Isarsu masarautar ,bai zame da su ko ina ba sai cikin hanyar fada ,yana gaba tana biye da shi cikin ranta tace ” yanzu har akwai masarautar da bawa zai dinga kutsa kai cikin fada ba tare da izini ba? ” bud’ewar wata k’atuwar k’ofa ne ya katse ta daga tunanin da take yi ,kai ya kutsa ba tare da fadawan sun Hane shi ba har ya k’arasa ya nemi guri ya zauna ……..
Zubewa tayi itama tana kwasar gaisuwa kamar yadda yayi sannan ta gyara zama. Wani bak’in mutum ne wanda fuskar shi ba wani almuru don ko murmushi da yake yi kamar dole aka sa shi yake yi . ” yarima har an dawo ne!!? ” tambayar da sarkin yay masa kenan ,yayin da shi kuma saurayin ya gyad’a masa kai ,nan yaci gaba da yi masa kwatance da hannu irin na kurame ita dai Jaseena ta zuba musu ido cike da mamaki da kuma tambaya dake cikin zuciyar ta ” me yasa Yerima guda babu ko hadimai balle shiga ta alfarma?! ” don ita da tayi zaton bawa ne gashi kuma kyakkyawan gaske amma mahaifin sai bak’i da muni ,ta d’an jinjina kai tace ” hala mahaifiyarsa ya biyo”
Maganar sarkin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga ” Yaya sunan ki baiwar Allah? ” shine abunda yayi karo da kunnen ta. A d’an rusune tace “Jaseena”. Sarkin ya d’an yi murmushi yace ” daga yau na baki masauk’i cikin masarauta ta domin Yerima Haidar ya sanar da ni cewa 6ata kikayi ,toh nan ya zama miki gida kina da iko ki shiga duk inda kike buk’ata a masarautar nan ! Tai ma sarki godiya sannan Haidar ya ja ta suka fice daga fadar ya mik’e da ita har wani hanya daban wanda ta yi nisa sosai da fada ga k’ofofi kala kala masu kyau da kwalliya ga fitilu masu haske abin ba’a cewa komai …..
Wani d’aki ya nuna mata ta sa hannu ta bud’e ta shiga da murmushin ta zainu na biye da ita ,shima murmushi yayi sannan ya juya ya fice daga wajen yayinda ta bishi da kallo kamar Yar k’auye.Yau kwanan Jaseena uku a Wannan gari wanda ko ita kanta bata san sunan garin ba ,Haidar kuwa kusan kullum da safe sai ya lek’o don ya duba lafiyar ta ,haka take wuni ita kad’ai sai zainu yana d’ebe mata kewa kasantuwar Haidar bai cika dawowa da wuri ba in ya dawo ma sai gari ya waye yake duba su….” Yau kam sai na fita na zaga gari!!” Cewar Jaseena kenan tana ta faman gyara zaman dogon rigar da ta saka ,sai duba kanta take ta madubi don bata saba saka irin kayan nan ba ,ita kanta ya mata kyau ,sannan ta dauki mayafin wanda da shi da kwalin tata duk d’aya ta yafa a kanta ta nannand’e ta fice zainu na binta a baya kamar yadda ya saba , tana tafiya tana faman tattare riga don yadda yake Jan ‘kasa a haka har ta bar fada ,tana ta kalle kalle ta tsaya can ,ta ta6a wancan , tana cikin haka har tayi nisa da masarautar a can nesa ta hango wasu mata guda uku kowacce da tulu sun sha ado sai ture -turen juna suke a kan hanya suna ta raha……
Cikin sauri Jaseena ta k’arasa inda suke ,tana iskesu ta sa hannu ta ta6a kafad’ar daya daga cikin su duk suka juyo suka k’urawa Jaseena ido sai kuma suka bushe da dariya suna nuna ta da yatsa hakan yay matuk’ar bawa Jaseena haushi ta yamutsa fuska tace ” toh me nayi kuke min dariya !!. A tare suka tsare kamar da gaske sannan suka sake bushe wa da dariya ,wata Yar siririya sosai tace ” ke kuma Wacece haka !? Ko rigar ma bata iya sak’awa ba Yar k’auye kawai!! Suka juya suka ci gaba da tafiya yayinda ita kuma Jaseena ta tsaya Kallonsu har suka shige ta daina hango su ma……………

ESTÁS LEYENDO
JASEENA
AventuraIts a war for pride! A story of royalty and love! Jaseena a valiant girl whos love for adventure unfolds the truth behind her identity, a truth which changes her life from herb trader to a great warrior and queen