18

788 71 6
                                    

Sati daya kenan da Jarood ya daina daukan wayan Jawahir, inda ta shiga damuwa sosai duk saboda shi, har gidansu taje mahaifiyarshi tace itama kwana uku kenan bata sa shi a ido ba.

Farida a wata sabuwar duniya take, an samu abinda akeso dan kuwa a kullum Osama seya kira sau uku sau hudu duk dan yaji lafiyar jikinta, kuma duk kiran da zeyi be taba tambayar Jawahir ba kuma bawai yana kiran ita Jawahir din bane, yayin da Farida kanta bata ragawa Jawahir wurin sata aiki, shara, wanke wanke, wanki, guga da goge goge ba irin wanda Jawahir batayi, tin bata iyawa har tazo ta fara bada himma dan batason batawa Farida rai ko kadan, girki ne kawai Farida ta dauke mata nauyin shi, shima din dan tasa Jawahir dafa white rice ne ta cika gishiri tace karta kuma girki dan bata shirya mutuwa ba, wannan dalilin yasa Jawahir bata girki a gidan amma bayan wannan duk wani aikin cikin gida Farida sata takeyi, sedai ta zauna tana gyara farce, ko kallo, ko kuma karanta novel yayinda Jawahir ke kai kawo tana mata aiki.

********************


Mamah da Harun (Abba) fahimta da shakuwa ta musamman ce ke shiga tsakanin su, yana iya kokarinshi wurin ganin ya kyautata mata kaman yadda take kokarin ganin ta faranta mishi, har gida Sabreena ta biyo ta dan nuna mata farin cikinta na amincewa da Abbanta da Mamah tayi, yayin da Najib ya kaiwa mahaifiyarshi wato Yaya Aysha labari inda ta ziyarci Mamah take bata shawaran cewar karta wani ja lokaci in dai har ta amince da Harun tinda yanzu su ba yara bane, Mamah ta dauki shawarar hannu bibbiyu kuma ta shaidawa Yaya Aysha inshallah Allah zata sanar dashi amma Yaya Aysha tace su bari tukunna dan suma se sunyi bincike, bayan kwana biyu Yaya Aysha ta kirata take shaida mata cewar sunyi bincike kuma alhmdllh ba'a samu wani aibu tattare dashi ba dan haka idan sun shirya seya turo magabatan shi wurin mahaifin Yusuf (mijin Yaya Aysha, uba ga Najib kenan), kan maganar auren. Mamah tayi alkawarin sanar da Harun a cikin wannan satin. Wannan kenan.

********************


Yau weekend, tin safe Jawahir ta gama ayyukan ta dan haka tayi alkawarin komawa gidansu Jarood ko zata sameshi, seda tayi wanka ta shirya sannan ta nufi dakin Farida, a gaban dressing mirror ta ganta zaune tana kwaliyya da alama itama fita zatayi, cikin sanyin murya Jawahir tace "Aunty zan dan fita in dawo amma bazan dade ba", ba tareda Farida ta juyo ta kalleta ba tace "sekin dawo", juyawa tayi ta ficewarta daga gidan.

Ta dade tsaye bakin titi tana jiran daidaita, da kyar ta samu daya ta  fada mishi inda zata tareda kudurtawa ranta cewar idan Dada ya dawo zata fada mishi tana buƙatar mota, se a lokacin ta tuna tinda ya tafi sau daya sukayi waya which is so unlike him dan idan yayi tafiya akai akai yake kiranta amma wannan karon ba haka ba labari yasha banban.

Batasan sun karaso ba seda taji me adaidaita yana cewa "Hajiya mun iso", sannan ta dawo daga tunanin Dadanta data shiga, fitowa tayi ta biyashi kudinshi sannan ta juya zuwa gate din gidan ta fara kwankwasa wa, me gadin su ya bude mata kasancewar ya santa ya bata hanya ta wuce.

UWA TA GARI (EDITING)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin