_*HABIBI DA'IMAN 🌷*_
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*Intelligent writer's association*_
_*Page 65~66*_
_*Bismillahir rahmanir rahim*_
Rarrashinsa Mami tashigayi cikin tsintsar tausayin halinda ya tsinci kansa aciki,
Kuka yake sosai yana fad'in "HUDAYYA ta ina kikaje ne kika barni, haba dan Allah kidawo gareni, wlh bazan tab'a iya rayuwa babu ke ba, zuciyata bazata taba iya rayuwa dawota ba, wayyo Allah ka kawo mana d'auki".
Janyosa Mami tai tarungume tana rarrashinsa itama tana zubda kwollah.
...................Around 8am dot jirginsu papie yad'aga isowa k'asar kebbi domin karb'an auren Hamida wa HINASH, wonda mahaifinsu yabasa.
Sai kusan 1pm sannan suka iso k'asar kebbi, Koda suka iso tini driver's sunzo d'aukansu donhaka Kai tsaye suka fice izowa gidansu dake gesse phess 1, Saida sukaci abinci sukai sallahr la'asar suka huta sannan suka shirya izowa gidansu HUDAYYA dake gesse phess 2.
Kamar kullum cikin karamci da mutunci da haba haba aka taryesu, abun mamaki dik y'an uwan momy saudat maza da mata bawonda baizo gidanba kusanma sune suka taryi su papie, abunda yafi bashi mamaki kenan, su abbu sunzama y'an kallo tamkar basune woenda za'anemi auren a gunsu ba.
Side d'in momy saudat aka woce dasu Kai tsaye inda aka saukesu a babban parlon Abban du HUDAYYA wonda yasha k'awa da gyara irin na alfarma,
Nan dai suka zauna suka gaggaisa sannan aka fara shigowa da abinci kala kala kaikace woni bikine akeyi, abunma harya fara bama su papie takaici sbd abun nasu ysi yowa ssi.
Ko 3mnts basufi da zama ba saiga momy saudat tafito jikinta bako mayafi bare hijab, tai d'aurin d'ankwali tamkar tsohuwar karuwa tana taunar cwingom tana fari da ido tashigo tana dariya tashiga gaidasu papie, shidai papie abun yamafi k'arfin tinaninsa.
Abba Barrister kanensa kowa ko kallon arziki baimata ba sauran y'an uwonsu ne dasukazo dasu ne sukadan saki fuska suka gaisa, su Abbu kowa sunzama y'an kallo sun rakub'e gu daya suna kallon ikon ubangiji.
Y'an uwan momy saudat maza su hud'u ne suka shigo yanzu tareda Abban su HUDAYYA cikin shiga ta alfarma idan kagansu kaikace wosu hamshak'an y'an kasuwa ne ko ma'aikatan gomnati, bayan koma ko tsinke kitso basa siyarwa dik aikin momy saudat ne woi don kar su papie su rainasu suce y'an uwonta talakawa ne, shine tamasu wonnan shirin.
Bayan sun iso nan suka gaisa sannan suka zauna, Abba ne yafara magana kamar haka "to Alhmdllh, bak'inmu sannunku da zowa, muna maku barka da isowa lafiya" suka amsa sannan yacigaba,
"To abunda yataramu anan shine, inaso ne kusani cewa, nabada auren yata Hamida wa HINASH domin tamaye gurbin y'ar uworta data b'ata tsawon lokaci Mai nisa shekara tara, woi shekara hud'u, au shekara shida" kallon kallo aka shigayi tsakanin su papie dasu abbu dakuma su jibrin y'an uwan momy saudat".
Can ganin alamar kamar bamaya cikin hayyacinsa yasa dasauri hamza, d'aya daga cikin y'an uwan momy saudat yai saurin karbar zancen yana Yar dariya yace "amm...am....to yanzu dai ayi batun abunda yahad'amu".
Jibrin yacigaba da fad'in "bamasan auren nan yawuce yau, sbd mu bamazauna nan bane, ni gobe gobema zanfice nabar k'asar nan, so inaso ayi auren ina nan" hamza yacigaba "gsky nima nazanfi kwana daya a k'asar ba zankoma".
Abban su HUDAYYA yacigaba "nayanka sadakin yata Hamida Naira dubu dari da hamsin" saiya juyo yakalli su abbu sannan yace "kuzama shaidu, nabama HINASH auren yata Hamida akan sadaki naira dubu dari da hamsin domin tamaye gurbin y'ar uworta HUDAYYA" su abbu kam basu iyacemasa komaiba kawoi suka d'aga masa Kai alamar sunji,