Wani irin kaduwa mihjana tayi a yadda take ji a ranta tamkar ta gudu ta bar kotun ko kuma ta kurma ihu sedai hakan be nuna a fuskarta ba ta dake ta cije lips dinta hade da jan wani gauron numfashi ta sauke shi ta furzar da iska ta kada kwayar idanunta ta gama nazartar komai ta kai mintuna biyar a haka kamin muryar barr.imran ya katse mata hasasshenta.
Ya me shari'a ya kamata barr tasan aikin ta kuma ta daina mana wass da hankali bata da wani sheda na cewa maryam na raye kuma dr.abdool shi ne makashinta ya me shari'a lokaci yayi da ya kamata kotu tayi watsi da duk wani hasashen karya na barr mihjana ta kwatowa wadda aka kashe yancin ta nagode.
Alkali yayi gyaran murya ya gyara glass din sa ya ce barr.mihjana ko kina da wani abun cewa? Na lura wannan kara tana cike da kalubale da dama da sarkakiya muna cikin RASHIN SANI na abunda ya faru ki warware mana da hujjoji masu karfi ko kuma mu zartar da hukuncin da ya dace.
Mihjana ta ce ya me shari'a ina sa hujja!
Kusan a kade mami da zulaihat suka kalli mihjana me dakiyar zuciya da kums jarumta taki saduda.
MIHJANA:-Ta maida kanta gun zulaihat ta gama nazartar ta, ki fadawa kotu dalilin da yasa dr.mukhtar ya kama ki?
Zulaihat:-saboda anti maryam ta umarce shi da yin hakan dan nayi kokarin tona masu asiri ita da shi suna soyayya.
Mihjana:-garin yaya suka kama ki?
Zulaihat:- ban san cewa sun gane nice nake musu barazana ba na tambayi makudan kudi a gun su ni a gani na nayi babban tarko na ashe ni suke ma kallon mara hankali.
Sun sa mana gun haduwa saidai da isata naji an doke ni da wani abu me nauyi a kaina a nan take na fadi na sume ban kuma sanin me a ciki ba seda na farfado na gan ni cikin wani daki me duhu,tun daga ranan suke azabtar dani ta hanyoyi da dama har se yau da wannan bawan ALLAH ya kubutar dani.Mihjana:-karya kike yi
Zulsihat:-ta waro idanuwan ta waje cike da tsoro.
Mihjana:- cike da jindadin samun nasara ta murmusa ta ce a ranta da alama gussing dins ze zo daidai bara na bida ita a haka har seta fada da bakin ta.
Zulaihat:-ban..ga.ne..me kike nufi ba!
Mihjana:-eh cewa nayi karya kike yi zulaihat.
Barr imran ya gama saduda dan kuwa mihjana tana da jarumta da wayo ya gane ta lauyoyi take san yiwa zulaihat.
Mihjana:- ya me shari'a ga yadda labarin yake , maryam kamar yadda muka sani suna soyayya da dr.abdool tun suna garin paris,maryam ta shiga depression saboda auran kawarta da saurayin ta yayi bayan ta yarda dashi se take ganin dr.mukhtar wanda yake bata shawara da kwantar mata da hankali sedai wata rana taje gidan dr.mukhtar inda ta gan shi da me aikin gidan su zulaihat suna mu'amala irin ta ma'aurata tare, a takaice dai gidan da en'mata kanana da manya a cikin sa shi kan sa besan da zuwan maryam ba ranan. Dr.mukhtar ya kasance yana dilancin yaran mata kasashe da gari gari yana yin kudi dasu (flesh business) suna saida jikin su.
Maryam ta shiga tashin hankali da ganin wannan abun seta bar gidan a sace da kudurin samun kawarta ta fada mata komai da kuma en'sanda sedai ta makaro ashe gun fita meenal ta ganta sedai ita bata ganta ba.
