_*HABIBI DA'IMAN*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*Intelligent writer's association*_
_*Page 1~2*_
_*Bismillahir rahmanir rahim*_
Kwance take akan makeken bed d'insu tana bacci, daga d'ayan gefenta na dama, yarane kamarta y'ammata kuma kyawawa masu kama daita guda biyu, saikuma d'ayan gefenta ma wata yarinya ce wacca bata wuce sa'arta ba a kwance,.
Jiyo bugun k'ofar da'akeyi ne yasa suduka sukai saurin farkawa daga baccinda suke a razane kuma a kid'ime kuma a tsorace,.
D'aya daga cikinsu ce tace "ohh...!!! God momy, wai meyasa take mana haka ne dan Allah",.
Itakuwa a kid'ime tai saurin mik'ewa dasauri jikinta har kyarma yake saboda sanin ko wacece ke bugun k'ofar taje tabud'e k'ofar a tsorace,.
Wata matace nagani a tsaye taharde gabas da yamma, kudu da arewa, tasha kunu tasha mur tamkar bata tab'a sanin miye dry ba, sauran yaran suna ganinta suma suka sakko daga kan bed d'in cikin tsananin tsoro da fargaba,.
Itakuwa a tsorace tace "mom...momy dan....dan Allah kiyi hak'uri wallahi gajiyarda mukai jiyane yasa muka kasa tashi dawur....." kyakkyawan marinda ta sauke matane yahanata k'arisa maganar,.
Cikin zafin nama da d'agawar murya tareda zazzaro idanuwa da firfito dasu woje tace "zanci kutmar ubanki wallahi idan kika k'ara cewa tak awajen, shegiya wawoyar banza",.
Kallon sauran tai sannan tacigaba da fad'in "wato yarannan kun rainani ko dan ubanku watou dama banzo na tashekuba da babu lokacinda zaku tashi ko, to mekuke nufi ne da aikin gida, kuna nufin nice zanmaku shi bayan kunsan bawani wanda zai maku aikin sai ku, to wallahi bara kuji yau ba'inda zakuje harsai kun k'arisa aikin gidannan gaba d'aya, ina nufin hadda School",.
Tana gama fad'ar haka tajuya tafice fuu kamar zata tashi sama.
D'aya daga cikinsu ce tazo dasauri tarik'o hanunta cikin tsintsar tausayi tace,
"Sannu *HUDAYYA* dan Allah kiyi hak'uri kinji halin momy sai addu'ah kawai" wani irin murmushi HUDAYYA tai wanda yafi kuka ciwo tashare kwallanda suka zubomata tace,.
"Wallahi HAMIDA insha Allah sai Allah yasaka mana da cin zalinmu da momy keyi, nidai fatana Allah yatashi kafad'ar Ammin mu yakuma dawo da tinanin Abban mu da hankalinsa akanmu ko Allah zaisa mufita daga cikin wannan k'angin bautar damuke ciki",.
"Ameeeen"
Sauran yaran biyun dake bayansu sukace sannan d'ayar tace "ni wallahi Allah magaji da wannan bautar, haba wannan wace irin wohala ce, mu da gidan mahaifinmu amma munzama tamkar bayi",.
D'ayar ma cewa tai "wallahi nima nagaji kawai musami Abban mu mufad'amasa gsky amaido da y'an aikin nan sucigaba da aikinsu, amma ina zamu iya aikin wannan k'aton gidan",.
Itadai HUDAYYA shuru tai tana sauraronsu batareda tace uffan ba, hamida ce tace.
"kunga kutashi muyi sallah muyi brush muje mufara aikin nan" nan dai suduka suka tashi suna k'unk'uni sannan suka fara shirin yin sallah,.
Da d'addaya duka farayin alwala tareda yin brush sunayin sallah har suka gama, suna gyangyad'in rashin isasshen bacci suka fita daga bedroom d'insu suka nufi cikin gida,.
Kai tsaye bedroom d'in wacca suka kira da momy sukai, koda suka shiga tana kwance kan bed d'inta, cikin ladabi suka durk'usa sukamata barka da kwana,
Kamar bazata amsa ba kuma ta amsa tana zabga masu muguwar harara, ganin haka yasa suka tashi zasu fice,.
Dasauri tace "ke hamida zo nasakaki wani aiki" wacca takira da hamida taje gunta sukuma sauran suka fice abunsu.