6

927 83 5
                                    

Kwana biyu kenan da faruwan mummunar abinda ya auku akan Hindu, gaba-daya ta canza bata magana, bata tashi daga inda take, abinci ma se anyi da gaske take ci, a takaice ma dai dura ake mata.

Osama kuwa be kara zuwa inda take ba tin daga ranar, idan ya tashi da safe ya fita baya dawowa se goma na dare, yana dawowa kuma ze kwanta koh lekata bayayi.

Wannan abin sosai ya canza rayuwar mutanen gidan ba kaman Hindu, Osama da Shaukiyya wacce tafi kowa sanin ciwon 'ƴarta, ganin haka ne yasa Hajiya Hindu cewa zata dauki Hindu su koma Kogi a canza mata makaranta a chan kila ta dan sake amma Hindu tace ba inda zata, ba yanda ba'ayi da ita ba taki tafiya.

Ganin iyayenta na shiga damuwa yasa ta fara sakewa tana fitowa amma abinda ke matukar bata mamaki shine rashin ganin Osama, tayi tunanin ya koma makaranta ne shiyasa bata wani damu sosai.

BAYAN SHEKARA DAYA

Gabadayansu sun dangana sun maida komai ba komai ba sunci gaba da rayuwarsu kaman ba wani abu daya taɓa faruwa. A halin yanzu Hindu nada shekaru goma sha biyar, sosai ta zama budurwa dan har an fara samun masu zuwa cewa suna sonta. Ganin haka yasa su Hussain tsaida ranar aurenta da Osama saboda kar asamu wanda ze hure mata kai idan sukace sun mata miji taki amince ba tareda sun sanar da yaran cewar an musu baiko ba.

A ranar da Osama ya dawo daga school aka zaunar dasu gaba-dayansu Hussain yayi gyaran murya tareda cewa "Osama kai ɗana ne, nasan kanada masaniyar cewa bazan taɓa cutar da kai ba, Hindu kanwarka ce, mun dade da muku baiko tsakaninku, saboda haka yau nake maka albishir da cewar nan da wata daya me zuwa zamu aura maka Hindu a matsayin matarka duk da musan cewar bawai ka kai ka rike mata bane".

Osama ji yayi kaman ya dora hannu a kai ya fasa ihu, tuni zufa ya wanke mishi fuska yasa handkerchief ya goge yana mamakin meyasa iyayensa suka masa haka, a rasa wacce za'a aura masa se Hindu, yarinyar da aka lalata mata rayuwa a gabanshi, da wani idon ze kalleta? wani irin rayuwar aure ze shimfida da ita bayan har yanzu ya kasa cire abinda ya faru ranar a kanshi, ba komai yasa yake guje mata ba sedan duk sanda ze ganta se ya tuna da wannan mummunar ranar, yanzu a haka akeso ya aure ta? Ina bazai yiwu ba.

Tunani kala kala yakeyi ya kasa dagowa ya kalli iyayenshi balle su san halin da yake ciki, ita kuwa Hindu rakuɓewa tayi jikin kujera hawaye na silala a kumatunta dan ta tabbata Osama ba sonta yakeyi ba, a rayuwa batada da burin da ya wuce tayi auren soyayya, ta auri wanda take so kuma yake sonta amma koda ace tanajin son Osama a zuciyarta ta tabbata shi baya sonta.

A2 ne yayi karfin halin cewa "Osama idan kaga banason Hindu zamu janye maganar mu", murmushin da yafi kuka ciwo Osama yayi a hankali yace "Abba na isa ince banason jinin ka, aiko bana sonta muddin kukace na aureta zan kokarta na koyawa zuciyata sonta, saboda haka Abba na amince da zabinku Allah yasa yakan shine mafi alkhairi", gabadayansu sunji dadin abinda yace, da murmushi kan fuskar ko wannensu Hussain yace "Masha Allah, haka akeso ɗa nagari ya kasance, Allah ya muku albarka gabadayanku", da ameen suka amsa sannan duk suka mike suka fita.

Tun daga ranar Ammi ta fara gyara 'yarta, dama ta dade tana gyarata ɗorawa tayi daga inda ta tsaya, Hindu ta zuba ido ta gani ko Osama ze zo su fuskanci juna amma har aka fara shirye shiryen biki dangin su suka fara zuwa batasa Osama a ido ba. Wannan kawai ya tabbatar mata da lallai Osama baya sonta.

UWA TA GARI (EDITING)Where stories live. Discover now