ma ai shi ya hana mu in ba haka ba da abun ya fi haka ,ko wacce a cikin mu na da labari mai ban tausayi tun yarintar mu kuma labari mai ban tausayi amma da Sannu zaki san komai amma kafin nan ko zaki iya bamu labarin rayuwar ki da yadda akayi kika tsinci kanki cikin Wannan masarauta ta Ramali?? ”
Nan Jaseena ta kwashe duk labarin rayuwar ta ta fad’a musu har yadda akayi ta fito daga dutsen da had’uwar ta da shi Haidar ,duk sun tausaya mata matuk’a , Jauda ta mik’e tsaye tace ” toh ai duk labarin d’aya ne duk fa akan mulki aka k’ask’anta mu kawai don an fi k’arfin magabatan mu toh yanzu zama zamuyi a dinga cin kashi a kan mu ne??!! Aisha ta mik’e tace ” inaaaa!! A’a Sam bazai yiwu ba dole mu kwace hak’k’kin mu da kan mu mu tashi muyi yak’i mu k’watar ma kammu y’anci!!! ” Jauda ta sa hannu tace ” wa yake tare da ni??” Duk suka d’aura hannayen su a kan nata gami da cewa “ni!!” Duk suka maida dubansu ga Meenah da ko motsawa bata yi ba ,ganin duk sun sa mata ido itama ta d’aura nata hannun” Jaseena ta rasa Wannan wane irin hali ne Meenah take da shi kwata kwata batada fara’a a fuskar ta. A tare suka watsa hannayen sama kowannen su yana murmushi irin na masu k’arfi a jika
    
Jaseena. 

Guri ne babba na gaske amma mutane duk sun cika gurin an zagaye makeken filin wanda Hasken farin wata ya cika shi fal! Gurin da mutanen suke hawa hawa ne ga fitilu nan ta ko ina sun haska benen dake sama sosai shine inda sarki Hasheem ke zaune shi da wata Kyakkyawar mata tasha ado na zinare ,gefe d’aya kuma sarakuna ne da matan su wayanda suka zo suma da y’an wasan su ma’ana sadaukai na k’asar su don suma su fafata a cikin gasar ,akwai gefen sarki Hasheem wanda duk cikin guraren ya fi ko ina k’ayatuwa ,wani sarki ne bashi da haske sosai amma da ka ganshi kasan ya dama ya shanye a sarauta ,gefen shi wani kyakkyawan saurayi ne ya sha ado gwanin sha’awa fuskar shi babu almuru ga dukkan alamu d’an sarkin ne ,ga kuma wani ta bayansu a tsaye da alama sarkin yak’in su ne don sanye yake cikin kayan yak’i saidai ya manyanta sosai don dattijo ne….

Toh masu ku biyo ni a episode na gaba don jin wainar da zata toyu a Wannan fili na gasa ,ina godiya masu karatu love you all!!

JASEENA Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang