_*HABIBI DA'IMAN*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_wattpad@Aufana8183__*Intelligent writer's association*_
_*Page 31~32*_
_*Bismillahir rahmanir rahim*_
Dazuwonsu aka fara masu lalle, humaida aka faramawa sannan HUDAYYA.
Bayan angama mata aka faramawa munawara, ana cikin yiwa munawara saiga kiran HINASH yashigo woyar HUDAYYA.
Woyar na ahanun hunayya tana game, danhaka tai picking call d'in sannan tak'arawa HUDAYYA a kunne tareda fad'in "ya HINASH ne yakira, kiyi magana".
Ahankali cikin zazzak'ar muryanta tattausa kamar kanari tarangad'a masa sallama, zaune yake akan k'ayataccen bed d'insa amma saida yad'an kwontarda bayansa kan bed d'in sbd yanda taushin muryan tata yaratsa dodon kunnensa,
Saida yad'auki y'an wosu saconni sannan yafurta "I really need u in palace baby, ina cikin woni mawuyacin hali HUDAYYA dan Allah kizo ki taimakeni karna illata, kokuma kifad'awa su mami a d'aura mana aure tin yau please my habibty".
Tinda yafara magana takasa fahimtar inda zancen nasa yadosa, hakama yanzu yak'ara rud'arda ita sbd sam bata fahimci abonda yake nufi ba,
Cikin tattausar murya tace "ban....banfahimci abunda kake nufiba, kuma kayi hkr ina cikin mutane anman lalle ne, kasake kirana zowa anjima" daga haka tad'auke kunnenta tareda cewa hunayya,
"Kashe woyar".
Ba musu kowa hunayya takashe woyar.Jin abonda tafad'a yasa ransa yab'aci ya harzuk'a, tafasarda zuciyarsa kemasa ta karu gakuma woni azababben sha'awa dake damunsa hartakaiga maransa tafara d'aure masa,
Kwonciya yai tareda k'udundunewa a zuciyarsa yana fad'in "lallaima yarinyar nan, taraina sosai, bankumasan yaushe ne raini yashiga tsakanina da'ita ba, but i will teach her a very gud lesson, very soon, zata gane kurenta ne idan tashigo hanuna" yai kwafa sannan yasake juyawa d'ayan b'angaren hanunsa dafe da maransa.
********
Around 7:30pm komai angamawa amare wonda yadanganci make-up da shiri da dai sauransu, amare biyar kyawawa jikokin Alhj mo'allayid'i jinin fulani tsatson fulanin daji, humaida,HUDAYYA, Amira dakuma munawara.
8pm dot motoci suka d'aukesu izuwa gunda zaa gudanarda kamun.
Koda suka isa kowa mutane dik sun iso holl d'in yacika sosai da mutane, kayansu iri d'aya ne suka saka, material ne maroon color d'inkin yoruba riga da zane da ashoke na yafawa da d'an kwali wonda ake rolling dashi, sunsha make sosai wonda aunty meenah beauty tamasu, takalmansu da y'ar jakarsu dik silver color ne abun gwanin birgewa.
Sunyu kyau matuka gakuma lallensu ja da bak'i sai shining yake abonka da fararen fata sai suka zama taurari sai haskawa suke,
Tinda suka shigo akafara feshesu da tiraruka masu dadin k'amshin har suka isa gunda aka tanadar domin su, daganan kuma akacigaba da gudanarda kamun.
Angwaye dika bawonda yaje kamar wo'enda sukai hadin baki, kome yahanu zowa oho,
Bayan angama komai sannan akafara d'aukan hotuna da camera's da wayoyin hanu.
Sai kusan 12am sannan aka gama kamun kowa ya watse, aunty billy itace ta d'auki amare a motarta tamaidasu gida.
HUDAYYA dama tagaji ssi suna isowa tacire kayanta, sallar isha kawai tai tabi lafiyan gado.
Hakama su humaida sungaji ssi amma sukam saida sukai wonka sukai sallah suka saka kayan baccinsu sannan suka kwonta, asuba tagari.
Tana cikin bacci saitafara mafarkin Amminsu, woi gasunan ita da y'an uwonta sunje dubiyarta Egypt, koda sukaje saisuka tadda ashe woi tarasu tin shekara shida dasuka woce, kuka suka fashe dashi ita dasu humaida tana fad'in,