chapter 4

946 61 3
                                    

RASHIN SANI!

KHAIRAT UP

04

Mih , daga nan office din su ta nufa dama tana studying wani case ne. wayar ta da ke adabarta ta dauka ta duba number da kyau ta buga tsaki ta ce a fili lust man.

   sanda wayar ta kuma kara kin dauka tayi kusan sau hudu daga karshe ta kuma buga wani tsakin had'e da dauka da niyan kashe wayar saidai ganin kawar ta ce ke kira yasa ta dauka ta ce

Hello,ya akay kawata?

barr ina bukatar ganin ki dan Allah!

why? oh ina nufin ba yanzu muka rabu ba?

eh nasani ay dama ba yau nake nufi ba.

ok yanzu dai ina aiki a off kuma gobe ina da case ne so gaskiya haduwan mu is not possible a cikin week din nan.

to next week ya miki?

eh Allah ya kaimu

ameen.

glass dinta ta maida idan ta wanda ya bayanar da kyan fuskarta ta dauko wani sungumemen littafi ta na dubawa.

   bugun kofar da ake ne ya sa ta fitowa daga daki da sauri ta na magana waye ne ze 'balla mun kofa ina zuwa mana.

   budewan da zata yi ta yi tozali da fuskan wanda bata yi tsamani ba juyawa tayi kawai ba tare da ta damu da ta ce a shigo ba.

kai ya gyada ya bita cikin falan dama yasan za a rina amma ya wayance da ke gogagen namiji ne  ya ce da ita.

haba Mih why are u complicating things?

a hasale ta juyo ta ce masa oh nice ma me laifie?

to ai naga na miki laifi kuma na ce am sorry ya kamata ki hakura mu sake sabon rayuwa kin san ind san ki da yawa juya mun baya da zaki yi shi ne ze sa na koma ...

kaga malam saurara mun bani da lokacin maganganun ka mara sa tushe da amfani ka koma mana me nawa a ciki ta nuna sa da dan yatsan ta tace mr.abdul ka rike a ranka Allah baze barka ba cin amanar aure na da kayi, ka ha'ince ni ka yaudare ni ka kuma cuce ni ban san iya lokacin da ka dauka kana kwana da matan banza ba a waje i dispite u abdul tir da halayen ka na kyama nayi dana sanin auran ka dube ka mutum har mutum ashe fasiki ne .

mih, i said am sorry me a ciki dan na kwana da wata bayan ke? is nrml zamani ya canja

hannayen ta , tafa ta ce gud abdul ai na manta kai din dan zamani ne kuma mara kunya wato tutiya kake da halin bunsurancin ka? da ace yau ni ce ka kama da laifin kwana da wani ya za ayi ai nasan saki na zaka yi ka tozarta ni a idan duniya.

hannu ya daga ze mare ta

da sauri ta ce kul da kenan wallahi kada ka soma taba ni da kazamin hannun ka a kai gaba in kana dukan karuwan ka to ni basu bace ni matar ka ce kar ta san kar kasan ni na san ka bana tsoran ka ko kadan , insha Allah sai kaga ishara da hisabi tun a duniya ba sai a lahira ba.

takaici ma hanasa magana yayi ya juya ya fita a fusace.

nan ta zauna kan kujera ta saki kuka na takaici wai tsabar lalacewar duniya alfahari da aykata zina ne wallahi Allah sai ya saka mun da gaggawa.

duk ranan dana gano wadda take tare da kai sai na hukunta ta.

***           ***           ***          ***

duk yadda taso ya dau wayan ta ki yayi ta kira sa yafi a kirga amma yaki daga wayar ta.
karshe ma a blacklist ya saka ta

ta jefa wayan kan kujera ta na kyarma ni abdul ze ma haka? ni ze ki daga ma waya? ni ze sa a blacklist? to wallahi ahir din ka sai na koya ma hankali. sai na tona maka asiri a idan duniya, ta kunna taba hannun ta na rawa idanuwan ta duk sun yi luhu luhu dan zubda hawaye ga idanun sun canja launi zuwa ja jawur dan kayan mayen da take sha. ta gama kudurta a ranta cewa seta tona masa asiri zata fadawa mih abunda yake tsakanin ta da mijinta in ta rasa abdul kowa ma ya rasa shi in be zama nata ba to be isa ya zama na kowa ba bata san cewa tana mugun san abdul ba sai a wannan lokacin da ya juya mata baya ya kuma tabbatar ma a da cewa ya daina abunda yake mih yakeso ihu ta fasa hade da jifa da kwalbar benelin dake gefan ta.
ya abun yake?

     wannan kennan

RASHIN SANI!!!Where stories live. Discover now