Isarsu Kalahari basu zame ko ina ba sai cikin fada kamar wanda ake jiran isowar su mutane aka fara bude hanya don su samu su wuce ,Jaseena kam da ta hango baban ta taga yadda suke tafiya a hankali a saman dokin ,yasa ta dirko daga kan dokin ta ruga. Rungume mahaifin nata tayi tana kuka ,ya d’ago ta yana faman share mata hawaye ,zata yi magana kenan suka ji Hameed ya ja wani irin numfashi kamar an shak’e shi ,idon shi na hawaye ,tace ” baba!! Me ya sameka baba??” Kallo na biyu da zata masa ne ta ga abunda ya matuk’ar tada mata hankali ,mashi ne a wuyan shi ga kuma Jini yana malala kamar ruwa ,a take ta kurma ihu ta zube a k’asa jiki na b’ari ,da gudu Haidar ya iso inda suke ya rike Hameed yana hawaye , abunda ya iya furtawa shine ” ga Y’ata nan Amana ,Kar ku cutar da ita marainiya ce don Allah!! ” ya dan saki wani ‘kara gami da Kalmar shahada take ya mace a gurin ,wani irin ihu Jaseena tayi ta sulale daga zaunen da take ta fad’i sumammiya Haidar ya dubi su Jauda da ke faman zubar da k’walla yace ” ku kai Jaseena ciki ku tabbatar ta samu kulawa don Allah ! Suka yi kamar yadda ya umarce su.
Haidar yace sojojin yak’i su shiga su nemo koma waye yayi wannan Harbin a kawo masa shi. Ana cikin wannan alamari ne wani soja ya zo da gudu wujiga wujiga duk jikinshi yanka ,sai haki yake yana kiran sarki Haidar. Fadawa suka tare gurin shigowar amma ya umarce su da su barshi ya karaso domin daga ganin shi kasan akwai wata matsalar da ke tafe da shi. Kafin mutumin ya fara magana ,Haidar ya juya ya dubi su Rizwan yace ” a shirya gawar baba mu sallace shi Mu kaishi makwancin shi na gaskiya,” sannan ya juyo ya dubi mutumin yace ” bawan Allah me ya faru da kai haka? Wa ya aikata maka wannan taaddancin kuma daga ina kake?
Cikin rawar jiki mutumin yace ” Allah ya baka nasara daga Ramali nake ….” Ko da Haidar yaji an ambaci Ramali yasan tabbas babu lafiya gashi sarki Hameed ya rasu ,ga Jaseena Kwance babu maraba da matacciya dole su Jauda su kasance tare da ita , toh me ma yake faruwa ne haka?” Tambayar da yayi wa kanshi kenan gaba daya ya kasa tunanin abu daya, ya tura wasu Fadawa tare da mutumin su bashi taimakon gaggawa kuma a kula da shi”…….
Ana shirin sallatar Hameed ne Jaseena ta farka ,bata bi ta kan su Jauda ba ta furma a guje ko mayafi babu duk gashi a barbaje gashi duk ta zabga gumi gashin ya mammanne mata a fuska bata zame ko ina ba sai gaban gawar mahaifin ta cikin yanayi na tausayi ,bakinta karkarwa kamar mai jin sanyi , ta d’aga hannun ta mai karkarwa kamar zata yaye masa fuska sai kuma ta fasa ta dunkule hannun cikin kuka tace ” baba !! Ka tashi don Allah kar ka tafi !!! Abunda ta yi ta maimaita wa kenan hakan ya sake tada wa Haidar hankali don a tunanin su ta zauce ne ,yadda take yi din abin tsoro da kuma tausayi. ” Meenah ku koma da ita ciki don Allah ” shima yana kokarin danne kukan da ya so kufce mishi.
Bayan sun dawo daga janaiza Haidar bai zame ko ina ba sai cikin fada don ya nemi dakin da Jaseena ke Kwance ,ko da ya iso gurin shi da Rizwan basuga Kowa a d’akin ba ,babu Jauda ,Jaseena Aisha da kuma Meenah. Haidar ya fito a fusace ya dubi bafaden da ke bakin k’ofar yace ” ina suka tafi kuma ?” Bafaden yace ranka shi dad’e sun fita su hud’u amma fa naji kamar suna maganar Ramali ban sani ba ko Chan suka nufa……. Bai ma saurari k’arshen zancen ba ya juya suka nufi hanyar fita……………….
YOU ARE READING
JASEENA
AdventureIts a war for pride! A story of royalty and love! Jaseena a valiant girl whos love for adventure unfolds the truth behind her identity, a truth which changes her life from herb trader to a great warrior and queen