Babi na 14

630 63 0
                                    

Sarkin yak’i Amjad ne zaune a gefen sarki Hameed hannun shi rik’e da na Hameed. Na ganta! Naga y’ar ka Jaseena ,tana cikin k’oshin lafiya ,kuma ga dukkan alamu tana cikin shiri,Hameed ya mik’e yana murmushi yace ” nasan ban haifi lalatacciya ba!! Kuma nasan dama tana nan tafe , amma ya maganan mayak’an da na ce ka tara ? Amjad yace ,komai an kammala shi kuma yanzu haka suna chan a kogon tare da y’an fursunan k’asar Ramali! Da sarki Hasheem ya sa Jalalud-deen ya d’aure shekaru kusan goma sha da suka wuce ” Hameed yayi murmushi yace ” da kyau sarkin yak’i!!! Aikin ka yana kyau ,Allah ya mana jagora!! Sarkin yak’i yace “Ameen”sannan ya mik’e ya fita………
Yau tun da safen nan Jaseena take motsa jiki tun bayan sun dawo daga gurin su Jauda Zabil kuwa ya samu Haidar ba kasafai yake waiwayar inda Jaseena take bama don in zai fita daji tare suke tafiya. Saidai yau Haidar bai je ko ina ba yana tare da k’anwar sa Meenah a cikin makeken lambun dake wannan masarautar suna ta hirar su duk da ma dai itama maganar kurmancin yake mata amma ta saba don ko ubanta Hasheem bai iya magana dashi sosai ba. A nan ya sanar da ita cewa yana soyayya da Jaseena, murmushi kawai tayi. Haka sukayi ta hira har kusan azahar, sannan ya tafi domin gudanar da ibada yayinda itama Meenah ta juya tabar wajen ,zata koma gidan Benaxir.

      Jaseena
Yau kwana na uku kenan ana ta bidirin gasa, Sam Sam Rizwan abun ma bai dameshi ba balle ma ya shiga ,hasalima cewa yayi babanshi ya chanja wanda zai yi wasan shi bazai iya ba ,babu yadda aka iya haka aka chanja shi da wani k’ak’k’arfa daga cikin mayak’an Kalahari. Jaseena kuwa tun ranar farkon nan bata sake shiga filin ba kullum tana daga chan baya ita da su Aisha amma fa ta lura cewa sarki Jalalud-deen hankalin shi bai kwanta da ita ba. Washegari da safe ta shira cikin dogon bujen wandonta bak’i da wata riga fara sannan ta rataya takobin ta da y’ar jakar ta ta fice daga fada ,fuskarta a rufe ta bar idanuwan ta a waje kamar wanda ta saka niqab , tafiya take cikin sauri kamar zata tashi sama, duk saurin ta sarki Hasheem yana tsaye ta sama a d’akin shi daga tagar d’akin yana kallon duk abunda ke faruwa ,tana fita Rizwan ma ya bi bayanta, ganin haka ne yasa sarki Hasheem shima ya rufa wani k’aton mayafi don Kar Fadawa su ganshi su ce zasu rakashi ya fice daga fada suna tafiya yana binsu duk yana jin abunda suke fad’a har suka shiga Inda Haidar yace za suna had’uwa ,ya lab’e bayan wani dan ice yana sauraron duk abunda suke fad’a….

JASEENA Where stories live. Discover now