Babi na 7

669 70 0
                                    

Duk Wannan abun da ya faru Haidar na tsaye yana kallon ta ,shi ma kanshi ta bashi dariya kawai ya tsare ne,kwata – kwata rigar baibai ta saka shi bayan haka kuma gaba a baya ,duk da hakan da tayi yay matuk’ar yi mata kyau amma ba daidai bane shi yasa matan ke mata dariya….
Nan ta nemi k’ark’ashin wata y’ar bishiya ta zauna tana ta 6ata rai harda d’an hawayen ta ,tace ” ai yanzu da baba ne bazai min dariya ba cewa zai yi yayi min kyau !! Toh ma miye laifin kayan nan tunda dai ba tsiraici na bari a fili ba!!!Mtsew!!!” Take ta zabura ta mik’e tace” Baba!!!”

*****        ******      *******
Kwance yake cikin wani matsatsen d’aki mai duhun gaske duk ruwan datti ta nan yake biyo wa ,ya tashi ya mik’e tsaye sai kai kawo yake a d’akin yana cizon le6e ,duk tunanin shi ya koma kan y’ar sa Jaseena addua kawai yake yi Allah ya sa Kar su gano ta ,Allah yasa basu kamata ba duk da yasan k’arfin damtse na y’arsa da kuma wayo irin nata. ” HAMEED!!! K’iran da waziri Zakar yayi masa kenan , hakan ya sa shi juyawa cikin sauri fuskar shi a d’aure. ” kamar yadda muka kamoka kamun wulak’anci haka zamu kamo d’iyar ka da kake tak’ama mai k’arfi ce mu wulak’anta ku a bainar jama’a !!! Hhahhah !!!!! ” Zakar kenan yayi Wannan magana ,bai ankara ba yaji an shak’e wuyan shi har saida idanuwan shi suka fito kwala kwala ,ya kasa magana. Hameed kenan !! Yana cikin kurkuku ma amma k’arfi na nan !!. Wasu masu gadin gurin su biyu ne suka tunkari inda suke da ‘kyar suka cire waziri daga rik’on da Hameed yay masa sukayi waje da shi ,yayinda shi kuwa gogan ya koma ya zauna yana maida numfashi ………….

A tsayen da take tana tuna halin da mahaifin ta zai shiga a Kalahari taji durowar abu ta bayanta tuni ta zari wata y’ar wuk’ar ta ta juya zata kai hari ,hannu ya sa ya tare ,wuk’ar ta yanke shi a hannu. Tana juyawa taga ashe Haidar ne ta zare ido,a rikice ta cire gyalen da ta rufe
kanta ta raba gida biyu ta d’aure masa yankan da tayi sai bashi hak’uri take yi ,ga dukkan alamu bai ji zafin ciwon ba sai murmushi yake mata ,jiki a sanyaye ta nemi guri gefen bishiyar ta raka6e tana y’ar hawaye….
Wata murya mai dad’in gaske da ratsa zuciyar duk wani mai sauraro taji yace ” Jaseena!! Ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ,inaga lokaci yayi da zaki sanar da ni matsalar ki wata’kila na nema miki mafita ko in taimaka miki!! Kinga dukkan mu nan ko wanne yanada matsalolin da yake neman mafita amma 6oye su bazai amfane my da komai ba har lokaci ya k’ure mana !! A firgice ta juya tana neman inda akayi maganar amma ta rasa domin ta lura babu Kowa a gurin sai Haidar da har Lokacin murmushi kawai yake yi rik’e da hannun shi yana kallon ta da kuma mamakin yadda ta rikice tana neman wanda yayi magana………
Ta dawo gaban Haidar tana kallon cikin idon shi tace ” bakaji wani yayi magana ba ? Baka ga wanda yayi ba?” Murmushi ya sake yi sannan yace ” ni nayi miki magana Jaseena !!” Nan ta tabbatar tabbas shi ne yayi magana ,kafin ta ce komai ganin yadda ta saki baki kamar wawuya yasa ya fisge hannun ta yabi wata hanya da ita sai cikin wani daji dake gefe da gurin ,kan wani gungume ya nuna mata ta zauna ,yace ” eh nine nayi magana ! Kuma ke kad’ai ne kika san hakan ko sarki bai sani ba ,kuma ina so ki rik’e shi a zuciyar ki ,duk Lokacin da kike buk’ata muyi hira to kizo nan amma Kar ki kuskura wani yasan ina magana !” Kai kawai ta girgiza mishi cike da mamaki har lokacin ta kasa nutsuwa…,

JASEENA Where stories live. Discover now