3

1K 81 3
                                    

Dada na ajiye waya ya shirya ya fita, be tsaya ko ina ba se Nnamdi Azikwe International Airport, direct counter yaje, yaci sa'a akwai jirgin da ze tashi zuwa kebbi, ticket ya siya ya koma yana zaman jira, cikin kankanin lokaci suka gama shiryawa jirgi ya tashi.

Basu dau lokaci me tsayi ba suka sauka daga airport yayi charter din taxi dan gani yake idan yace ze tsaya jiran driver dinshi ma bata lokaci ne.

A gaban hospital din aka ajiyeshi ya biya sannan ya shiga ciki, a reception ya tsaya yana tambayan dakin da aka kwantar da Jawahir, wata nurse ce ta mishi jagora har cikin dakin sannan ta fito dan ta kira mishi doctor.

Cike da tausayawa yake kallon Jawahir harya karasa gaban gadon inda take kwance an mata dauri a kafa da hannu daya sannan dayan hannun kuma ana mata karin ruwa ga goshinta ga katon plaster da alama dai ciwo taji a wurin.

Hannunta wanda aka ma dauri ya riko tareda shafa kanta da dayan hannunshi a hankali yace "what the hell happened to my princess?", ba me bashi amsa dan haka yaja kujera ya zauna ba tareda ya sake hannun nata ba yaci gaba da kallonta yana me nadamar barinta wurin Mamah da yayi da zai yi tafiya.

Mahaifin Sadiq ne ya shigo da sallama tareda karasawa kusa da Dada ya mika masa hannu tareda cewa "I'm Dr Kabir, u must be her father?", kada kai Dada yayi yace "yes", gyara tsayuwa Dr Kabir yayi sannan yace "Good, karka tada hankalinka dan ba wani babban matsala aka samu ba, karaya ta samu a hannun hagu da kafa, se kuma goshinta daya buge da dutse ta samu rauni".

Cike da mamaki Dada yace "dutse kuma, waishin ya akayi ta samu duka wannan raunikan?", kallonshi Dr Kabir yayi yace "da alama baka da labarin cewar ta fita hiking itada kawayenta da abokanta wanda tsautsayi yasa ta fado daga kan dutsen", da sauri Dada yace "subhanallahi, wannan wani irin kasada ne", dafa kafadarshi Dr Kabir yayi ganin Dada ya shiga tunani yace "mu godewa Allah da abin yazo da sauki bezo da karan kwana ba, nan da anjima kadan zata tashi, idan ta tashi ina consultation room 4", kada kai kawai Dada yayi dan beda bakin magana. A haka Dr Kabir ya fita yaja musu kofa.

Mamah hankali tashe ta karasa cikin hospital din itama tana tambayar dakin da Jawahir take, har gaban dakin aka kaita sannan nurse din ta juya, gabanta ne ke mummunan faduwa saboda ko ba'a gaya mata ba tasan Osama mahaifin Jawahir na ciki dan kuwa ta jiyo kamshin turarenshi.

Lumshe ido tayi sannan ta bude tana sauke ajiyar zuciya, handle din kofan ta kama ta bude sannan ta shiga da sallama, amsa mata sallaman yayi ba tareda ya dago ba har seda ta karaso gaban gadon, bata kai ga riko hannun Jawahir ba taji muryarshi na cewa "i regret leaving her under your care", cak Mamah ta tsaya tana kallonshi bakinta se motsi yake alamar tanaso tayi magana amma maganan yaki fitowa.

Dagowa yayi da idanunshi dasuka kada sukayi ja saboda bacin rai yace "meyasa idan Jawahir na wurinki ba'a sati take shiga matsala, meyasa bakya kula da ita yanda ya dace, for goodness sake she is your daughter as well as mine, kidena bari kiyayyar da kikemin na shafanta dan duk abinda ya faru a baya batada masaniya akanshi, keda kanki kika kaini kotu akan na karbe miki 'yarki batayi wayo ba akace na baki 'yarki harse ta shekara bakwai sannan se mu fara rabawa tana zuwa wurina sometimes kuma wurinki amma gabadaya kin kasa kula da Jawahir", shiru yayi daga masifan da yake yayinda Mamah ke tsaye guri daya banda hawaye ba abinda takeyi.

A haka yaci gaba da cewa "yanzu kalleta, just look at her, kalli yanda ta dawo kaman ba princess dina ba, she looks pale dan ba haka na tafi na barta ba, amma cikin kwana uku kalli yadda ta dawo", girgiza mai kawai Mamah keyi sannan a hankali tace "Allah ya baku hakuri kai da Jawahir ya huci zuciyarku, kuma inshallah daga rana irin ta yau baza'a kara samun matsala ba dan kuwa na yafema Jawahir har abada kayi duk abinda kaga dama da ita, nima yanzu zan samu kwanciyar hankali Allah ya kawomin wani mijin nayi aure, idan ta tashi kace mata ina mata sannu", tana fadar haka ta fice tana goge hawayen kan fuskarta.

UWA TA GARI (EDITING)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant