“Dama kana magana ne?” Shine tambayar da ta fara fita daga bakin Jaseena. Haidar yayi wata Kyakkyawar dariya yace ,ina magana amma banda iyayena babu wani mahalukin da yasan hakan ko sarki Hasheem da kika gani bai sani ba ,duk da shine silar dawowa ta hakan !! Duk Wannan maganganu da yake yi babu abunda Jaseena ta fahimta duk ya dagula mata tunani , Ta mik’e tace in na fahimce ka ,kana so ka ce min kai ba d’an Wannan sarkin bane ? Kuma akwai abunda kake 6oye masa a matsayin sa na wanda ya yi rainon ka?
Wata dariya ya saki mai ban mamaki yace ” Jaseena duniyar tamu zagaye take da azzalumai masu bak’ak’en zuciya da son abun duniya !! Zan baki labari na da kuma dalilin da yasa na zama haka ,amma kafin na baki labari ina so ki min alk’awari babu wanda zai san ina magana a cikin masarautar nan ko da wasa ne! ” Jaseena ta furzar da iska daga bakinta tace ” inshaa Allah bazan bari Kowa ya san da Wannan zancen ba !! Sirrin ka zan killace shi kuma na bashi mazauni na musamman a zuciya ta !!” Murmushi yayi yace na gode !! Amma yanzu muje in nuna miki gari ,gobe zan sanar da ke tarihi na in Allah ya yarda ” Jaseena ta d’an 6ata rai tace” me yasa bazaka fad’a min yau ba? ” murmushi kawai yayi yace ” muje ” ya tashi ya mik’e ita ma tabi bayan shi har ta sa k’afa zata tafi sai tace ” kai ka je !! Ni zan gyara riga na, ba tare da ya tanka ba yayi tafiyarshi ita kuma ta juya rigan ta gyara tsaf sannan ta fito daga duhuwar da take …
Tsaye ta same shi a gefen Wannan bishiyar yana jiranta ” na gama mu tafi” shine maganar da ta ratsa kunnen sa ,ya juyo ya k’ura mata ido kamar ya had’iye yace ” muje” ya fara tafiya ta bi bayanshi sai fama da doguwar rigar takeyi duk ta mata nauyi ta tattare rigar har guwiwa hakan yasa ta bata sauri sai ta d’an ruga ma take iske Haidar duk da ya ga yadda take fama da rigar wanda hakan ya bashi dariya matuk’a amma ya kafse kamar bai san ma tana yi ba .
⚜kasuwar garin ya fara kai ta ,sai kalle kalle take yi ,Kwatsam ya bi da ita layin sayar da tsuntsaye ,su Jaseena an samu abun yi ,nan ta dinga bin keji keji tana ta dariya kamar pagal (mahaukaciya) shi dai haka yake a tsare sai tafiyar shi yake in taga yayi nisa sai ta sa gudu ta taro shi ,ga shegen surutu kamar aku ta sha gaban shi yana tafiya ita kuma tana tafiya da baya baya ,” kai nace ka d’an tsaya mana sai sauri kake yi ko baka ji na ne!! ? A garin ja da baya ta banke wata budurwa ta d’ebo kwai a kwando ta fad’i k’asa kwayayen suka fashe ,a gurin ta daskare ta kasa magana ,budurwar ta mik’e tana karkad’e jikinta yayinda Jaseena ta sunkuya tana kwashe mata wayanda basu fashe ba sai hak’uri take bata. Murmushi yarinyar tayi tace ” babu komai !! Ba kece wadda muka gani dazu zamuje deban ruwa ba?” Jaseena ta d’an d’aga kai alamar tunani tace “ ” Eh nice !! Ina sauran guda biyun suke?” Yarinyar tayi murmushi tace suna can gida ni sunana Jauda , ke kuma fa?” Ni kuma Jaseena! Shine amsan da Jaseena ta bata .
Ta juya sai dube dube take yi bata ga Haidar ba murya can k’asa tace “toh shi Wannan ina ya tafi ne?!” Murmushi Jauda tayi tace ” tun yaushe ya tafi!! Kizo mana mu tafi tare zamu nuna miki cikin gari ni da yan uwa na !” Da ‘kyar Jaseena ta yarda ta bi ta suka tafi………….
YOU ARE READING
JASEENA
AdventureIts a war for pride! A story of royalty and love! Jaseena a valiant girl whos love for adventure unfolds the truth behind her identity, a truth which changes her life from herb trader to a great warrior and queen