Babi na 15

561 70 0
                                    

Haidar, Jaseena, Aisha, Jauda, Meenah, da Rizwan!!!! Duk na ji abubuwan da suke shiryawa !!! Don haka dole ne mu kawar da su tun kafin su cimma burinsu. Sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye ya rasa me zai ce saboda ko kad’an baya son dansa ya shiga wannan alamari amma tunda ya nuna taurin kan shi a fili toh lallai ba makawa sai an hukunta shi.
Haidar yana sane da cewa sarki Hasheem yana wannan gurin shi yasa ko ‘kala bai ce ba a gurin ,sannan kuma yasa Jauda tayi karya akan shirye shiryen da sukayi ,sun yi akan sai an gama gasa zasu far musu amma ashe shirin Sam ba haka yake ba !!! Cikin dare k’afa duk ya d’auke suka shirya duk irin yadda Jaseena take shiganta ,suka shigo fada ,Jaseena akwai ilimin duk wani abu da ya shafi yayan itatuwa da ganyayyaki saboda haka ta shiga d’akin da sarki Hasheem yake ta zauna bakin makeken gadonsa tana wani muguwar dariya ta fito da had’in maganin da tayi sannan ta debi kad’an ta watsa a fuskar shi a take ya farka gami da yin wani atishawa ya sulale ya koma kan filow ,nan ta d’aure shi ga igiya tam sannan tayi fito a hankali ,Haidar ya shigo shi da Rizwan suka ciccibeshi suka yi waje. Haka ne ya faru da sarki Jalalud-deen ma ,suna fita basu zame ko ina ba se cikin wani tangamemen daki mai kama da keji suka tura su ciki ba komai bane ke gadin wajen illa damisa guda uku manya manya
Da dariya suka fito su Jauda suka d’aga Jaseena sama yayinda Haidar da Rizwan ke ta musu dariya, suka koma cikin gari ,kasantuwar inda suka je da nisa ,sai kusan asubah suka iso cikin Ramali ,wannan kurkukun kuma shine asalin kurkukun masarautar Ramali kafin sarki Hasheem ya hau mulki. Isarsu cikin gari basu zame ko ina ba sai fada ,Haidar yasa a tara masa duk jama’ar wannan masarautar su hallara a cikin fada ,kafin awa d’aya duk Kowa ya samu isowa ,Haidar yayi murmushi ya gyara murya sannan ya fara da cewa:
Al’ummar Ramali !!! Akwai wani d’an karamin labari da zan baku labari ne na mikiya kuma ina kyautata zaton daga jin wannan labarin zaku fahimci Inda na dosa!!” Cike da mamakin jin magana da sukaji yarima Haidar yayi suka amsa da ” muna sauraron ka yarima!”

This episode is d shortest of all bear with me readers days are being hectic

JASEENA Where stories live. Discover now