Sanda na fara bibiyar ki kika ki bani fuska nikuma na nace miki dan har ga Allah ina mugun kaunar ki da son ki da zuciya daya irin love at first sight din nan na ke miki wanda nasan Allah ne ya dora min.
Da kyar kika fara kula ni har na fara koya miki so na da kauna ta muka shaqu muka saba da juna har manya suka shiga maganar munyi shekara daya muna dating juna kamin aka yi bikin mu.
Se ranan bikin maryam tasa waye zaki aura.
Ta shiga tashin hankali da damuwa ta so tona mun asiri na mata dadin baki na lallaba ta dake nasan halin kayata, har alkawari na mata cewa zan aure ta daga baya.
Ana haka nasan ainihin kishin ki akan kishi babu abunda bazaki iya ba tun sanda kika ma wata yarinya duka a mall da muka je shopping tare saboda kin gan mu muna magana to tun a nan na saduda nasan cewa maryam cab never be my wife sedai mistress dita.
Kalmar ta bakanta ran mih wato mistress duk da cewa ita ta jawa kanta amma ai maryam shaqiaiyarta ce.
Ganin ina raina mata hankali ina amfanuwa da ita muks fara samun matsala wanda ishaq ke sasanta mu duk dan bana san kisan meya ke faruwa.
Nida maryam mun tsorata lokacin da kika lura cewa ina hulda da wata a waje har kika kai mata kukan ki kika nuna mata cewa idan kika gane wadda ta miki shige a auran ki to fa zaki kasheta ne.
Sai....... Se yayi shiru
Se me tace dashi s hasale da kyamata?
Sai ta kira ni naki dauka karshe ta mun text.
IDAN KANA SON ASIRIN KA YA RUFU KA DAUKI WAYATA INA DA SHEDU MASU GAMSARWA DA ZAN NUNAWA MIHJANA A KAN DANGANTAKAR MU NI DA KAI NA YARDA DUK MU RASA KA NI DA ITA.
Sakon nan ya daga mun hankali dan i cnt afford loosing you.
Harara t watsa masa tamkar ta tsinka masa mari haka take ji ta ja tsaki tsuuuut.
Na nemi ishaq na fada masa ya ban shawara na kira ta mu hada meeting muyi magsna nida ita ayi ta kawai ta kare.
Hmm!
Aiko na kirata muka gaisa ta fara mun sambato dake a bige take da kayanml maye.
Mesa ka daina sona?
Mesa ka auri aminiyata...?
Why did u betray me?Look maryam ina san mu hadu nida ke.
Ok a ina?
Inda muka saba haduwa!
Ta ce mun to ta yarda muka tsaida rana ds lokaci.
Kwatsam washe gari ta canja meeting point din zuwa badala hotel dake kan titin airport rd opp da airforce base.
Then?
Wallahi mih sanda naje she was already dead ban ankare ba na ji alamun mutane a kaina it was the police!.
Humm abdool an samu fingerprints dinka a jikin wukar da aka kashe maryam da ita.
An samu you were the last to call her!
An samu text message's, pictures, video's dinku a both wayoyin ku, taya zaka ce baka san magansn ba?
Wallahi mih bani na kasheta ba.
Abdool cool down zaka iya tunawa bayan kai da ita se wa ye yasan zku hadu a inda tace ku hadun?.
Ni ban fadawa kowa ba daga ni se ita muka sani.
Insp. Ya shigo madam time.
Oh nagode hakan ma se anjima
Zan dawo gobe dan jibi zamu court for hearing.
Daga nan tasa kai ta fice daga station din.
Insp.nagode ko zaka iya mun iso gun da aka yi kisan?
Eh to se an samu approval daga magistrate off.
Kar ka damu zan je yanzu
Ok se anjima munyi waya.
Ranan ta gama komai ta ce da insp su hadu a can da wajan karfe biyar na yamma.
***********************
GIDAN SU MIH!
A gajiye ta koma gida wanka kawai take bukatar tayi ta sha tea ta huta ta je hotel din.
Tun a falo ta ci karo da fuskokin en gidan nasu amma dake miskila ce kums ta shirya ma ko wanne kalubale seta basar tayi hanyar dakin ta.
Mihjana
Cak ta tsaya kasancewar me kiran sunan nata.Ta juyo a sahale na'am abbu
Zo nan
Ta karasa kusa da kujeran da yake ta tsuguna a gaban sa.
No no tashi ki zauna magana zamu yi.
Zama tayi ka kujera tana sauraron sa.
Me dalilin ki na shiga case din abdool_razak ?
Sabida bashi da sa hannu a kisan maryam.
Mih after all he did to you?
Abbu ina kare abdool a matsayin mara laifi ba wai ina kare shi dan yana mijina ba .
Ai maryam ya kamata ki nema ma justice ba shi ba
Abbu in ban manta ba kai ka mun nuni da zama me gaskiya, da rikon amana ka taba fada mun ita gaskiya bata karewa sedai karya ta kare ka yarda da ni zan ceci abdool ne a matsayin sa na wanda bashi da sa hannu a kisan kswata aminiyata maryam, zan kare shi a matsayin client dina bayan mun gana case din nan ze sake ni . abbu , ummi da maryam da abdool duk sun cuce ni sun yaudare ni bayan na yarda dasu amma ba komai hakan ba ze hana nayi aikina bisa gaskiya da amana ba.zan nemo Wanda ya kashe maryam kuma zan zamo silar shigar sa prison.
Abbu maryam da abdool sun dade tare tun suna makaranta ni na shiga tsakanin su ta nisa sannsn tace RASHIN SANI!! Ina ma da zata dawo da na datse alakata da abdool da nasan sun dade tare ko sun san juna da bn aure shi ba sedai kaddara ta riga fata ba komai hakan ma alhamdulilahi.
Tausayinta ya kama su abbun ya shafa kanta hade da cewa allah ya miki albarka mih, ya baki nasara a rayuwan ki.
Amin abbu ta fada tana murmushi ta fada dakin ta mukuli ta sa ta rufe take wani irin kuka yazo mata ta sake shi ta fada kan gado.
Why abdool , why maryam? Na yarda da ku amma kuka ha'ince ni mesa? Mena muku?.
Vote
Comment
Share.
YOU ARE READING
RASHIN SANI!!!
Short Storylabari ne a kan mata biyu wayanda suke soyayya da mutum daya. aminan juna ne, labari ne me tsantsar yaudara,fushi,butulci,amintaka,kisa ku biyo ni dan jin wannan gajeran labarin.