Kutsawa tayi cikin taron mutanen da k’arfin hali ta samu ta shige inda matar take ta d’aga ta tana yi mata Sannu yayinda sauran mutanen suka watse daga gurin Kowa ya fara tattare 6arnar da akayi masa amma da ka gansu kasan a tsorace suke duk da Jaseena ta fuskanci hakan bai sa ta ko girgiza ba ta d’aura matar kan dokin ta sannan ta ja akalar dokin suna tafiya matar na mata kwatance har ta kaita gidan ta, ta kuma taimaka mata har cikin gida ,wanda ba girma gareshi ba amma sai tsafta ,wani gadon kara ne gefe guda ta hango ta ja matar har gurin ta zaunar da ita sannan ta tashi ta nufi d’ayan 6angaren gidan don nema wa matar ruwa, akayi sa’a ta samu ta d’ebo mata….
Bayan ta tabbatar matar ta samu nutsuwa sai ta tashi zata fice ,hannun ta matar ta rik’e ta ce ” nagode baiwar Allah !! Amma yaya sunan ki ? Ta juyo da murmushi tace ” “Jaseena ” matar ta d’an jinjina kai ta ce ” amma ke bakya tsoro labari yaje kunnen Yerima Rizwan cewa kin taimaka wa wanda ya wulak’anta? Zai ce kin raina mar hankali ,sannan ya sa a miki horo mai tsanani ,kuma gashi ke yarinya ce bai kamata kina k’arama ki jefa kanki cikin had’ari ba !!! Murmushi kawai Jaseena ta sake yi tace ” Kar ki damu umma !! Ni ma ba kanwar lasa bace !!!in yana ji da sarauta nima ina ji da ita !! ke dai ki kula da kanki kuma ki daina fita ke kad’ai domin hakan ba k’aramin had’ari bane” tana kai Wannan ta juya ta fice gamida rufo k’ofar gidan ,matar ta bita da kallo ,a ranta tace ” yau naga mace mai kamar maza!! Yanzu har a masarautar Kalahari akwai macen da zata iya tsallake dokar Yerima ?? Ta girgiza kai ta koma ta kwanta.
kasuwar ta k’ara komawa ta gama saye-sayen da zatayi sannan ta juya ta bar garin , da la’asar ta isa kogon su ta shige ta nufi inda tasan kullum mahaifan ta yake motsa jiki da yamma ,wani d’an fili ne ya zagaye da itatuwa a nan ya ke koyawa Jaseena dabarun yak’i ,da gudu ta nufi inda yake ta zari wani sanda suka fara fad’a cikin raha har suka gaji suka bari.
wuta suka hura tana taya shi gasa kifi sai zuba take yi don duk abunda ya faru a Kalahari sai da ta zayyano masa shi dai bai ce ‘kala ba ya ci gaba da gasa kifin ,ganin ba sauraron maganar ta yake ba ta mik’e ta nufi wata duhuwa mai siriryar hanya ,gaba kad’an ruwa ne ke sauk’a ta saman dutse birin ta wanda take k’ira da suna Zainu yana nan kan kafad’ar ta yayinda take Kutsawa cikin duhuwar kukan damisa ta jiyo hakan ya sa ta wata Yar siriryar dariya ta kama wata reshe kamar biri tana lek’o inda taji kukan ,domin takan ji kukan ne tun tana Yar yarinya amma bata tab’a yin gaba da Wannan gurin ba kasantuwar daga Wannan dutsen mai ruwa babu wani guri a gaba balle ta ce ko daga chan ta jiyo k’ara. yau de ba Jaseena bace zata fita ,mahaifin ta Hameed ne zai fita duk da ranta bai so ba amma tasan bata isa hana shi fitan ba ,kamar kullum ya debi ganyeyaki a jaka ya ja Zabil suka fice …..tana cikin wasa da zainu su kama Wannan reshen su saki wancan Kwatsam ta sake jin Wannan kuka na damisa ,ai kuwa nan ta k’udiri niyyar sai ta gano duk inda Wannan ‘kara ke fitowa !!! Diro wa tayi daga saman bishiyan tabi hanyar da ta jiyo karan kamar kullum de bakin dutse take riskar kanta amma yau tace bazata juya ba sai taga menene a bayan ruwan da yake zuba kuma zata nemo inda Wannan damisa take
; Hawa tayi kan dutsen duk ruwa yana ta jik’a ta a hankali ta mika k’afan ta gaba taji dai ya zauna ai kuwa sai ta kutsa kai ,zainu kuwa tun da yaga ta shiga ruwa ya koma gefe yana kallon ta itama bata biya ta kanshi ba tai shigewarta………….
Wata Yar siriryar hanya ce a ciki sai duhun tsiya amma don rigima ta shige sai tafiya take ,har tayi tsakiya ta juya tana kallon hanyar da ta baro ,sai kuma ta tabe baki ta ci gaba da lulawa……………
YOU ARE READING
JASEENA
AdventureIts a war for pride! A story of royalty and love! Jaseena a valiant girl whos love for adventure unfolds the truth behind her identity, a truth which changes her life from herb trader to a great warrior and queen