chapter 10

683 51 4
                                    

Govt p:-shedata ta farko wadda ta ga lokacin da aka yi kisan hotel laundry staff tina obi kotu tana bukatar ki .

Tina obi:-ta yi rantsuwa zata fadi gaskiya kadai.

Govt p:-tina ko zaki fada mana ranar lahadi 10 ga watan mayu sheksra ta dubu biyu da sha biyar meya faru a dakin num hotel 321? .

Tina obi:-_ranan ni ke da duty a laundry, saboda haka duk wani bedsheet ni zan kai dskuna tare da abokan aikina, cikin sa'a kuma na nufi dakin 321 wanda tun a bakin kofa na fara jin hayaniya alamun ana fada da karfi ana fadar maganganu to da naji abu yayi tsamari ne na bude dakin daidai lokacin na ga wannan mutumin yana sa wuka a wuyan madam.

Govt p:-nagode kina iya komawa ki zauna, alkali ya kamata a duba maganan nan.ya juya ko lawyern wanda ake kara kina da tambaya?

Mihjana:-yes

Aka bata dama ta  fito ta kirawo Tina again.

Mihjana:-mrs.ko zaki iya fada min sheksrun ki nawa kina aiki da badala hotel?

Tina obi:-erm ma'am shekara na daya da wattani hudu

Mihjana:-ko zski fada ma kotu da ina kike aiki?

Tina obi:- uhm ina aiki da royal.

Mihjana:-mesa kika bar gun?

Tina obi:-erm saboda suna bani albashi kadan.

Mihjsna:-tana gyada kai tace ok, amma na samu labari an kore ki daga royal ne saboda sun gano kina musu sata a kitchen dep.

Tina obi:-ta kwalalo ido waje ni kuma sata no oh madam me no be thife.

Mihjana:-ta daure fuska ta juya ta dauko wata takarda ta mikawa alkali, wannan shedar hotels din da tina ke siki da an koteta ne saboda tans da halin bera,koda kuwa customers sun zo ta kan musu sata a dabsrance hakan yasa aka koreta da kyar ta samu aiki a badala sedai duba da record dinta suks kaita bangaren wanki saboda suna da labarin halinta.

Govt p:-ya mike objection mi lord wannan ba hurumin mu bane ba kotu tana magana ne akan kisa ba sata ba ko character din tina ba.

Alkali:-sustain,ya kamata ki maida kai.

Mihjana:-nagode, sedai wadannan tambayoyin se mun yi sannan zku gane me nake nufi.

Tina kina nufin a kan idan ki abdool ya sokawa maryam wuta?

Tina obi:- eh

Mihjana:-kuma kin ji maganganu a tsakanin su.

Tina obi:-_yes ma'am.

Mihjana:-kamar me?

Tina obi:-erm ....uhm..tana cewa ya kyale ta kada ya cutar da ita,tana san sa sakkayar da ze mata kennan, shi kuma ya ce ki gane mana maryam ina da mata ina santa pls kije ki aure,no baka isa ba nima se ka aure ne saboda ina san ka to zan fallasaka a gun matar taka.

Mihjana:-toh se kika shiga dakin?

Tina obi:-eh lokacin naji ihun ta

Mihjana:-tom , ihu kika ji? Ko kuma kin shiga ne kinga ya danneta ya soka mata wukar a wuya.?

Tina obi:-ta fara sosa keya

Mihjsna:-ina sauraron ki kina kallo ya soka mata wuka kika kass neman taimako a taimaki maryam ko kuwa ihu kadai kika ji daga waje?

Tina obi:-erm ina waje ne ,da naji ihu ne ya sa na bude dakin da mukuli na se nagan shi da wuka ita kuma cikin jini.

Mihjana:-point to be noted mi lord tina obi ihu taji da maganganu daga waje,bata ga kisan ba, bata ga lokacin da abdool ya kashe maryam ba ta dai ga hannun sa a kan wukar,kuma ko a maganganun su bata ji yace ze kashe ta ba.

Govt p :-ya yi wuki wuki da idanuwan sa yana mamakin kaifin basira da hikima irin ta mihjana.

Tina obi:-madam ni dai ku kyale ni bsn san komai ba iya gaskiya ta na fada muku ni ban ga yana kasheta ba oo na dai ji ihun ta.

Mihjana:-uhm ko kin tuna karfe nawa ne lokacin?

Tina obi:- uhm ban tuna sossea ba amma ina ga karfe hudu ne na yamma.

Mihjana:-ta juya ta dauko wata tskarda doguwa fara , ta mikawa alkali mi lord wannan takardar ta pm (post murtom) reports ne na maryam an kashe maryam tun karfe sha biyu (12) na rana,kuma abdool lefty ne kuma inda aka kashe maryam dama ne taya ya me Lefty ze iya aiming ta right side? Abdool ya je badala hotel karfe uku da minti hamsin da uku lokacij yayi sining to tayaya za a ce shi ne ya kasheta?

Govt p:-karyane mi Lord lawyern wanda ake kara tana so tyi wasa da hankalin kotu ne ta kare dr.bayqn ga gaskiya nan a bayyane na wanda yayi kisan, sannan a makamin kisan fingerprints din dr ne a jiki.

Mihjana ta katse shi:-govt p ban ce babu fingerprints dinsa ba sedai ya sa hannu ne dan ya zare mata wukar lokacin kuma tina ta shiga dakin shi yasa taga kaman shi ya kashe ta.

Aka soma musu alkali ya taka musu burki ya kuma daga kara zuwa 1st june,ya kuma basu umarni su kawo kwararrun shedu masu gamsarwa!.

Nan kowa ya watse ana ta jinjina basira ta mihjana da iya aikinta dan tana komai a nutse ne har wasu suna jinjina mata suna kuma ganin cewa da gaske ba abdool ne yyi kisan ba, wasu kuma na ganin wautar ta sabida ta na kare mijin da ya ha'inceta.

Tun kan taje gids aka turo mata sako da wata boyayyar number.

BRAVO MIHJANA GASKIYA KIN BURGE NI. SEDAI KI SANI NEXT TIME NI ZAN CI WASAN!

Bata maida abun serious ba ta buga tsaki ta shge gida abunta.

RASHIN SANI!!!Where stories live. Discover now