Ciki ta shiga ta rutsa dr.mukhtr da tambaya dr.taya ya aka yi Maryam tazo yau bayan kasan yau muna da business?
Maryam kuma ya tambayeta?
E ita fa yanzu naganta ta fita.
tabdi jan meenal banma san cewa ta zo ba amma indai haka ne zamu dau mataki nasan mezan yi kira wo num BIG BOSS!.
Suka sanarwa big boss damuwansu.
Nan dai suka yanke shswarar yadda zasu biyo mata.
Washe gari ya kira maryam yace ta samesa a hosp ya samo maganin damuwarta da kuma hanyar da zasu bi su sa abdool ya aureta.
Wajan fitowa ne mami ta tsaida ta ina zaki maryam?
Zan dan je unguwa ne mami bazan jima ba kimun addu's buri na ne ya kusan cika.
To sekin dawo
Amin.
Murnar samun abdool yasa ta manta da wannan maganar ta jiya.
Ya gama jan ta da hira tukuna sannan yace ds ita mun yi magana da abdool kuma ya yarda ze aure ki
Da murna ta ce masa nagode mukhtar na gode da wannan albishir din
Sedai kinsan se kin cigiba da karbar magani da allurai u still need them kuma ki tabata kin daina amfani da miyagun kwayoyin nan kin ji ko
Inshs Allah dama ai a rashin abdool nake shan su kuma yanzu na samu insha Allahu bazan kuma sha ba.
And ki dan saurara masa tukuna ki daina kiran sa ze kira ki da kan sa ki dinga dan ja masa aji akwai abunda nske yi daga karshe nasan ze kira ki mun yi maganganu dashi sossai.
Ta kuma murmusawa tace nagode kuma zan bi duk wata shawara da zaka bani na yarda da kai.
Nan ya mata allura guda biyu a hannu ya kuma bata wasu tablets ta sha ya kuma bata guzurin wasu tayi ta godiya ta tafi gida.
Ko da taje gida ishi take ji hakan yasa ta nufi kicin nan ta tarar da zulaihat a kicin take jiya ta fado mata ta watsa mata harara tace ke ba se kin bar gidan nan mtsw matsa min ta bude fridge ta dauko ruwa ta shs ta nufi dakin ta duk da tana jin ciwn kai ya adabeta.
Kwantswa tayi ta soma bacci tun daga ranan ta kasance a cikin maye kullum ashe wadanan magungunan na gushe hankali ne kullum se an yi mata shi tun bata farga ba harta farga gashi ta zama addict to them ba yadda zata yi cikij watanni biyu maryam ta soma zama tamkar mahaukaciya!.
Kowa seda ya girgixa ya tausaya wa maryam ta sha wuya kamin a kasheta.
Alkali yace taya zamu yarda da wannan bayanin, ?
Mihjana ta ce maryam ce da kanta ta sanar dani sedai ban ga sakon da wuri ba har seda ta bar duniysr nan gaba daya sannan na sani ya me shari'a maryam aminiyata ce tare muka taso tare aka haife mu iyayen mu ne kawai dabn komai nata sani a wayata ta turo mun ta email dina sedai ban samu gani ba seda ta bar duniya nan ta ciro copy din ta mikawa alkali ya duba ya ajiye ya ce to yanzu yaya aka yi suka kashets?
Mihjna ta ce ya me shari'a ga su nan su zasu fada mana cigaban labarin meya faru da maryam.
Dr.mukhtar da ya riga da ya saduda yasan no way out yace zsn fadi komai mihjana da gaske take sakon da maryam ta tura mata gaskiya ne kuma mu ne muka hada komai mune muks kuma kashe maryam muka dorawa abdool dan asirin mu ya rufu.
YOU ARE READING
RASHIN SANI!!!
Short Storylabari ne a kan mata biyu wayanda suke soyayya da mutum daya. aminan juna ne, labari ne me tsantsar yaudara,fushi,butulci,amintaka,kisa ku biyo ni dan jin wannan gajeran labarin.