Babi na 2

883 84 0
                                    

Bayan an na’da Yerima Hameed a matsayin sarkin Kalahari sai Jalalud-deen ya fuskanci cewa matar sarki Hameed Sarauniya JASEENA tana dauke da juna biyu hakan ya tunzirashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko baccin kirki bayayi tsabar Kishi domin gani yake yi in har Hameed ya samu magaji to tabbas babu makawa ko ‘kamshin sarautar ma zai daina ji…………
    cikin Sarauniya Jaseena yana wata tara ,haihuwa ko yau ko gobe ,tana zaune cikin dakinta mai cike da kayan ado da k’yal-k’yali sarki Hameed ya shigo ,mutum ne mai tsayin gaske ga haske kyakkyawa ne wanda ba sai na tsaya misalta shi ba haka ma Jaseena kasantuwar a kasar masar ya auro ta , zama yayi kusa da ita yana zolayan ta suna ta hira ,basu ankara ba sukaji ‘kara a waje ,a tare suka mik’e cikin firgici Jaseena ta rike Hameed ta ‘boye ta bayan shi jiki na rawa yayin da shi kuma ya zare takobin shi ya rik’e yana dube-dube don yaga ko waye zai shigo Kwatsam sukaji an banke k’ofa kamar daga sama mutanen suka yo kansu nan suka kaure da fad’a ,gashi mutanen fuskar su a rufe da kyar ya iya fisge mayafin d’aya daga cikin su ,abun da ya gani ya matuk’ar girgiza shi !!! Amintaccen shi na fada ne Zakar da wasu wanda ya tabbata fadawan shi ne ,da yaga sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi kaway ya figo Jaseena suka fita yayinda mutanen suka bi bayansu ganin Jaseena ta gaza yasa ya kwantar ta bayan wani k’aton tukunya yace yana zuwa ,cikin sand’a yake tafiya har ya isa gurin da dawakai suke ,fito kawai yayi wani kyakkyawan ingarma ya nufoshi fari ne fes ,ya shafa kan Dokin sannan ya haura shima ya nufi inda ya bar Jaseena,ya sameta yanda ya barta cikin ciwon na’kuda ,take ya umarci dokin da ya kwanta ,hakan yayi ma Jaseena daidai yanda zata samu sauk’in daidaitawa a saman dokin ,kafin su ankara sukaji harbi kibiyar ta chaki Jaseena ta gefen ciki ganin sun kusa far musu yasa ya fita a d’ari da dokin suma suka hau dawakai suka bi bayan su har suka samu suka shiga Wannan kogon dutsen……..

                    JASEENA.
        Hameed ya d’auki gawar Jaseena ya fito bakin kogon ya tsaya , kasantuwar bai taho da komai ba daga shi sai takobin shi haka ya dinga tono da Wannan takobi har rana ta fito yayi gumi ba na wasa ba hannuwan sa duk sun salube sun ya’yyanke har saida ya gama tono ya sallace ce sannan ya binne ya d’au takobin ya koma cikin kogon ya zauna ya k’urawa jaririyar ido ,tsananin tausayin ta ya kama shi kasantuwar ta zo duniya ne lokacin da uwarta take gangaren barin duniya ,gashi shi bashi da abincin da zai ciyar da ita gata kuma abar tausayi kasancewar ta bak’uwa a duniya ,ya d’aga hannayen sa biyu yace ” ya Allah ga baiwar ka ta zo duniya lokacin da zalunci ya mamaye al’umma Kowa burinshi yaga shine a gaba ,Allah na rok’eka ka raya ta kan tafarki madaidaiciya kuma ka bata ikon kare hak’k’kin duk wani wanda aka zalunta a gaban idon ta ,ya Allah ka kareta da ikon kariyar ka!!!
  
  Kukan Jaseena(sunan mahaifiyar ta ya maida mata) ne ya katse shi  ya je da sauri ya dauketa ya rasa ta inda zai fara domin kuka take na fitar hankali ,kamar ance d’aga kanka sama kawai ya hango wani haske ya hasko cikin kogon kuma ba daga asalin k’ofar da ya shiga ba ne, ya mik’e ya nufi gurin dokin shi ma ya bishi kasantuwar kogon makeken gaske ne …..,
     Abunda idon shi ya gane mishi yasa ya zaro idanuwa ya d’aga hannu yana godiya ga Allah .,

JASEENA Where stories live. Discover now