HABIBI DA'IMAN....69-70

1.2K 125 10
                                    

_*HABIBI DA'IMAN 🌷*_

_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183_

_*Intelligent writer's association*_

   _*Page 69~70*_

_*Bismillahir rahmanir rahim*_

Ihunda taratsa ne yajanyo hankalin police d'inda ke cikin station d'in, Abban ta najin takurma ihu dasauri yamike a tsaye yazo kusa da'ita.

Arazane yake kallonta, y'an uwonta kowa Sam basu fahimci abunda yake faruwa ba, amma Abban ta kam tinda yaji takurma ihu yafahimci komai, hanu yad'ora aka tareda fashewa da kuka yana fad'in,

"Tabbas yau dubuna tacika ni haliru, nashiga uku, yau k'aik'ayi yakoma kan mai shek'a, wayyo Allah na nashiga uku ni haliru" jin abunda yake fad'a yasa su hamza sukayo gunsa suna tambayar abunda ke faruwa.

Bai iya cemasu komaiba, itakowa saudatu tini tafara cire kayan jikinta tana ihu tana koma sosan jikinta tamkar ciwon k'aik'ayi,
  ...................

Daddad'an iskan k'asarta ta haihuwa taja acikin hancinta tareda rufe dara daran idanuwonta tana murmushi "Alhmdllh ala kulli haalin" shine abunda tafurta sannan tafara sakkowa tana kallon yanayin garin.

Bayan sun sakko sannan suka zauna suka jira fitowar kayansu, bayan kayan sunfito sannan suka fito su uku mata kowaccensu sanye da jallabiya bak'a da rolling na veal shima baki, idan kagansu kaikace jinin shuwa'arab ne sbd tsabar kyansu da had'uwa bazama kace sun hayayyafa dayowa ba.

Koda suka iso gunda ake shiga taxi sai suka tadda driver's sunzo d'aukansu, tsohon driver d'inta tafara ganewa Ilyas, har k'asa yadurk'usa yagaishe da Ammi farida cikin girmamawa, itama cikin fara'a ta amsa sannan yagaisa dasu uncle Faruk, daganan suka fice izowa gida.

Tinda suka kamo hanya take kallon gari tana murmushi, komai an sauya abubuwa da dama sunsauya, anyi sababbin gine gine, har suka iso kofar gida idanuwonta basu dauke daga kallon woje ba.

Ahankali ta sakko kafarta tafito, tsaye tai tana kallon gidan, shima ansauyasa ssi, dan hatta gate ansauya bare kuma ginin.

Saida ma'aikata dasu Ilyas driver suka gama kwashe kaya suka shiga dasu ciki sannan sukuma suka kama hanyar shiga, suna shigowa compaund d'in gidan saigasu HUDAYYA sunzo dagudu su mama da ummi dasu Amira haddasu Affan suna bin bayansu cikin farinciki,

Koda acikin bacci sukaga mahaifiyar su zasu ganeta bare koma yanzu, aikwa dagudu sukaje suka rungumeta suna kukan farinciki, itama k'ankamesu tai ssi ajikinta nantake kwollah suka fara zuba daga idanuwonta, har d'aurin veal d'inta yakwonce jakarta kowa Saida momy firdausi ta amsar mata da phone dinta, dan ita tama manta dasu sbd tsabar farinciki,

Saida suka d'auki kusan 5mnts ahaka su sunkasa barinta itama koma takasa barinsu sai faman sharb'an hawaye suke, Abban sune ya'iso cikin murmushi yazo tagabansu yasanya hannayensa yad'ago HUDAYYA da hunayya yana shafa kansu.

Cikin zubda kwollah wonda yake had'e da dariyan farinciki tafara magana "masha Allah, yarana sun girma, ashe zansake sakaku acikin idona, bantab'a tinanin zanyi tsawon rayuworda zamu sake ganin junaba, nad'auka ciwon tafiya zaiyi dani, ashe bahaka bane" tak'arisa tana zubda kwollah masu zafi,

Dasauri Abba yasaka hanunsa yashare kwollan yana fad'in "kyakkyawor fuska wocca take d'auke da annuri akoda yaushe, hawaye basu dace da'ita ba, Sam baidace aga kwollah nazuba akanta ba" murmushi tai tasaka hanunta tashare kwollan.

Cikin murmushi HUDAYYA tace "yau tsawon shekara goma sha biyu kenan rabon mu damu sanyaki acikin idanuwonmu, munyi maraicinda ko wonda bashida uwa bashida uba kuma bashida gata baiyisaba, munsha wuya iya wuya, rashinki agaremu yazamo tamkar mutum yarasa gangar jikinsa ne gaba d'aya, tin muna y'an k'ananun mu mukasan miye wohalar rayuwa musamman ni danake karama acikinmu dan humaira kam batada damuwa, momy saudat tamana rikonda bawoni mahaluki dazaiso yayiwa woni d'an uwonsa irinsa, wollahi badanda darajan su hamida ba dasainace Allah yamat...." dasauri Ammi tatoshe mata baki tareda juyamata kai alamar a,a karta furta.

HABIBI DA'IMAN Where stories live. Discover now